KALLON KITSE PRT (19)
Duk yadda kaga jafar naji da kansa, yana huci kamar kumurci, da yadda baya wasa da yaransa, inya shigo gida dole ya ajiye wannan abu gefe, zama yake tamkar karamin yaro a gaban marliya, idan yadawo aiki na wannan wunin toh bazai fita ba, ko emergency aka kirashi, da yake yana aiki anan 44 dake cikin garin kaduna, wani lokaci kuma suna zuwa jeji training, marliya bata aikin komai a gidan 'yan aiki ne da ita su uku, kowacce da aikin data keyi, sai kuma cook da yake girkin abinci, hatta abinci bataci da kanta indai jafar yana gida, shike bata abaki, toh balle ta dauko masa abinda zaiyi amfani dashi, duk abunda ta keyi, shima baisan dalilin da yake yi mata shiba, amma abun na bala'in damunsa, ba yadda za ayi, kuma ya fadawa wani, a rayuwarsa bai taba tunanin zai bautawa 'ya mace ba, shi abun ma ya daure masa kai, da in ya zauna a office tunani kawai ke damunsa, shi wai meke damunsa ne? Ya tambayi kansa, duk karfin halinsa da kuma jarumtakarsa, amma ace mace ke juya shi, yadda ranta keso, wai meke damunsa, shin wai so haukane? Ya kara tambayar kansa, duk abunda tace baya musawa, sai kace uwarshi, yanzu haka watansa biyar kenan rabonsa da kebbi, kullum saiya ta yiwa inna karya, aiki ne yayi masa yawa, koyayi shirin karya dokar marliya, sai yaji bai iyawa, duk yawanci fadansu bai wuce in yace zaije kebbi ba.
Duk bakar zuciya da aka sanshi dashi, saidai yayiwa na waje, amma badai marliya ba, duk abun duniya ya ishe shi, tun a wannan lokacin shi kanshi yasan ya canza, inya koma gida bayada hutu, shi yasan yana son mata, amma yau yaga wadda ta fishi, domin sai su kwana suna making love da marliya, amma bazai isheta ba,
shi abun har mamaki yake bashi, inda shiba soja bane, da yake cikin excrse ba da tuni ya rube.
Yau ya iso gida gabansa na faduwa, saboda jiya yace da ita a kebbi zaiyi weekend dinsa to batace komaiba, amma ya shirya yadda zai bullowa matsalar, ya shiga falo ya iske an shirya abinci akan tebur, ya duba ko ina amma baiji motsinta ba, daki ya shiga ya sameta kwance, wai batada lafiya, nan da nan hankalinsa ya tashi, ya isa bakin gadon datake kwance, ya tsugunna ya riko hanunta, "ya akayi ne sweety, na dawo kina kwance?
Ta ya tsina fuska tare da ture hanunsa, tun safe nake amai banjin dadin jikina, "dauko min abinci in dan ci." ya mike da sauri ya nufi tebur din abinci,ya febo mata, ga mamakinsa ta cinye shi tas, ta dube shi tace "doctor, dama haka take kiranshi wataran, ya amsa sweety, dubani meke damuna?
Tayi kwance rashe-rashe, ya dan kalli idonta, ba abinda ke damunta, lafiyarta kalau, yayi jim yace, inaga stress ne ke damunki, amma ga fleden kisha, zaki sami sauki."
ta karba ta rike, sai kuma ta wurga masa a jikinsa, tace "bazan shaba, kaje ka hadomin kazar danasa a gasamin tana cikin micro wave".
Ya mike a sanyaye yaje ya dauko, cikin ransa abace yake yayi bakikirin, amma a zahiri fuskarsa babu alamun haka. Saida ya zauna ya bata ta cinye shi tas, sannan tace "ya aza mata ruwa tayi wanka. Daga karshe wankan ma shi yayi mata shi, ya shiryata, sannan ya sami kansa yace, "zaije yayi sallar mangariba".
Yawanci saboda aikinta a gida yake sallah shidda, baya taba barin jam'in sallah ya wuce shi, amma yanzu ya zama gwani.
Abun mamaki sai gashi jafar yayi sallah a kaduna, abunda bai taba faruwa ba komai dare dole ya kasance da inna, tare suke farin cikinsu.
Anyi sallah da kwana salaha ta dira gidan jafar anan kaduna, daga kebbi take, tunda suka iso basuga marliya ba, kuma tana nan aciki, sam salaha batayi mamaki ba, saboda tasan haka zai faru.
Tun a kebbi take shirin abunda zata fadawa jafar na tsiya, amma abun mamaki data ganshi, saita kasa furya koda kalma dayane, yabi ya lalace, kamaninsa duk ya canza ta rasa da wacce kalma zata fara yi masa magana, ya dubeta sosai ya wangale baki, "yaya salaha". Ya karaso yana dariya, yana cikin kaki (kayan sojoji) ya cire hular da yake kansa yana yi mata barka da zuwa.
Da kyar ta maida kwallar dake idonta ta amsa gaisuwarsa, sun danyi hira kadan, yana wasa da fa'iz dan salaha data haifa, inasu faisal, ba a zo dasu bane?.
Ta kalleshi murya shake "jafar baka tambayeni inna ba? Ya danyi shiru bai mata magana ba, amma yasan bazai iyaba, saboda kunyar salaha dayaji, "ai nasan tana nan lafiya yaya".
Tamike toh bari in wuce, dama na biyo ne in gaidaka tunda kai kafi karfin hakan nan da abuja baki da hanci." murmushi yayi kawai, baice komai ba, abun ya daure wa salaha kai, hatta dan barkwancin nan dayake tsakanin su baiyi mata ba, saida suka fita a falon take ce mishi, "anya lafiyarka kalau jafaru? Ya amsa cike da fara'a "llafiya lau yaya, me kika gani hala?. Ta juya kanta menene ma bangani ba, Allah ya sauwake." yana kallo ta wuce bai iya cewa komaiba. Duk cikin zuciyarsa ba dada, yakeji.
Bayan ta wuce ya shigo gidan ya iske marliya tana tsaye, tana shan kamshi, da sauri ya isa gunta yanayi mata magana, "yana ga ranki a bace, me akayi maki sweety?.
Ya rike hanunta ta janye ta nemi wuri ta zauna, ta saki kuka,
YOU ARE READING
KALLON KITSE
Ficción GeneralKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi