Chapter 4: The Dream

1K 103 11
                                    

     Hi Naila fans Naila would like to know how you feel about her and what is happening with her......So that we can countinue Moving Foward not the way round so kindly leave your comments.....and WhatsApp readers comments note emojis this time thanks for Reading👍
                          👇🏼
About Ayatul Kursiyu Wanda yayi saving Naila from that horrible world...Zanfada kadan daga cikin falalar Ayatul Kursiyu Ance idan an karanta Ayatul kursiyu shaidan na nisantar wurin na tsawon kwana uku..idan kuma ankaranta Ayatul Kursiyu na tsawon kwana talatin to bawani me sihiri da zai kusanci gu na tsawon kwanaki Arba'in...Manzo (S.A.W) yace " mafi girman Aya acikin Alkur'ani Ayatul Kursiyu". Bayan wannan tsokaci danayi akwai falaloli masu girma masu amfani cikin wannan Aya yan uwana muyi kokari murike wanann aya dakyau a duk halinda muka tsinci kanmu.

🅿️04

" Naila kinyi Salolinki"
Daga kai nayi alamun eh ya Nafy sake kura mun ido tayi
" Naila are sure kinyi isha'i"
Tabe baki nayi tare da maida kaina kan Tv din batare da na bata amsa ba sosai nake Jin haushin yadda suke damuna bayan especially ma ita da momy.

Ganin banda niyyar kulata yasa ta dau remote ta rage volume din ta gyara darduman ina kallonta ta tada Sallah juyawa nayi kan Tv abuna Ina kallon wani Indian film daya dauke mun hankali "Alone" film din Bipasha Basu.

" yanzu Naila kinsan yadda kike bad dreams Amma kike kallon horror film a Daren nan",

" please ya walh I love this film an kusa gama wa",

Nodding head dinta tayi " alright but you didn't had your dinner don't forget to have it ok",

" owk sis",

Kashe ligaht din tayi tare da kwanciyar ta sanina ne film din ba mai karewane a wannan lokacin ba kusan lokacin aka farashi,
Ba'a gama film dinba sai 12:30am wannan lokacin gidan yayi shiru kowa ya kwanta gashi yunwa nake bala'in Ji a wannan lokacin sai yanzu tsoro da dana sanin rashin Jin maganar ya Nafy ya dira a zuciyata.

Tashi nayi a hankali na kunna light na bude kofar falonmu Wanda yayi duhu saboda already ankashe komawa daki nayi na dauko phone dina dan banson kunna light wani ya tashi,
A hankali fita na nufi kofar kitchen din direct direct fridge na bude tunawa da nayi momy na ajiye youghort  aiko nayi sa'a nasamu yayi sanyi sosai,

Murmushi nayi nafara kwalkwala batare da na rufe fridge dinba " Ke!" Abunda naji ance kenan bansan lokacin da na saki robar youghort dinba zuwa kasa na bude baki inashirin sakin ihu ya fusgoni tare da rufe mun baki.

Kokarin kwacewa nake daga jikinsa " shhhhhhhh shut up banso naji ko peep a bakin nan naki do you understand",

Yafada yana haska kwayoyin idanuna shiru nayi Ina nodding head dina tare da kikifta idanuna idonshi na cikin nawa ya kura mun ido,

Mamakine sosai ya kamani gashi sanin halin ya Neeb ban Isa nayi kwakwaran motsi ba sam ban fahimci meyasa yake kallona haka ba,
Mun jima a haka naga yayi murmushi Mara sauti Wanda tunda nake dashi bantaba ganin yayi ba nakan dai Ji yana dariya da 'yan uwan shi shima ba kasafai ba.

Murmushin kuwa ya bala'in mai kyau nan nakara ninka yadda eyes dina ke motsawa cike da mamaki nake kallonshi nima duk da zufan da nake ga rikon yafara mun zafi,

" Me kuke a kitchen a wannan daren!",

Ya Nafy Tafada sanda ta kunna light din gun hakan yadawo dashi daga duniyar daya tafi take ya hankade ni har saida nadan bugi fridge din bai tsaya ba yasa kai ya fice.

Wani irin takaicinsa ne ya shige ni da haushi na ciza lebena Ina shafa gun da yake mun zafi ya Nafy Dariya tayi Tana kada kai,
Hakan ba karamun Kara kunna ni yayi ba hakan yasa na sunkuya nadau youghourt dina daya fadi Wanda naci sa'a bai zube sosai ba.

Fice nabarta tana Shan ruwa Koda ta dawo bata kulani ba ta kashe light tayi kwanciyar ta,
Najima Ina juyi Ina tunanin abunda yafaru tsakanina da ya Neeb Wanda sam na kasa fahimtar menene a haka bacci ya daukeni batare da bata lokaci ba nayi nisa ciki.

Garin yayi shiru kamar ba mutane yayi duhu tafe nake nidaya anguwa ce wacce bantaba sanin akwai shiba wasu karnuka na hango tundaga nesa,

Duk tsoro yafara shigata haka na daure na cigaba da tunkararsu har baje gab sukayo kaina " wooooooooo wuhw!",

Ji nayi kamar ko ina amsa kukan karnukan yake juyawa nayi da gudu suna bina na samu nayi musu nisa sosai,
Naga wata kwana na shiga aiko inakwana wasu lodin karnuka ne suka sake yowa kaina nan ma da gudu nasake diba nafito wannan kwanan.

Wani gida nagani naga kamar ana girgiza kofar gidan batare da bata lokaci ba na nufi wannan gidan duk da jikina rawa yake a wannan lokacin bakina har wani kadawa yake ga wani irin mugun sanyi,

Ina karasawa naji kofar tayi shiru alamun andaina girgiza ta na tsorata sosai amma na karasa na bude shi banga alamun kowa ba,
Haka nan na cigaba  zurmukewa cikin wannan gidan saida na kai tsakiya naga ko ina yacika da karnuka a cikin gidan Wanda sai haushi suke,

A hankali na fara kokarin ja da baya Amma me kan na kai ga daukar mataki tuni naga sun waigo sunganni,
Nan suka soma haushi inda na diba da gudu banganni ko ina ba sai cikin wani daji Wanda banda kukan na mun daji ba abunda kakeji.

" Naila karki manta kiyi Addu'a ita kadai zata fiddaki cikin wannan guri nikaina ban Isa na taimakeki ba always remember",

Muryar Dana Ji kenan kamar daga sama naji zazzakar muryar mace nafada mun hakan zama nayi tare da sa kaina cikin gwiwowina na rufe kunnuwana Ina kuka,

" hahahahahahaha Naila karki Ji tsoro taso kishiga wannan ruwan zai kaiki gida"

Wata muryar Mara dadin saurara ta fada dagowa nayi inajin kukan wani abun tsoro na dosoni wanda bana iya gani,
Tafiya na fara a hankali Ina tunakarar ruwan sakamakon galabaita da nayi bazan iya gudu ba a wannan lokacin,

" Always remember! Always remember!! Always remember!!!"

Abunda muryar nan me dadi ta fada yake dawo mun Amma still ban fasa tunkarar rafin nan ba.

" Naila kidaina wasa da addu'a dan Allah"

Zancen momyna dataimun  Yau nake tunawa kan addu'a Wanda harta bani wasu addu'oin,
Batare da na ankara ba naji ni a cikin ruwa yayinda nake ko kuwa da breath dina dake shirin barina Ina kokarin yadda zan fito na nutse can ciki gashi ban iya ko swimming ba.

Tuna wata addu'a nayi wacce momy ke yawan fada mun Tana da kyau kayi ta in zaka fita gida ko in kadawo kan dukkan abunda zakai Tana da kyau da falala kariyace babba.

" Naila muje kizama daya daga cikin mu zaki daina tsoron komai"

Wata murya ke fada mun hakan Ina runtse idona nayi duk da yanayin da nake ciki masa hannun dama na kan kaina nafara karanto "Ayatul Kursiyu" nan take nafara jin kamar Ana kwanceni,(please kukaranta saman page bayan abunda nace kan Ayatul Kursiyu akwai abubuwa da dama).

" Naila No! No!! No!!!",

Dai2 lokacin dana bude idona tare da sakin wata irin Kara sai dai abunda zai baka mamaki ba Wanda yaji,

Inakokarin motsi inayi amma Sam gangar jikina takasa najima a haka bude kofar toilet naji anyi a wannan lokacin,
" ho Naila yanzu a tashi ayi sallar Asuba ae",

Ya nafy ce Tafada sanda ta nufoni tare da daura hannun alwalanta kan forehead dina Wanda kamar ta banbarun wani abu naji na motsa,

" what! Yau kintashi kenan ba fighting ba komai lallai kinyi abun kirki da Ana ta baki zakina tashi walh da naji dadi",

Sauka nayi duk nayi zufa duk da fankar dake dakinmu toilet na wuce cike da tsoro nazo na fara Sallah harda magrib da banyi ba jiya da isha'i saida nayi bayan na idar kuwa na dau kur'anina nacigaba da karatu ya Nafy nata mamakina har lokacin da momy tashigo Wanda itama tayi mamakin ganina a hakan taji dadi sosai.....................

                   Sai mun hadu a Next page on Monday my best day Insha Allahu👏

NAILA Where stories live. Discover now