Chapter 47: Accident

814 76 14
                                    

          I am sorry for not updating Soon abubuwa sai a slow nagode naga sakwanninku wasu daga cikinku kukara hakuri....👏


         Dedicated to all My Fans👌



🅿️47

Harna kwanta bacci ban kara ganin Momy ba duk yadda naso ganin ta hakan bai samu ba.

Dady bai dawo gida ba sai kusan 11:45pm na dare kamar Wanda ruwa ya cinye haka ya shigo cikin gidan duk a takure kallo daya zaka mishi ka fahimci shidin wayene.

Tunda ya fito cikin motar yake kallon kofar da zai sa dashi da cikin gidan yadan jima yana kaiwa da komowa kafin ya nufi kofar bala maigadi mamakin yanayin uban gidan nashi yayi sosai.

Da sallama ya shiga falon Amma tsit yaji ba alamun mutum ba kamar yadda ya saba gani ba falon ba kowa komai a kashe cikin dan hanzari ya nufi part dinsu nan Koda ya shiga falon bai tadda kowa ciki ba girgiza kai yayi ya nufi kofar dakin nasa Amma Sam nan ma ba alamun Karima tsayawa yayi yana Karema dakin kallo da fargabar yadda haduwarsu zata kasance.

Ko meya tuna Kuma saiya fito dakin ya nufi dakin ta Koda ya sa hannu ya murda a rufe yaji kofar hakan ya tabbatar mishi da bata son ganinshi sam.

Karima dake kan dardumarta Tana Jin sanda ya murda Amma Ko alamu da niyyar tashi batai ba Sam.

" Karimatu! Harkin kwanta ne".

Tana jinsa tayi banza dashi shima Jin tayi shiru yasa yawuce dakinsa Daren dai ba'a magana Sam haka Momy ta kwana Tana nafilfilu Ko zata sama saukin zafin Kishinev dake azalzalarta.

" Today and now you most call him!" Matar Tafada wacce kallo daya zakai mata ka fahimci itace mahaifiyar Asmy.

" Amma mo...."

"Shut up and call him right now dan Walh gobe zamu dira kaduna muga iyayensu Su San abunda kuka aikata".

Asmy wacce idonta banda hawaye ba abunda zaka gani duk ta rame ta lalace saboda tsangwamar said take samu kan cikin dake jinkinta daga gurin 'Yan uwanta jar wayar tayi tashiga kokarin nemo Nabil Momynsu na tsaye kikam kanta.

Tafe yake tun bayan fitowarsa daga gun dadynsu yake Jin kamar ana binsa a baya Kuma yana ganin wata mota dake ta faman binsa duk inda yayi nan take hankalin Nabil ya tashi.

Wayarsa ce ta shiga ringing da sauri ya dauka batare da ya duba Ko waye ba " hello!".

Baikaiga sake fadar wata kalma ba from nowhere wata mota tazo tasha gabansa inda ya danna wani irin burki tare da sakin wayar saboda yadda motar ta tafi kana iya Jin karar da tayi lokacin da kansa ya dan bigi steary din motar.

Banda ajiyar zuciya ba abunda Nabil yake kansa still Tana kan steary din " hello! hello!! Nabil are you there wannan sound din na miye".

Muryar asmy ce hakan ya tabbatar masa ita ke Kira a hankali ya daga kansa Amma yana dagawa yaga mutum tsaye gabansa rike da gun kafin yayi wani yunkuri harya shooting dinsa karar da Asmy taji kusan sai uku yasa ta kara Riki cewa gun kiran sunansa Amma ina dip kake ji.

"Momy! Nabil!!"

Tafada ma mahaifiyarta data sata gaba "yes Nabil meya faru?"

NAILA Where stories live. Discover now