14

2.3K 159 0
                                    

KALLON KITSE PRT (14)

ita kuwa tana daki dadi ya cikata, ta saka jallabiya light green da dan karamin hijab dai-dai lokacin da hajiya magajiya ta shigo, tace ya iso dame za a fara?
"haba Ammi ya zaki saka siket? Nace miki fa you have  to look decent, ga hijab din dana karbo nan ki saka.
"kewai meke damunki nagane duk kinbi kin zauce, saboda wannan dan karamin alhakin, kin manta irin sharrin da mukewa maza ne? Komai jin kansu da barazanarsu muna juyasu you dont need to pretend my dear.
"Ammi kinyi alkawarin bani hadin kai, dan haka inaso kiyi abunda nace, saboda wannan gayen is different from others am in love with him.
Ta rike kafadarta "am sorry, zan baki hadin kai marliya, i promise to you.
Tayi ajiyar zuciya tace, thank you,
a lokacin kaninta mansur ya shigo, sister bakonki yana falo.
"yauwa thank you, amma inaso ka kama kanka, banaso ka rinka shishige masa, ka ganeko?
"nawa za a bani in na hada kai daku? Tayi murmushi, "bet me, zaka so tayina, yayi dariya ya fita.
Ta iske shi ya dan kai bayansa a kujerar da yake zaune akai yana danna wayarsa, ta shigo tare da yin sallama, ya amsa ya koma zaune, ta sami wuri ta zauna tareda gaisheshi, yaji dasin yanda take kama kanta, sai yaji tana kara shiga ransa, ya amsa tareda da ajiye wayarsa kan centre table, "ya akayi aka bari na shigo cikin gida bayan baki fadiba?
Tadanyi jim kadan sannan tace, nima ban saniba, yayi murmushinsa mai kashe 'yan mata yace, "toh kefa a gaskiy narasa dalili jiya na hadu dake amma harda kasa barci a daren jiya. Ina sonki marliya, kuma dan Allah ba maganar wata wasa ta kawoni ba.
Ta muskuta kadan tace bakomai Allah yasa mudai-daita.
Ya amsa mata, tamike, "ina zuwa.
Kayan ciye-ciye takawo masa, ba abunda baici ba, yanaci suna tba hira, ko ince ma shiyaketa zuba duminsa, ita kuwa daga eh sai a'a, haka hirar tasu taci gaba, sun sami kamar awa daya, sannan tace bari in kira Ammi ku gaisa.
Ta fita, yabita da kallo, yarinyar ta hade dayawa a idonsa, yana mamakin yanda son yarinyar yayi yawa atare dashi.
Haj. Magajiya ce tayi sallama, da sauri ya koma kasa, ta nemi wuri can nesa dashi tace, "Dan nan ya kake?. Ya sunkuyar da kansa kasa sosai yana gaidata.
Bayan sun gama tace jafar kake dan nan?
"eh hakane Ammi. Tace "toh ga dai marliya nan, amma sai ahankali, kasan yara, nidai kam ban taba haduwa dakaiba, amma sainaji ka kwanta min, da alama kai dan mutunci ne,kanada decipline dan haka na baka amanar marliya, tun daga yau, bata sauraran samari amma kai nayi mamakin da har ta kawoka gidan nan, dan haka arike amana.
"nagode, nagode Ammi, kuma zan rike amana, Allah yasaka da alkhairi, tamike ta fita, ya kallo marliya yace, toh ke kinji Ammi ta bani ke, har abada its means in fara shirye-shiryen aure kenan?.
Tayi masa kallon datasan zataja ra'ayinsa tace, in ni na amince kenan ko?
"toh nidai Ammi ta bani ke, dan haka nasan banida matsala.
Haka dinne kuwa, bai samu matsala ba, dan cikin wata biyu suka kamashi a hannu, zan iya cewa tun daga lokacin cinsu da shansu ya koma hannunsa, ko a labari yaji tana son abu toh gobe zai kaimata shi, cinsa da shansa ya koma gidan, dan a kullum sai yaje gidan sau uku, acan yake karin kumallo wanda akasa asirai kwamacala iri-iri yaci shi, duk da baya jin dadin abincin haka yake daurewa yaci, ya rinkayin kamar baitaba cin irin wannan abincin ba. Can kuwa wasu kyama ma suke bashi, acikin wata ukune da haduwarsu yaje ya fadawa inna, ai kuwa bayan komawarsa da sati biyu akaje tambaya, abun mamaki su baba yunusa da kawu hashimu da wani Alh. Sabi'u limamin masallacin baba yunusa, sukaje neman aure yadda sukaga irin tarbar da akayi musu shiya fara daure musu kai, wani matashine ya amshesu da ganinsa bai wuce warin jafar din ba, sannan ko ruwa saida suka roka, sannan aka basu, abun mamaki shima ruwan a kananan kofi, abunda suka lura dashi, jafar baima damu da abunda ke faruwa ba, baba yunusa yace sunaso su biya kudin komai a yau, harda sadaki saboda gari da nisa, kawu hashimu yace, inma da dama sai asa rana.
Saurayin yace angama duk abunda aka shirya dai-dai ne, saboda shima yafi so next month a daura auren in sun shirya.
Eh kam mu a shirye  muke, sai ayi wami watan, sha shida ga watan dan yakama ranar asabar kenan,
yayi dai-dai dasai mata sun kawo lehe.
An yake sadaki akan nauyin gold, waisu da gold suke sadaki, dan haka saida  aka zabo gold dankarere na kusan dubu dari uku da hamsin, harda 'yan canji akai.
Ya biya kudin shiga gida dubu dari da hamsin, sannan su dabino dasu sweet duk aka hada aka kai musu,
washe gari da zasu tafi baba yunusa duk jikinsa yayi sanyi saboda tausayin jafaryasan ba karamin rayuwa ya shiga ba......"

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now