Chapter 48

858 82 6
                                    



                        Dedicated to All My Fans👍

                     Not Edited😓
🅿️48

" A gaskiya Aliyu Nasan muna abubuwa Amma Sam bantaba tunanin zaka iya ma Nabil jininka wannan mugun aikin ba Sam".

Kallont yayi tare da girgiza kai yana murmushi "Haj .Maryama kenan to meye aciki meye Kuma abun tausayi kan yaron dake son ja dani Aliyu!".

Yakara she yana nuna kansa yana murmushi me sauti yayinda take cigaba da kallonsa cike da mamaki tabe baki tayi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya ta dau glass cup din gabanta tasha dan juice din dake ciki ta mayar ta ajiye suna kallon juna.

" hmm yanzu meye plan dinka kan Kawata ne da kuma Raheenat?".

Kallonta yayi ya girgiza kai " banda wani plan a yanzu but gaskiya ina cikin damuwa kan yanayin Karimatu kinfi kowa sanin yadda nake son karimatu a duniya Walh fishinta na masifar damuna sosai a rai".

Girgiza kai maryam take tun sanda yafara magana harya Ida Tana kallonshi Amma takasa tausaya mishi sam.

" hmm namiji Kanin Ajali Alh.Aliyu kenan kana zancen nan kamar forcing dinka akai kan Raheenat bakai ke sonta ba"

Shafa gefen bakinsa yayi tare da maida hannayensa duka kan desk din " Amma kinsan sha'awa ce ta kaini ga abunda yayita faruwa tsakanina da Raheenat kinfi kowa sanin ba laifina bane Raheenat tajawo duk wannan abubuwan da muke ciki a yanzu da tunfarko bata takura tayita bina da son zuciyarta ba da ba'azo wannan gun ba yanzu".

Ba mamaki a fuskarta saima murmushi me sauti datai masa " uhm mu ae gani Ka kasa mu'amala ta Alaka irin wannan dani kaje kana bin Raheenat yar yarinya ae gashi tasa Ka a tsaka maiwuya nibama abunda yafi damuna irin Karimatu da 'Yan uwanku su San gaskiyar lamarin".

Shiru tayi Tana kallonsa Wanda sosai taga alamun damuwa kwance kan fuskarsa " Amma meyasa Ka nema da ajanye hankalin Raheenat kan yarta a Kuma mantar da ita Abunda yafaru a wannan ranar kaf".

Girgiza kai yayi yana kallonta " hmm maryama kenan yo yanzu Ai inkin lura asirin ya karye Wanda akai kan Naila tunda gashi Tana bin yarta Tana so bandamu ba Amma wancan yazama dole karta tuna kinfi kowa sanin sirrin".

" uhm tunda haka kakeso shikenan" takara she tana tabe baki tashi tayi ta zaga ta nufi side din da yake  tana kokarin tabashi ya tashi da sauri yayi ya janye.

Cike da takaici ta maiada hannayenta da idannunta da suka soma kadawa tayi baya zuwa seat dinta tadau handbag dinta yana kallonta tamai sallama ta fita ajiyar zuciya ya sauke ya koma kan kujerar sa ya zauna abunsa cike tunanin zantukan da sukai da haj.Maryam.

"kawata kina Ina?"

Banji me a kace mata daya part dinba naji Tana Dariya " haba kawata bai kamata Ki koma ba daga dawowa haba dan Allah".

Shiru tayi Tana cigaba da sauraran abunda can part din ake fada mata " Kai dan girman Allah yaushe Nabil din?"

Ta jero alamun tambayoyi lokaci guda  ta cigaba da sauraron abunda ake sanar mata.

" innalillahi wayo Allah yakyauta ya Kara tsarewa wani hospital ne".

Girgiza kai tayi tare da yatsine fuskarta Tana turo baki " to inkindawo nazo gida zancen na gidana tabbas".

NAILA Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora