Chapter 19

800 59 2
                                    


                        No Edition

🅿️19

Bayan momy tafito taban abinci nafara ci kenan lokacin da mukaji sallamar su goggo dai2 ana kiran magrib fuskarsu ba walwala sam a cikinta,

" Ah yaya bark...."

Hannun da goggo ta daga mutane yasa taja bakinta tayi shiru " ina Alin!"

Abba yafada kana Jin muryarsa kasan cike yake da bacin rae " nifa banga amfanin zuwa nan bafa",

Harar da Abba yamata yasa umma tayi shiru kokarin gaishesu muke Amma cikinsu ba Wanda keda niyyar amsawa " Karima kikiramun Aliyu duk inda yake kusanar mishi ina jiransa yanzun nan"

Momy na kalla wacce kana kallonta zaka fuskanci damuwa a tattare da ita fitowar Dady kenan da alama masallaci zashi ganin yayyun nashi yasa gabanshi faduwa,

" muje masallacin mudawo a zauna" Abba yafada juyawa sukai suka tafi masallaci muma duka shiga alwala mukai dan gabatar da sallah.

Falon tsit kake ji kamar ba alamun 'yan Adam a ciki dukanmu munyi shiru abba me ya nisa ya kalle inda muke nida su ya Nafy,

" Kutashi ku bamu guri ba zancen Ku bane"

Sanin ba lafiya yasa muka tashi muka bar falon Koda muka koma daki muna iyajin abunda suke fada a falon dan da karfi Abba yake ma Dady fada kan shiga fadan yara da yayi da abubuwan da yake na gorace2,

" Nifa gaskiya yaya kuna takuramin duk abunda nake bakwa gani nama 'ya 'yanku na muku ya ke yaushe sule yazo garin nan nab....."

" yimun shiru indai kudin Kane zance yadawo maka dashi"

" A'a Aisha ba wannan zancen kibarni dashi naji uzurorinsa kan abubuwan da yake tukunna",

" dan Allah yaya kuy..."

" karimatu banson Jin maganar Ki wannan karon kullum ke kike bada hakuri kina karyar mana da gwiwa yakamata Yau na fada mishi abunda ni bantaba niyyaba" zata kuma magana Abba ya dakatar da ita.

" Aliyu intambayeka waya kawo ka garin nan"

Shiru Dady yayi hakan yaba Abba damar cigaba da mai maganganu " kuma da kake batun biyama Nabil kudin makaranta kan Ka biya masa niban biya maka ba?"

Shiru nan ma Dady yayi tare da sunkui da Kansa kasa " tambayarka abu nake Aliyu kayi shiru"girgiza kai abba yayi cike da takaicin dan uwansa,

" sai batun yarinyar nan inajin labarin yadda kadau tsana Ka daura mata dan kana rikonta intambayeka mana m..."

" A'a yaya banso Ka kai nan mudai mai fada Amma karmu"

Girgiza kai abba yayi " Aisha Ko Kunaso Ko bakwaso saina tada zancen nan yasan kallonsa kawai nake"

" Ayi hakuri yaya"

Momy tafada cike da damuwa itama " duk abunda zaku ce ansaba dan haka Yau zanmai tuni naga alama ya manta sai ana tuna masa,
" intambayeka dukiyar da kake takama da ita takace",

Shiru falon yayi na dan wasu lokuta kafin Abba yayi ajiyar zuciya " hmm Aliyu kenan Ka dai dunga tuna dukiyar marainiyace kake juyawa idan Ka zaluncita walh sai Allah ya kwatar mata hakkinta dan haka zaifi kyau idan kayi gaggawar gyara dabi'unka muba yara bane inaso daga Yau duk abunda zaifaru tsakanin yaran nan karka kuma shiga bakafi karfin nasaka kona hanaka ba haryanzu, sai batun Nabil kobaka biya masa ba Allah bazai hana yadda zai koma ba",

Nan dai suka cigaba da tattaunawa karshe Dady yabasu hakuri umma kam haryanzu da alamun bata hakura ba Sam haka sukai sallama momy tayi2 suci abinci Amma Sam taki haka suka tafi Dady yagama kunkuninshi yafita abunsa,

NAILA Where stories live. Discover now