Chapter 17 : The care

812 60 1
                                    

                 surprise
нow do yoυ lιĸe мy ѕυrprιѕe ι aм ѕorry ғor ĸeepιng yoυ all waιтιng ιnѕнa Allaнυ yanzυ zaĸυ cιgaвa da jιna yadda yaĸaмaтa nagode ѕoѕaι da ĸυlawarĸυ..


               dedιcaтed тo 80ĸ 😃 naнυтa ĸo

🅿️17

" Mom! Mom!! What is wrong with her",

" Neeb just kataimakeni kawai mu shiga da ita ciki now is not the time for question son!"
Jikin Neeb ma rawa yakara so ya rikoni duk Sam banso hakan ba da lafiyata kalau Amma yanayinsa bakomai banda tashin hankali,

" Mom slowly maybe tana Jin zafi"

Yafada ganin yadda momy burinta kawai ta shiga dani gida a wannan lokacin duk a rude take ya Nafy da sauri ta tashi itada Faddy " meya sameta momy",

Suke tambaya ba Wanda momy ta amsa direct dakinta suka wuce dani itada Neeb suka kwantar dani tashi momy tayi da sauri tana kallon Neeb Wanda yake a hargitse shikansa.

" Muneeb ku kula da ita I have to collect some medicine for her kaji zandawo yanzun nan"

Banda daga mata kai ba abunda Neeb yake ya Nafy harda hawaye " Naila! Naila!! Meya sameki",

" Nafy bata iya magana a yanzu just look after her kubata ko tea ne"

Ficewa momy tayi yayinda ya Nafy tawuce kitchen " Neeb kazo dama akwai ab.....",

" shut up! Baki ganin meyake faruwa ne  just get lost before I end up doing something regrettable"

Tsaki taja tare da cinno baki duk akan ido nane maida dubansa guna yayi " Naila meke miki ciwo please tell me what do you want I will check it for you meya faru"

Duk wannan tambayoyin ni yake jeroma wacce Ko magana bana iyayi " please Naila try and say something"

Zazzare ido na fara sakamakon muryar da naji " Naila help me!!!"

Muryar momy naji hakan yasa na fara kokarin motsi ta karfi " Naila meya faru Naila!"

Yafada lokacin ganin yadda nake zaro ido ina mimmikewa da gudu ya Nafy ta shigo " Neeb meyake faruwa",

" innalillahi please Naila meyake damunki"

Tafada tana rirrikeni itama ganin yadda nake kallon sama yasa tafara tofamun addu'a a hankali nadaina ji nan take na sama nutsuwa.

" Alhamdulillahi she looks owk now jeki kawo tea din"

Fita tayi tana mamakin kulawar da ya Neeb keban yanzu ita da kanta nikaina banda kallonshi ba abunda nakeyi duk yabi ya damu hankalinsa a tashe,

Bata jima da  fita ba tashigo dauke da cup din inda ya karba ita kuma ta taimaka waken zaunar dani,

Debo tea din tayi a cokali tasamun a baki da zafi bata sani ba hakan yasa na zaro ido aiko kan idon Neeb.

" mtsw bani cup din kije baki hura abuba kinbata zaki konata jeki zanbata"
Dan zaro ido tayi cike da mamaki zai bata kuma Amma tasan in tace zata musa mishi rigima zata dauko ma kanta babba hakan yasa tafita batare da tamai musu ba.

Matsowa yayi kusa dani " sorry Naila"

Yafada lokacin da yafara debowa yana hurawa yakaimun a Farko kamar bazan karba but yadda naga damuwar dayayi yasa na bude bakina ya zubamun,

Murmushi yayi alamun yaji dadin hakan sosai murmushinsa bansan meyasa naji wani irin dadi ganin yadda yake murmushi ba,
Bansan lokacin da na lumshe idona na bude ba kallona ya tsaya yi bansan me yake jiba naga ya kuramun ido sosai.

NAILA Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt