Chapter 12

810 81 8
                                    

             Dedicated to all my Fans👌

🅿️ 12

" ya akayi take iya ganin mu"

" just leave!"

Sarauniya Tafada cikin daga murya Easha cike da mamaki ta bace a fadar itama Sarauniya bacewar tayi.

Momy dakinta koma  Amma ta kasa zaune ta kasa tsaye sallamar Faddy ne yasa ta dan saki ranta,

" Aunt Lafiya Ko bakijin dadine"

Girgiza kai momy tayi " no jeki kawai Fadeela ba abunda ke damunsa he kuyi kallonku"

Batare da ta Kara cewa komai ba ta taso inda mukaci karo da ita lokacin Ina shirin shiga harara ta tayi ta wuce abunta Nima harar na ita dashi,

" mom....."

" please Naila kifita kawai I want to be alone especially from you",

Mamaki zancen yabani from me kuma tabe fuska nayi inakallonta na matsa " momy kona miki laifi ne kifadamun plea..."

" fita kibani guri!!!"

A tsorace na tashi a bakin gadon cike da damuwa nafita falon Faddy dake kofa Dariya tasa " kema kamar mayya why won't you let her be kina yi kamar wata yarta mtsw ' ya 'yanta ma sun share sai k.....",

" haba Faddy Naila fa ba Sa'arki bace me zai sa kidunga shiga harkarta kina zubda girmanki"

Tabbas kalamunta sun bala'in mun ciwo dan a duniya ba abunda na tsana irin ace momy ba ita ta haifeni ba cikin sanyin jiki nayi hanyar dakinmu Koda muka hada ido da ya Neeb tashi naga shima yayi yabar falon,

Daki na wuce Nima naje na zauna with my sad face sometimes nakanyi tunanin wani irin rayuwa nake living a wannan gidan,

Dis! Dis!! Karan digar ruwan ya soma wanzuwa a kunne na hakan ya sa na zare duka idona cike da tsoro rufe idannuna nayi da karfi tare da matse su Wanda inda Ana saboda da wahala yakamata ace nafara sabon,

" Naila! Meye kika zauna kina kuka"

Ya nafy ce kallonta nayi lokacin da tazo ta zauna gab dani tare da jana zuwa jikinta " yakamata kidaina sa irin zantukan su Faddy a rai karki manta ita  halin ta ne dama taga ran wani ya baci to meye na daga hankali ciki",

Share hawaye na nayi Wanda tabbas nasan she is right " ya baki Ji yadda momy ta mun shouting ba"

Murmushi tayi tare da kamo hannuna " I know momy bata miki fada irin haka ni kaina bantaba ganin abunda yasa tayi behaving hakan ba maybe akwai abunda yake damunta da bamu sani ba kibata zuwa Safiya",

Ta karashe Tana murmushi " But inaso nayi sallar nafila dan rokon Allah ya yaye mana damuwa"
Murmushi tayi tare zaro eyes dinta " really Naila ke zakiyi Nafila Yau alright I will tell you how to",

" kinsan matsala ta dake Naila"

Nodding kaina nayi Ina kallonta "bakison Ibada which is very bad inason fada miki Amma inkinsan ba Zaki rike ba let it be a bar zancen",

Kallonta nayi da sauri tare da kamo hannunta da karfi " please! Please!! My sister kiban I will Insha Allahu",

Murmushi tayi tare da Jan hancina " you know how to get your way with words owk then Nafila da zan fada miki indai kin rike ta dakyau Ina mai tabbatar miki zata zame miki kariya, dafa'i sannan duk abunda ke damunki zata zama waraka gareki kan duk abunda ke damunki inkinyita Insha Allahu zata dunga warware miki su inafata kinfahimceni",

Gyara zama nayi dan saurarta dakyau na dauko biro da yar paper saboda gudun mantuwa.

" Bayan kinyi Alwala Zaki tada sallah ga abubuwan da Zaki yi a ciki kamar haka.......

  " Raka'a ta farko Fatiha da Aya daya daga cikin Suratul Bakara, sai kiyi Ruku'u bayan kindago daga Ruku'u saiki karanta Aya daya Ko biyu daga Suratul Yasin ba tare da anyi Fatiha ba, sai ki Kara yin Ruku'u sannan Ki karanta Izaja'akal Munafikuna Aya uku, Saiki dago kiyi Sujjada idan kika kuma mikewa tsaye saiki karanta Fatiha da Izaja'a sannan kiyi Ruku'u bayan kin dago saiki saiki karanta Tabatyada banda Fatiha, Saiki kumayin Ruku'u idan kika dago saiki karanta Kulhuwallahu, Falaki da Nasi sannan kiyi Sujjada kiyi Tahiya kiyi Sallama",

Shiru tayi tadan nisa kafin ta dubeni " nasan duka kin iya dan haka kiyi kokari Naila please kiyi hakan",

Murmushi nayi tare da rungumeta " thanks a lot my luvly  sister Insha Allahu I will"

" so what are you waiting for"

Dariya nayi na tashi na nufi Toilet cike da farin ciki na shiga batare da addu'a ba sam abunda idona yafara cin karo dashi shine drop din ruwan dake diga daga Tap din a hankali Wanda nake Jin karar shi har brain dina,

Lokaci gudu na hango Faty yar makotanmu da bata wuce 3yrs ba tana struggling da ruwa Wanda ke sinking dinta tana motsawa lokaci guda naganni ciki gab da ita bata numfashi Amma a wannan lokacin Kara na bude bakina zanyi lokacin da ruwa yashiga ciki nan take nafara struggling da numfashi na dake shirin daukewa a wannan lokacin,

" Naila! Naila!! Naila!!!"

Wannan muryar matar Dana saba jine tadawo rufe idanuna nayi lokaci guda aka daka mun tsawa,

" Get up!!!"

Cikin wata irin murya me tsoratarwa na bude idona still na ganni a toilet din a tsorace nafito daga toilet din ganin Faddy nayi saman bed dina Wanda banda buri a yanzu daya wuce na kwanta akai,

Momy ce tashigo " kun kwanta ne!"

Kallon bed din ya Nafy nayi Wanda already tayi bacci shigowa momy tayi kallona tayi Tana murmushi ta kalla Faddy wacce kunne ta ke makale da earpies Tana latse2 phone dinta,

" muje Ko yar autana"

Momy Tafada tare da Jan hannuna Tana mun murmushi muka fita zuwa dakinta " kinyi Sallah" nodding kaina nayi nace " eh",

Kuma Sam banyi ba Amma banso nayi disappointing dinta a yanzu dana ganta cikin farin ciki " get on the bed" hawa nayi Ina Jin kamshin gadon nata me dadin gaske,

Bargo taja ta rufe ni " bari inazuwa make sure you pray ok"

Fita tayi Jan bargon nayi me kamshi inajin dadin kasancewa ta dakin momy na najima inajuyi karshe bacci yayi awon gaba dani bansan lokacin data dawo ba sam.

" Maraba da zuwa"

Aka fada cikin wata yar Kankanuwar murya wadda take kamar ta yara waigawa yayi yana son ganin ta inda muryar take,

" hahahahaha Maraba da zuwa"

Wannan karon cikin babbar murya aka fada Wanda za'a iya Kira gardin murya lokaci guda kuma wani dan karamun yaro ya bayyana,

"Kana iya zama" nuna mishi mazauni akayi nan kuwa ya zauna batare da musa ba nan take yaron ya koma babban mutumi Wanda Ko kadan baida kyan gani,
Wanda duk gashi ya gama baibaye shi a jiki abun kyama abun tsoro.

" Nasan meke tafe dakai Amma kasa ni Naila bazata haukace a yanzu ba akwai sauran lokaci hahahahaha zata cigaba da firgita da tsorata da gane2 Amma burinka ba mai cika yanzu bane",

Da sad face dinshi ya kalla bokan " Meyasa yanzu nakeso amun hakan nagaji da jira sai yaushe"

"Yi mana shiru ba'a ja da zancenmu a nan tunda ance maka kaje kaje din ka cigaba da ba wannan abun jini yanzu haka yana bukata zaka ga next jinin yaron da yake so hahahah",

Tashi yayi batare da yakara cewa komai ba yabar gun bana iya ganin fuskarshi saboda lullube yake da ma yafi me kauri Wanda hakan bai wuce nasaba da sanyin da ake tsugawa a wannan lokacin.

Juyi nazo yi najini kusa da mutum a tsorace na tashi har na dan buge ta batare da na saniba
Kokarin sauka kan bed din nashiga yi naji ta rikoni " Naila is just me kinyi mafarkine",

Jin muryarta yasa nakoma na rungumeta " baki yi addu'a danace kiyiba Ko oya tashi kiyi addu'a" ta ban baroni daga jikinta tashi nayi nayi addu'oi na koma Tana rike dani Tana shafamun baya hakan yasa nayi feeling very safe,

Ban dau lokaci ba bacci yayi gaba dani me nauyin gaske...................




                Ayi hakuri da short page kunsan yanayin jikin sai a hankali nagode da comments dinku a Koda yaushe don't forget to share, Vote👌👍

NAILA Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora