Chapter 40

953 74 4
                                    

Don't forget to follow me on insta@Mimsqueen
      Also don't forget to subscribe our YouTube channel @Hasken Alkairi Tv Naila Voice will soon be with you soon Insha Allahu Thanks all 👏

               Dedicated to Hajiya Maryam (jikar kulu) and her doughter for their long comments👍 and zeeY Farfaru 👍I know kuna da yawa but wannan nasu ne su uku.

🅿️40

1week later........
Zaune nake baranda din Ina game a phone dina na bubble lokacin da naji motsin mutum akaina gabana ne ya fadi Amma Sam hakan baisa na daga kai na kalla waye ba sai dai inajin alamun ni ake kallo ga kamshin turaren me karfi Wanda ke shirin taso mun da mura.

"Naila!!!"

Muryar dady ce ta sauka a ears dina a hankali na daga kaina na kalleshi tare da amsawa cikin sanyin jiki dan Sam kwanakin nan narasa gane abunda dady ke nufi especially irin kallon da yake mun.

Murmushi ya tsareni dashi sosai Wanda Sam ni banson yadda yake nuna mun wasu alamomi da nake yawan karantawa a littafai da films Amma nakasa gasgata me yake nufi Sam.

"Ina 'yan uwanki kike zaune nan ke daya"

Yafada yana kare mun kallon kurilla maida kaina kan wayata nayi lokacin Dana bashi amsar suna ciki.

Bangaren Dady tunda boka ta bukaci yayi using Naila yake matukar Jin feelings kanta Wanda da Sam baiji ga kyau ga diri ta hada duk irin abunda yake son gun mata dama can ya kasance na mata sosai a waje yawancin rikicinsu da hajiya Amina bai wuce kan bin matansa ba.

" kituran account no dinki inason sa miki kudi tun shekaran jiya nafada miki Ko and banso Ko momynku ta sani wannan naki ne ke daya kinji 'diyar Albarka".

Yakara she yana murmushi nan ma kasa magana tayi ta daga mishi kai Ko a jikinsa wuce wa yayi yashiga motar sa yanayi yana waigenta harya shiga yataba mota yafice gidan bata daga kai ta kalleshi ba Sam.

Haka kawai na tsinci kaina da shiga cikin duniyar tunani narasa gane meyasa duk lokacin danaga su dadyn Farid sai gabana ya fadi sam sosai nayi nisa a duniyar tunani.

Muneeb ne ya shigo tundaga nesa ya karanci Sam bata cikin hayyacinta especially ganin littafin dake hannunta Amma Sam fuskarta bata hakan ya tabbatar mai zuciyarta baya gun sam girgiza kai yayi yakarasa daga dan gefenta ya tsaya,

Murmushinsa me kyau yayi Wanda ke rikita Nailansa irin na gefe daya saba jingina da bangon tare da zuba hannayensa cikin pocket dinshi kamar yadda ya saba dan lekata yayi yaga wayarta dake kan jikinta zaro wayarsa yayi yashiga dialing din no dinta.

Ringing wayarta tashiga yi Tana vibrating akan jikinta Amma Sam bakiga alamun tajiba mamaki abun yabasa yakara tsura mata ido " what is wrong with you haka!".

Yafada a zahiri sanadiyar dan ramar dayaga tayi sosai yacigaba da nazarinta jin shirun yayi yawa yasa yasake dialing din wayarta yana kallonta gabansa ke faduwa Wanda baisan dalili ba Ko yanayinta ya firgita shi oho.

Cigaba da vibrating wayar tayi har saida ta kusa katsewa nadawo hayyacina inda gun daukar wayar Ina nemanta tafadi kasa tare da book din dake hannuna duk na gigice dakyar nasamu na dauka wayar Amma tuni ta katse ganin "Ya Neeb" naji nakara rikicewa hannuna na rawa nashiga kiran.

"Wayoo Nashiga Ukuna Ya Neeb ne!"

A tsorace nafara kokarin nemansa nasa a kunne na jikina na rawa.

NAILA Where stories live. Discover now