FORTY 💕

5.2K 406 48
                                    

*WADATA*
_Forty 💕_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥Shatuuu095@wattpad




Hajiya ta numfasa gami da cewa

"Aisha, Allah ya saka maki alheri kin ji, hakika baiwa ce babba samun aboki na gari. Na roki Allah yayi muku albarka ya saka maku albarka cikin lamuran ku. Insha Allah Alhaji na dawowa ni zan masa wannan kyakkywan albishir din"

Husna ta kwabe fuska tana shirin kwalla tace

"Amma Hajiya baki ji ta baki na ba fa? Kuma daga gama takaba sati biyu kawai sai aji labarin nayi aure?"

Aunty Bushira tace

"Sai me? Ki rabu da harkar mutane kin ji? Yanzu kawai ki duba tsakanin ki da mahallicin ki kawai, sauran abubuwa ki watsar dasu. Indai shari'ah ta amince wa abu matsayin dai dai to kawai kiyi ba tare da sauraron mutane ba."

Mun bata baki amma shiru Hajiya tace na kyale ta kawai duk yadda ake ciki zata kira ni gobe nace to.
Tare da Auntyy Bushira muka fito daga unguwar Hausawa nan Bawo Road. Ita nan Hotoro take don haka muka tafi tare a hanya tana tayi min tambayoyi game da Rayyan wanda na sani na bata amsa.  A kwanar gidan ta na sauke ta naso shiga da ita amma taki tayi min godiya na wuce gida.
   Mama na samu dasu Yaya Sambo da murna ta nace

" Yaya Sambo, sannu da zuwa "

Yace

" Yauwa."

Guri na samu na zauna. Gaba daya ya sauya mijin Mama ya samo masa aiki can ministry dinsu ta man fetir yayi haske ya sake murjewa da gani hutu ya zauna masa. Amma ya wani hade rai yana fadin

" Uwar yawo.... Mama kin sangarta yarinyar nan duk inda taso taje kamar kar......"

Mama tace

"Ka karasa sai ka tashi gaba na"

Yace to. Dakin Umma ya nufa yana fadin

"Umma Amaryar Baba daga ke babu wata a zuciyar Malam Garba, yana buga rafta amma ke ce manne a zuciyar sa..."

Dariya kowa yayi haka yake in yaso tsokanar Mama. Mama nata kasafin auren Rukayya dame dame zaa bukata Yaya yace nima nayo nawa nace ni kam na yafe su ji da Rukky kawai.

Shirye shirye ake sosai daga ko wani bangare. Sulaiman nata gyara don so yake yayi gyaran gida amma ba wani mai tsada ba ya so ne ya kashe kudi sosai kuma transfer dinsa ta samu ya zama kamar yayi asarar kudinsa. Rahama dai kam shiru bata dawo ba, Inna ma kuma bata yi masa zancen ba don son ranta ace sun rabu ita gaba daya, wannan abu da ya faru ya koyarwa da rayuwata darasi ba kadan ba mussaman da ta dandadi dacin sakin 'ya. Su Kansu sauran yaran kowa ya nutsu kada ma Zinatu taji labari don ita yanzu tasan me ake nufi da ZAWARCI!! Ko sau daya bata taba hangowa kanta shi ba sai gashi tashi daya Allah ya nuna mata iyakar ta. Wasila ma kam yar ta na gwaruwa hannun dangin miji daga aure zuwa yanzu tayi bari akalla uku banda yara biyu da ta haifa babu rai saboda wahala gashi mijin ya hana ta shiga lamarin yace duk ranar da tayi to abakin igiyar auren ta.
  Duka suka hadu ka'in da na'in akan shirin bikin na su Sulaiman.

Rahama kam tana can taji labarin Sulaiman zai maida matar sa. Jakar uba! Ita fa wallahi da ta zauna da kishiya gara a kira ta BAZAWARA!!! sai tafi na na'am da hakan. Ko Gwaggo bata fadawa ba ta taho kano lokacin gidan babu kowa don haka Allah ya taimake ta da dan makullin ta a jaka ta bude gidan. Tabbas gashi kam an fara gyara gidan da gaske ne auren nan!!!!..............

Mu ma namu barin ana ta shiri wai har bikin Yaya Sambo ake so a hade gaba daya can a Abuja ya samo wata yarinya tana zaune gidan kawun ta tana University ta Gwagwalada amma yar asalin garin Katsina ce Daura har iyayen ta ma suna can. An yi bincike sosai kanta babu matsala. Anan quarters na ma'aikatan su aka bashi gida amma duk da haka Baba yace masa ya kukuta ya sayi fili ya fara ganin kansa. Mama kam babu zama ana shirin bikin 'ya. Wannan Karon kam Yaya sadiya itace ta dauke amarya gaba daya tace ita ai bikin nata ne. Nima bangare na ina ta shiri abuna duk da ma dai nace bana tarewa da wuri sai bayan kowa ya tafi.

WADATAWhere stories live. Discover now