Chapter 46

913 99 20
                                    

         The Best Day is here once again Jamma'at Mubarak to all my readers ina mana Dayan Alkairi a wannan rana Allah ubangiji ya boys mana bukatunmu na alkairi ya daura nagari akan mugu a duk inda suke yakuma tsare da dukkan sharri Ameen👏


Dedicated to all my Fans.......Not Edited.

🅿️46

Momy tuni ta rude Tana motsa Naila dake kwance jikinta Tana kallonta Amma Sam ta kasa furta Koda kalma daya ce.

Da gudu Raheenat ta nufesu tare da fisgo Naila daga rikon da Momy tayi mata " Naila!!!".

Naila zaro ido tayi saboda tsoro ganin mahaifiyar tata nan take idannunta suka rufe tare da sauke wani dogon ajiyar zuciya nan Farid ya nufesu yafara duba Naila inda ya shaida musu da suna bukatar Gi me iska a yanzu " And one more thing Aunty inaga a yanzu bai kamata Ki bayyana gareta ba saboda she is already in a state of shock so please stay away for now".

Momy cike da mamakin karfin hali irin na Raheenat take sosai kowa ya fahimci hakan Amma kowa yana tsoron yin magana saboda tashin hankalina dake gabansu.

Ana fitar dasu ne dadyn Farid dake kallonsu Wanda maganar shi Sam bata fita saboda yadda bakinsa ya murde gefe ganin zaa barshi shikadai yafara kokarin musu magana haj.Amina cike da tsana take kallonsa Tana mishi Allah ya Isa ta fice batare da kowa yabi ta kansa ba suka barshi agun inda yafara Jan jiki yana matukar daya sanin abubuwan daya aikata a rayuwarsa tabbas dama karshen masu hali irin nasa baya kyau Sam.

Koda aka fiddasu falo addu'oi Momy da Su Farid sukai ta ma su Naila cikin ikon Allah bakin Ziyad ya bude banda kallon dan uwansa ba abunda yake " Zahed!"

Abunda yafara iya fada kenan lokacin daya fara motsa hannunsa zuwa na dan uwan Wanda idonsa ke rufe yana numfashi Amma kamar matacce haka yake.

Tashi Momy tayi dan hankalinta yafara dawowa gareta Sam taji ta tsana ganinsu a yanzu hatta Naila bata Jin Tana son ganin ta tashi tayi ta sauke kan Naila dake kan cin yar ta zata tafi taji anriko zaninta.

Koda ta waiga ido biyu sukai da Naila " Momy! Momy!! Momyna kindawo".

Cike da farin cikin ganin Momy nake wannan maganar haka nan Momy ta tsinci kanta da matso kusa dani da sauri ta rungumeni wasu irin hawaye masu zafi Momy take irin rikon da tamun kamar za'a fuskgeni kowa dake gun shiru yayi cike da tausayinmu dagani har Momyn.

Banda Raheenat da ke kallonmu cike da tsanar Momy ganin yadda yarta ke kiran wata Momy Tana rungumeta kasa jurar hakan tayi tabar falon.

A hankali Momy ta sakeni ta dago Tana share hawayenta " Sannu Naila Allah yakara miki Lafiya kina bukatar hutu Ki kwanta Ki huta kinji".

Girgiza kai nayi dan tunda tafara maganar nake kallonta " Momy mu tafi gida".

Girgiza mun kai tayi " aa Naila kitsaya Mahaifiyarki ta dawo".

Zancen ta yasa natuna naga real Momy na dama ba mafarki nake ba dagaske ne kenan still nikam bazan iya zama ba Momy na ba girgiza mata kai nayi " please Momy Ki daukeni a cikin wannan gidan dan Allah Momy".

Nafada kamar zanyi kuka girgiza kai tayi Tana shirin magana Momy Raheenatu tafito " Ki zauna my doughter najima inajiran ranar da za'a ce gani gaki".

Takaraso Tana mun murmushi duk gun shiru sukai hatta dadynmu rasa bakin magana yayi karaso tayi tariko hannuna Amma na lura da harar Sarai ma Momyna Sam banji dadi ba duk da ita ta haifeni bana Jin zan iya baron Momy nakoma gunta.

NAILA Where stories live. Discover now