KALLON KITSE PRT (20)
Ta saki kuka, "don me yayarka zata shigo min gida batare da tanemi izini naba? Kuma data shigo ko kallon arziki batayi minba, saima ta rinka yimin kallon da baimin dadi ba, saboda Allah wannan wane irin wulakanci ne, kaima daka dawo ko ka kula da hakan?
Duk ilahirin jikinsa rawa yakeyi, shima kaman yasa kuka yakeji, yayi sauri ya rungumeta yana bata hakuri, da kyar ya samu tayi shiru, harda su ajiyar zuciya.
Ya dauketa cak, sai cikin daki, anan ya nuna mata tafisu 'yanci a idonsa, don saida ya tabbatar ta sauka, ya kyaleta, sannan yace ta kwantar da hankalinta, badai sune bata so ba, zamu zuba dasu.
Ta kalleshi a kadarance tace, meya kawota?
Ya tsura mata ido, bakomai wai tazone kawai mugaisa,
"ta dai zo ganin gulma, kaga daga yau banason ganin irin wadannan bakin, don basuda mutunci, ka gane ko? Ya hadiye miyau da karfi yace badamuwa zan kula, sannan suka ci gaba da soyayya.
Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, yau gashi jafar yakai kusan shekara biyu baije gida ba, koma ince ya manta dasu ko waya bayayi musu, tun abun na damunsa har ya hakura dan kansa. Ita kuwa uwar mulki ta samu yadda takeso, duk salary na jafar hanunta yake, ko kwandala baya karba, haka zata shirya itada mahaifiyar suje kasashe-kasashe abun ba a cewa komai, domin kuwa tayi nisa sosai, har lokacin da aka tura shi course lagos na watanni da dama itace ke ai watar da koma.
A taikace de bada shi kadai take harka ba, ba yanda bayyi da itaba su tafi lagos tare, taki tace, bakomai zata ringa kai masa ganinsa akai-akai, nan kuwa shirya masa karya tayi.
Ya samu kaman wata shida da tafiya su baba yunusa da kawu hashimu suka zo kaduna.
Marliya ba wulakancin da batayi masu ba, harda korarsu tayi tana fadin, "shin wai ku wasu irin mayu ne, ba yace baya yi dakuba, ko kun mata da nasa ya fada maku ku fita harkarsa?.
Kawu hashimu yace ke tsohuwar daga kiyi hankali......." baba yunusa ya dakatar dashi da hannunsa, "kyaleta lokacinta ne zomu tafi."
suka kama hanya suka tafi dan takaici basu saurara ba, suka wuce gusau gidan zainab, daga sama ta gansu itama, yadda ta gansu a zatatonta rasuwa akayi, ta kasa tsaida hankalin gu daya, ta shirya masu abinci, data ga basu damu su gaya mata wani abu ba yasa ta nutsu. Saida suka ci suka sha, sannan suka fita yin sallar isha'i bayan sun dawo suna tare da Alh. Tanimu ambursa, zainab ta shigo ta nemi wuri ta zauna, "baba ya bayan rabuwa?, ya amsa lafiya lau kinsan daga kaduna muke, dan mu duba jafar? Amma matar nan tashi ba karamar 'yar duniya bace, ashe haka take muna jin labarinta, muna ganin kamar ba gaskiya bane, ashe ta wuce yadda muke zato? Bakisan korar kare tayi manaba? Zainab ta zaro ido "hardaku tayiwa wulakanci baba?.
Ajiyar zuciya yayi, "aiba abunda za a tashi dashi, in banda atashi tsaye da rokon Allah, wane a sa ido duk bata taso ba.
Fatima ta maida abun abin fushi, aiba fushi ya kamata tayi ba, addu'a za a tashi arinkayi, shekara cikin na uku kenan fa, rabon jafar da kebbi, in muka sa ido bamu san ciwon kanmu ba, shifa mutum ajizine bai taba cika cikakken mutum ba, kawu hashimu yace, zainab don Allah kiyi addu'a Allah ya dawo da yaron nan gida, wallahi ya shiga abunda bakwa tsammani ba." hawaye ne tab da idonta, tace baba dan Allah kubawa inna hakuri ta dauki zafi sosai, dan inaga akwai lokacin da inya bugo ma ta daina dauka, saboda haka shima ya bari, sannan salaha ma ta fadamin abunda ya faru kwanakin baya dataje kaduna."
baba yunusa ya gyara zama, "ke bakiga auren mansura bai zoba ai abun ya wuce gona da iri, dan haka bazamu sa ido ba, dole mutashi tsaye."
"hakane baba Allah ya taimake mu".
"amin".
"gashi arziki sai karuwa yakeyi, kinga gidan da dama yake zaune aciki, ance nasane, gashi bai samu matar kwarai ba, shin waye mai dukiyar in yau akace babu shi? Dan haka dole mutashi tsaye, nikam yunusa wallahi sai nayi sanadin rabuwarsa da wannan ja'irar mace, insha Allahu ko nanda shekara goma, sainaga bayanta, Allah dai yayi mu rayu zata ga abunda ta manta dashi."
ahaka sukaita shirye-shiryensu, tare da tunanin yadda zasuyi, abun bakaramin daure masu kai yayi ba, "jafar da yake son jama'a, ga zuciyar kyauta kowa yasan yaro mai tarbiyane, tunda ansan hakan ya za a samasa ido, mun cutar da kanmu da kanmu, Allah zai taimakemu insha Allahu!!
**** **** **** ****
tunda jafar ya bar kebbi haka inna kuwa batada kwanciyar hankali, saidai sam bata nunawa, tasan tayi kewar autanta, amma ya zatayi? Tunda ta aza ido kan matarsa, tasan ba abun kwarai bace, tun kuma daga lokacin tai mafarkin ta, da wata irin muguwar shiga, so daga nan saita ga marliya ta nufota da wuka, ko almakashi ta biyota, acikin mafarkin Allah ke bata ikon yin addu'a, saita bace. Wata rana kuma tayi mafarkin ta cakumota zata jefa cikin wani irin rami mai bala'in zurfi, duk da iri mafarkeyen data keyi bata taba fadawa kowa ba, itama kanta abun ya daure mata kai.
YOU ARE READING
KALLON KITSE
Ficção GeralKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi