KALLON KITSE prt
28Basan yadda akayi na aureta ba, amma ni nasan ko kusa bazan taba tunanin aurenta ba, kuma haka dinne, na fara samun wani irin yanayi ne a tareda ni, kasan fa yanzu kusan ince nayi shekara hudu rabona da kebbi.."
"akan wane dalili jafar?
"wallahi ban saniba aboki, haka kawai, ni nasan tun ba yanzu ba, abun na damuna, amma ban iya fadawa kowa matsalata."
"haba aboki meyasa kayi haka?
Wallahi bashir in nace ma ga abunda ke damuna toh wallahi nayi maka karya, dan labarin dana baka kan marliya wanda na sani kenan. Dan Allah bashir ka taimakeni domin ganinka yasa naga kamar matsalata ta kare."
zan taimaka maka aboki, nima abunda ya shafeka ai ya shafeni aboki, dan haka shawarar da zan baka itace, zamuje wajen yayyenka mata mu fara dasu tukunna, koya ka gani? Hawaye ne suka taru cikin idonsa, amma basu zubo ba.
Nagode aboki, inasa ran zan samu leave din ranar jumma'a in Allah ya kaimu, ya zakaje ne kashirya?
Eh toh nima anyimin transfer nan garin, gobe zan shigo da iyalaina, kasan yanzu 'ya'yana biyu ko?
"kai dan Allah bashir?
"na uku ma na ciki insha Allahu next month zata haifeshi."
nima gaskiya irin naka zanyi, ta gida zan nema in aura."
da kaga canji, dan dai nikam amina ta gama min komai, dan sanadinta na zama abunda na zama yanzu, saboda cikin dari ita keda tamanin, na ci gaban rayuwata."
"hakane bashir, Allah nima ya bani wadda zata rikeni amana."
toh marliy fa? Ai baka rabu da itaba." hakane, bazan rabu da itaba har sai na gano yadda ta maidamin rayuwata ta zama haka, sannan saina rama wulakancin datayi min, bashir Allah ne kawai ya cetoni daga tsohuwar kilaki, Allah ya rabamu da irin wadanan matan amin."
"sai musa ranar tafiya, ranar lahadi kenan next weak a lokacin munga zainab da salaha ko?
Badamuwa duk yadda kayi bashir shine dai-dai."
washe gari bashir saida ya matsawa jafar, har saida yasa yaje yayi belling din marliya, ta dawo gida sannan ya wuce lagos yace, da yamma zasu shigo kaduna. Haka akayi kuwa, karfe bakwai saura, jafar ya taryesu a airport, gidan da akabawa bashir babu abunda babu aciki, gidane babba hawa daya, jafar ya siyo musu abinci suka ci, abun sha'awa ya rika bashi, yaran bashir duk sun taru a jikinsa suna wasa, ji yake da shima yayi auren kwarai daya ajiye iyali irin haka.
Haka yai ta sha'awarsu, har sai karfe tara da rabi yabar gidan bashir mashayarsa ya wuce, ranar ma abun har yafi na kullum, dan daki ya dauka, yana holewa da 'yan mata, in wannan ta shigo wannan ta fice waccan ta shigo, Allah ya shirya amin.***** **** *****
can birnin kebbi kam, abubuwa suna tafiya dai-dai, sai dai na inna ba haka bane, duk kwanan nan saita tai ta mafarkin jafar, ta kasa fadawa kowa, saidai inta tashi tayi sadaka, tana rokon ALLAH yasa bawani mugun abu zai sameshi ba.
Suna zaune a falo ita da uwani, uwani 'yar shagwaba, kanta na kan cinyar inna, sai sallama sukaji daga sama, muryar tayi musu wal,
YOU ARE READING
KALLON KITSE
Fiksi UmumKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi