1

12.2K 470 11
                                    

KALLON KITSE PRT 1..................

     Garin yayi zafi gashi bbu wuta, haj. Fatima wadda akafi sani da inna, tana fita asaboda zafin da garin ya dauka, duk data bude window da kofar falon da iska yake shiga.
Daga bakin kofar falon ta tsinkayi sallama, ta dago kanta ahanka tareda amsawa, wa alaikussalam, a'a maraba daku. Tamike ta zauna yadda zaji dadin magana. Shatu kece a yau? Shatu ta karaso cike da ladabi ta russana ta gaida inna, inna ina wuni? Lafiya lau ya hanya? Amma kam kun dauko zafi, cikin wannan uwar ranan da ai saiki bari har rana ta sauka ko? Tace inna wlh kam akwai ranar, saidai inaso inkoma a yau dinne shiyasa. Toh ya kwana biyu? Nina zata kin manta da alkawarin mu shatu, tun inasa rai har na hakura. Muna nan lfy inna, kinsan yanzu yan aikin akwai wahala, saboda sun daina bada ya'yan su saboda wasu dalilai, yanzu hka 'yata na kawo miki dan na lura yanda kike son abokiyar zama. Inna tace kefa kika sani, harma nasa a nemomin cikin 'yan kannen larai, saidai mahaifinsu ne yaki dole na hakura. Ina yarinyar takene? Shatu tamike ta leka waje yarinyar na labe a kofar falon, ke zo ciki mana. Ts juyota, inna ta dubi yarinyar ke 'yar fillo shine kika tsaya awaje, zonan ki zauna. Tana rike da 'yar ledarta a hannunta taje ta zauna inda tagaga an nuna mata. Tunda haj. Fatima tasa ido akan yarinyar taji sonta yakamata, ta dubi shatu amma bazata wuce shekara biyar ba wannan yarinyar? Shatu tace eh ba wuce hakan ba. Toh kince 'yar kice gashi ko kama bakuyi ba shatu?
Gsky ne inna, sunanta Aisha, amma iyayen na kiranta uwani, saboda sunana akasamata 'yar kanina ce, kma marainiya ce, saboda mahainta Dalhatu mahaifanmu daya dashi, nine na raine sakamakon muma iyayen mu sun dade da rasuwa, kma mu kenan suka haifa, tunda suka rasu yadawo zama aguna, dan farautane anan kauyen da nake yana shiga daji.
Ranan ina zaune ya shigo min da yarinya 'yar fulani cewa matarsa ce. Ya bani lbr cewa achan daji ya hadu dasu, mahaifinta ya bashi ita, baima bar garinba saida aka daura musu aure, abun bbu mamaki dan irin hka yasha faruwa, nidai da yake nasan halin Dalhatu yarone mai zuciya da neman na kansa, sannan yana kwatanta gsky a al'amransa, ya nuna minshi kam yana son matarsa, dole na ware musu daki suka fara zama, dayake mijina nada saukin kai da saurin fahimta, bai nuna damuwarsa da hkan ba. Sun sami kamar shekara sannan suka tashi daga gidan, da yake ya gina musu nasu, kuma a lokacin matarsa ta haifi uwani. Ana cikin hka rannan ya shiga daji, sai aka dawo mana dauke da gawarsa, hankalinmu ya tashi sosai hardaini  dashi kadai ne dan uwana, na tayar da hankalina aosai daga baya mukayi tawakkali. Uwani nada shekara uku mahaifiyar ta tasake yin aure, itama cikin data samune ajalinta, dan kwana tayi jini na zuba, gashi dan dake cikinta ya mutu, dan hka batama haifeshi ba, itama tace ga garinku nan. Uwani dama aguna take, saidai bata sakat a gidan, saboda mahaiyar mijina tace bazata zauna gidan danta ba. Dama yaya yake da har zai rike diyan wasu? Talauci ya masa yawa kona shi 'ya'yan ma ya yake ciyar dasu. Nida naso uwani ta zauna dani amma saboda yanda batada 'yanci acikin gdan shiyasa nayi niyar kawo miki ita, inna dan Allah gatanan amana! Haj. Fatima harda kwalla dan irin tausayawa uwani datayi, tayi ajiyar zuciya, tareda gyara zamanta, tace gsky ne insha Allah shatu zan rike uwani amana, inaso ki kwantar da hankalinki Allah ya jikan iyayen mu baki daya. A lokacin indo mai aikin inna tashigo, tana gaida shatu. Inna tace dan Allah indo ki kawo musu abinci suci, kada shatu tayi dare tace a yau zata wuce. Sunci sun sha sunyi hamdala, shatu tace toh uwani ga inna nan kiyi zamanki da inna. Sai kuwa nan ta fashe da kuka tana fadin ita bazata zauna ba.
Da shatu zata tafi har saida itama shatun tayi kukan, da kyar aka rabasu sannan shatu ta wuce jega. Inna kuwa sai hkr takeba uwani, amma uwani kuka take har dare. Ta kuma ki shiga daki tayi zaune abakin kofa. Jafar ne ya shigo, sam hamkalinsa na wani wajen bai lura da mutum ba. Tuntube yayi da har zai fadi yayi saurin kiran sunan Allah "subhanallahi! Baidai fadin ba, amma yaja tsaki "mts! Waye anan wurin? Jikinta na raw tamike tsaye, dan tsabar tsoro dan yanda ya daka mata tsawa, batace komaiba, amma taci gaba da kuka. Ya kara maimaita maganarsa wannan lokacin saida tayi fi tsari don tsabar kaduwa, sai a lokanci haj. Fati ta shigo falon tana fadin jafar bakuwace shigo mana.
Toh shine zata zauna a kofa? Nida kadan na fadi wlh."
yi hakuri ta fada tana kokarin zama tace " yau shatu ta kawomin ita 'yar kaninta ce.
Allah sarki shatu shine bata nemeni ba? Gsky ne a yau kam sauri take dan ta koma jega.
Inna ina wuni? Ya nemi wuri ya zauna, ta amsa masa cike da kulawa. Ya kara kallon bakin kofar falon , yace wai inna wannan yarinyan tsoron falonki takeyine? Ta dubi kofar itama, a'a haushi take shatu ta tafi ta barta, nan dai inna ta kwashe lbrn uwani ta zaiyane masa. Tausaya mata shima yayi, yace................

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now