NINE

2.7K 307 6
                                    

*WADATA*
   _Nine_

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💥shatuuu095@wattpad : Follow, Vote, comment and Recommend..... Ilysm

*MUQQADARI NE, KALUBALENMU, ME RABO KA DAUKA, GIDAJENMU, RAYUWARMU A YAU, MATSALARMU A YAU, MACE A YAU da WADATA. Gabaki daya mallaki na ne, all right reserved®  Ban yadda da piracy ba ko kuma wani Ya siyar min, novels dina are wholly Free idan zan siyar ni zan fada muku, duk Wanda ya siyar kanshi yayiwa, yamin guzuri....... I've seen your comments it gingered me up.... Gashi na baku kyauta! Allah Ya bar kauna*

*Anty Asma'u Madugu.... The page is yours💕💕💕💖*

A razane na tashi na jike da gumi sosai saboda tsabar yadda na razana, Sulaiman ya dube ni yace

"lafiyar ki kuwa?"

Gabana na tsananin faduwa Nace

"Eh lafiya"

tare da qaqalo murmushi Wanda ya tsaya a lips dina yace

"Na gani duk kin hada gumi, kin firgita is it a bad dream? "

Kaina na girgiza nace

" Zafi nake ji ne kawai "

yace OK. Amma ba don ya yarda ba. Nima kawai sai na share don bana so ya gano gaskiya. Gaba daya jikina yayi sanyi kalau ban san me mafarki na ke nufi ba,adduao kawai nake tayi a raina.
Ba jimawa ko sai gamu mun karaso. Garin ba xaa kira shi kauye ba don suna da ci gaba da gine gine na zamani abin sha'awa. A kofar wani gida muka yi parking, yara sai tsalle suke yi suna murna da ganin Sulaiman. Shima yana ta daga masu hannu ya karbi alawa a hannuna ya raba masu kana muka shiga gidan su yana rike da hannuna. Ba laifi gidan kato ne. Irin ginin kauyen nan me katuwar tsakar gida Kamar football field Sai wasu dakuna acan gefe daga extreme din gidan, tare muka shiga dashi. Wata doguwar mata ce ta fito daga ciki fara ce Sol! Kyakyawar gaske asalin Fulani, Tunani na itace maman Sulaiman ta taho da farin cikinta ta tare su, Da kuma yarensu tayi musu magana, a Sulaiman naji yace mata

"Wallahi kam tun shida muka fito shi yasa muka iso da wuri"

sai kuma ta sake masa magana naji ya mayar mata da fullanci ina tunanin hanya take tambayar su, ya amsa mata da Hausa ta kuma kwabe shi, Ko inda nake bata kalla ba, Haka jiki a sanyaye muka shiga ciki, Sulaiman kam baya so idan ina nan ana magana da fullanci. Dukkansu kujera suka zauna ni daya na zauna Kan carpet din,  a hankali a nutse Kaina a kasa nace

"Ina wuni Inna?"

Babu yabo babu fallasa Ta amsa da

"Lahiya lume"

Fuskar ta ba yabo ba fallasa sai naji jikina yayi sanyi nace

"Mun same Ku lafiya?"

Tace

"Lafiya kalau Ya iyayen naki?"

sai na dan ji sanyi nace

" Suna nan lafiya suna gaishe Ku"

tace muna amsawa. Daga Haka ta dauke kanta ta maida
Kan yaran ta ta koma suna ta hira ni dai nayi shiru Ina jina out of place. Lokaci lokaci Sulaiman na zungura ta da kafarsa in na dago sai yayi min murmushi. Shi a dole kar na kadaita. Can ta fita, Ahmad ne yace

"Hajiya Aunty kin wani takure"

Kaina na girgiza nace

"A'a kai kaga hakan"

yace ko? Abinci ta kawo a kwano ta aje mana tace

"Ga abinci ku shi ko? Ka shika ku da suturu"

Gabana ta aje wani kwanon abincin tace

WADATADonde viven las historias. Descúbrelo ahora