Chapter 6

1K 92 1
                                    

           Dedicated to Naila fans and also to 80k thanks for everything👍

🅿️06

Dakinmu na shiga na zauna Ina ajiyar zuciya a hankali nake tuna abubuwan da suke faruwa tsakanina da ya Neeb closing eyes dina nayi
Sakamakon tuna lokacin da ya matso so close I can't take the feeling cewan is like kissing dina yaso yi dan inagani a film
Matse idannun nawa nayi Ina ganin lokacin bude eyes dina da sauri nayi.

" No he hate me ne kawai ba kissing dina zaiyi ba he just want to hurt me only lovers do kiss",

Ni kadai nake duka wadan nan surutan kai ka rantse bani daya nakeyi ba muryoyi naji a can babban falo ana oyoyo,
Tashi nayi da sauri nayi waje zuwa inda nake Jiyo hayaniyar muryar goggonmu najiyo.

" Ina Naila ne!"

Ae da gudu na shiga falon na nufeta tsalle nayi tare da hugging dinta " wayo zata karyani",

Dariya su momy suka saka Nima dariyar nake sanda na sauka daga jikin nata kallona tayi
" wai haka kika Kara girma Naila",

Murmushi nayi " kai goggo daga zuwanki" Na fada Ina tabe baki Dariya ta sheke dashi.

" yo ai wannan naje dake kauye yanzu zan sha sallama da samari"
Dariya momy ta fece dashi Tana kallonmu,

" a kauye ae naga kamar Naila akema aure",

Ya nafy Tafada juyawa nayi na harareta gwalo ta mun Tana Dariya " sannu da zuwa yaya ki zauna ki huta mana",
Momy Tafada sakamakon goggo Shatu ita ce babbar yayar su dadynmu da nawa dadyn uwa daya uba daya Tana matukar sona Sam bata son ganin bacin Raina a rayuwarta.

" sallamu Alaikum"

Sallamar su ya Neeb ne ya katse hirar gajiyar mota da goggonmu ta kwaso gaishe ta suka shiga yi,
Cikin girmamawa tana amsawa maida dubanta kan ya Neeb tayi " shugaban miskilinci haryanzu kana nan da halinka ko ka sauya ya kasar turai din",

" tab goggo ae me hali baya fasa halinsa sai Wanda ya karu",

Ya Nabil Yafada kai mai duka ya Neeb yayi Dariya goggo tayi " karma ya sauya sai yazo neman aure a hanashi mata muga tayi",

Murmushi kawai ya Neeb yayi nikuwa Sam banson hada ido dashi tashi goggo tayi
" karima wanka nakeson yi kan akira magrib akwai buhu da akashiga dashi kitchen ki bude muku Kar kayan ciki su lalace a baza wash",

Tafada lokacin da take kokarin tashi daga kujerar " oya Naila kai ta guest room maza ki hada mata ruwan wanka" ,

Tashi nayi na dau yar jakar tata mukai ciki toilet direct na wuce dan hada nata ruwan wanka cikin kankanin lokaci kuwa na hada mata,
Na fito " goggo na hada miki" murmushi tayi Tana kallona " to yar albarka jeki to nagode in na fito zankiraki muyi hira",

Kai na daga mata na fita sosai nake Jin son goggona a hankali nake tafiya harnazo wuce kofar su momy naji maganar momy hakan yayi matukar shocking dina yasa nakasa daga kafata daga gun,

" Meyasa zaka amsa mata tazo da tace zata zo din nifa nasha fada maka banaso 'yan uwanka na zuwa mun gida Sam banda gulma da kwadayi meke kawo su"
Inaji tana ta balbalin fada Tana mita " haba karima ya kikeso nayi kinfi kowa sanin halin yaya in tace sai tayi kawai kiyi hakuri nasan ba jimawa zatai ba a nan din",

Mamaki ne ya kamani saboda tunda nake da ita bantaba Ji Tana fada ba bare irin wannan fadan kan 'yan uwanmu,

" kai ka sani Amma kasan nayi gaskiya ba zan iyaba da sa ido irin nasu",

Amma banda abun momy ae goggo bata da matsala kuma ba wani zuwa suke gunmuba sai lokaci2 take wannan mitar Anya ko sun taba mata wani abunne dan momy na Sam ba haka take ba ban ankara ba sai ganinta nayi tafito daga dakin,

NAILA Where stories live. Discover now