KALLON KITSE
saida ta gama kukan, sannan ta shiga tayi wanka, ta fito tayi sallar mangariba.
Sunyi shirin barci mami zainab ta shigo dakin ta mikawa uwani waya, a kunya ce ta amsa, saida zainab ta fita sannan ta kara a kunnenta, ta lura a kunne take,
"Hello" ta fada da murya mai sanyi, har ransa yaji muryarta, yana jin yadda tayi maganar....ta tsunka masa tunani da kara cewa "Hello"
yakike? Ya fada da kasaita, bata amsa masa ba "inaso gobe ki shirya mu shiga kaduna.." bata bari ya gama magana ba, tace, nifa ba inda zani wani irin kaduna kuma? Wana sani a garin...
"ke ina wasa dake ko? Ya tambaya, murguda baki tayi saikace yana kallonta,
nagaya miki ki shirya zan shigo gobe mu wuce."
abunda bazaiyu ba kenan." ta fada, da sauri ta kashe wayar, da sauri ta kaiwa zainab wayarta, "har kun gama?
Eh mami mun gama." ta fice cike da kunyarta, tana isa daki tayi zaune tana tunani, hafsat ta matso kusa da ita, "ya akayine 'yar uwa? Hawaye ne ya cika a fuskarta, wai kinji uncle, wai in shirya mutafi kaduna gobe, anya uncle yana da hankali? Hafsat dariya ta saki sosai harda hawaye.
Ita kuma kuka ta saka mata dama tanada niyar yin hakan, dole hafsat ta daina dariyar ta soma lallashi, "ke wasa fa yake miki danya gano weakpint dinki ne shine yake tsokanarki.
"da gaske?
"ni inda uncle yake bala'in burgeni uwani, shi yana bala'in iya soyayya, don Allah fadamin dayake, kissing dinki da dazu me kikaji?
Uwani ta marairaive fuskarta, "haba hafsat wannan shi ake kira soyayya? Na dole fa yayi min, me kike tsammani zanji, tunda baso nakeyi ba.
"keadai fadi gaskiya 'yar uwa." duka ta kai mata ta kauce, nifa bana son wannan hirar, ta kwanta, hafsat ta dameta da surutunta, karshe ta kyaleta.
Washe gari tunda safe jafar ya shigo gidan, ya fadawa zainab bukatarsa nason tafiya da uwani, anya haka zai faru jafaru?
Kai wai miyasa bakada hakuri ne wai?
Haba yaya kinsan fa nayi hakuri, munkai wata kusan takwas fa da aure yaya, kuma ai yaya ba wani abu zanyi mata ba."
"hum dama nasan halinka jafaru, kaifa in kana son abu ka iya naci, toh ai saikayi mata magana inta yadda toh kasan ni ba ruwana, kaida inna ne inta ji labari."
"don Allah kisa baki yaya."
"kwana nawa zata yi?
Kwana uku." ajiyar zuciya tayi, "nidai na fadama babu ruwana idan inna taji."
na yadda yaya yimin magana da ita, inaso mu wuce da wuri, kada rana yayi min, inada evening ne a yau din nan." a kicin ta samesu suna fere dankali, uwani jafar na magana yana falo, dama hijabi ne a jikinta, dan haka ai tsaye falo ta nufa.
Idonsa a kanta, tadan russuna, ucle ina kwana?
"lafiya. Ya fada, kin shirya mu wuce?" yayi saurin tambayarta cike da isa, miyau ta hadiye da sauri, "ina zamu? Ta fadi hakan cike da tashin hankalin.
"bana ce ki shirya kaduna zamu ba? Nan da nan hawaye ya soma zubo mata, uncle kayi hakuri, amma bazani ba wallahi."
"nima kiyi hakuri, amma ina bukatar matata, wai bazaki tausaya minba ne? Kinsan hakkin da ke kanki kuwa?
Kin san irin zunubin da kike kwasa kuwa? (Kuji fa shi bai duba nashi zunubin ba yana duban na wani lolz)
kuka ta keyi sosai, tana magiyar ita bazata ba, data lura hakan bazai fisheta ba, saita ce, "toh da kake fadan wani hakki, ai na sha fada maka, niba zan iya dakaiba kafi karfi na, sannan ai na fada maka bana sonka!"
dariya ya saki, wanda ke cike da nuna kasaita, baki sona? To wa kike so? Da sauri tace "hamza!!.
Waye kuma hamza? Baka sanshiba, amma kowa yasan shi, kuma kowa yasan irin soyayyar da mukeyi dashi."
kina nufi harda auren naki kina tadi da wani? Tambayar ta fado mata a bazata, ta kuma ga bacin ransa a fili, dan haka ta nemi kara masa bacin ran, saita danyi murmushin karfin hali, tana dubansa tace "eh! Mana ai inna tace raba auren nan zatayi." bata ankara ba, saiji tayi ya rike mata bakinta da yatsan sa biyu, dan tsabagen zafi bata san sanda gwiwarta suka kai kasa ba, "ni kike fadawa magana?
Hawaye kawai ke ambaliya a fuskarta, yaci gaba, "na fada miki dole ne ki soni yadda nake sonki, sannan dole ne zama dani, ban hana in na mutu ba, sannan da kike bugun gaba da cewa, inna zata raba aurena dake, hala igiyar a hannunta yake?
Zainab ta shigo falon, tana fadin "subhanallahi jafaru so kake kaji mata ciwo? Wai meyasa kake son gwada mata karfine? Da sauri ya saketa, ita kuma kuka takeyi sosai, nan da nan bakinta yayi sumbul ya kumbura, zainab ta rungumeta, toh gaskiya tunda haka ne, na fasa baka ita, nasan inba ma kusa abunda zakayi mata saiya fi wannan."
"yaya bakiji irin bakaken maganan data ke fadamin bane."
"amma shine zaka ji mata ciwo? Ran mami ya baci, ya lura da hakan, "toh yaya ayi hakuri, amma ai ita taja ma kanta."
haka ma zakace ko? So kake gobe na nemi alfarma gun inna taki kenan ka kyauta" ta riko hannun uwani datayi kuka harta galabaita, zo muje na fasa bada aron naki."
da sauri ya mike daga zaman da yake yi, yaya kada kiyi min haka, kin riga da kinsa min rai."
toh ka cire ran dan ba yadda za ayi in baka ita kaje kaji mata ciwo akan banza, aiyin soja ba hauka bane,
YOU ARE READING
KALLON KITSE
Ficción GeneralKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi