Chapter 11 : 4eyes

1K 102 10
                                    

                    Thanks for all the prayers and also Naila gaidaku inajin dadin sakwaninku masu son farko please visit my wattpad page Zaku samu daga inda kukeso thanks for comments, votes share inagodiya kwarae da gaske👏👍



🅿️ 11

Yau da mura na tashi sosai amma haka na shirya school bayan mun kammala ne mukai break fitowa mukai muka tarar da Ya Neeb gun mota sunkui dakaina nayi tuna abunda ya faru tsakaninmu jiya,

" bro kai zaka kai mu kenan" tsaki yaja yana kallonmu " inba nibane Zaki ganni ne a nan wai Ina musa driver ne mtsw",

Yadan bugi motar " inakwana",
" Lafiya" ya amsa mata tashiga  tsayawa nayi agun kamar dutse kaina a kasa bansan ya shiga motar ba naji kawai yama motar key da sauri na dago mukai 4eyes dashi,

Nan take naji gaba na ya fadi dan wannan eyes din nashi ba komai cike sai tsana Wanda wannan zuwan bangani cikin su ba sai Yau " bro please ka tsaya ta shiga mana" naji ya Nafy namai magana,

Wucewa nayi sadaf2 naje zan shiga baya wani tsawa ya daka mun Wanda najima banji ta hakan ba " Ke!!! Ubanwa ye driver dinki"

Jikina na rawa na sake hannun kofar naje nashiga gaban " haba bro Yau meke damun Kane haka naga kamar haushin mu kakeji Yau din nan waya taba ma....",

" Will just shut up Nafy!"

Hakan yasa taja bakinta tayi shiru ba Wanda yace ma kowa komai har muka sauke ya Nafy inda mukai sallama da ita gabana ne ya cigaba da faduwa saboda gudun da yake shararawa a titin har muka kai gate din shiga school dinmu yayi parking  din motarsa,

A hankali na kai hannu zan bude na fita " don't!",

Yafada tare da daura kansa kan stearing a dan tsorace na saci kallonsa idonsa a rufe suke yayinda daya hannunsa ke kan kirjinsa kamar Wanda ke sauke ajiyar zuciya mun kai kusan 10mins inaji aka kada mana assembly
" you can go" Yafada cikin wata irin kasalalliyar murya kallonsa nayi inatunanin kamar he is sick dan yadda yayi maganar,

Fita nayi tare da mishi bye2 Amma ko saurarata baiyi ba yaja mota yabar gun haka nashiga school kamar yadda na saba.

Gida ya koma cike da damuwa zuciyar shi yana shiga yaga mota alamun sunada baki a gidan " who could it be this early"
Tsaki yaja ya shiga cikin gidan direct part din su momy ya wuce dan bata key din motar dady,

Wata hadaddiyar budurwace zaune kan kujerar falon ita ba fara ba ita kuma baza'a kirata da baka ba kallonta ya tsaya yana nazarin inda yasanta duk da baya iya ganin fuskarta,

Rabin kirjinta bude yake zuwa kafadunta saboda yanayin dinkin tana dukiyar Fulani Masha Allah kana iya gani daga nan "Neeb!",

Da sauri ya dauke idannun shi daga kallon budurwar wacce tayi tsalle ta tashi Jin momy ta ambaci sunan shi murmushi tayi Tana kallon Neeb dake tsaye gu daya yana kallon momy.

" hi Neeb!"

Tafada sanda ta karaso gabanshi tare mika mishi hannu bai mika mata nashi ba a dake yace " Salamu Alaiki" hakan yasa budurwar sosa kanta alamun Jin kunya,

" Neeb kar dai kace mun baka gane Fadeelah b..."

" No Aunty faddy" dan kallonta momy tayi cike da takaici Neeb kuwa tuni ya ganota hakan yasa yayi murmushi a ranshi yana kallonta ya kallah Momy " you mean she I.....",

" yes your cousin yarinyar Auntynka dake NDC kagane ta yanzu" sake kallonta Neeb yayi tabbas itace wannan yar iyayin da bazai manta halinta Wanda dalilinta ya daina zuwa gidan su gashi kuma Tana son zama matsala  a rayuwarshi,

NAILA Donde viven las historias. Descúbrelo ahora