KALLON KITSE
da sauri jafar ya isa inda take zaune, idonsa jajir, haba inna meyasa don Allah ki fadamin, dalili da yasa kike kyamata, wallahi ni mai gyaruwa ne, inna ki taimaka min,
tsakanin da da mahaifi sai Allah, inna taji tausayinsa sosai aranta
amma bazata iya yin abunda ya bukata ba, ta kauda fuskarta gefe, sam bata sauko ba, tace jafaru inkana so mu zauna lafiya dakai, ka maida wannan maganar dan bazai yiyu ba, bazan iya ba, kana jina?
Ta mike zata wuce, Alh. Yunusa yace, fati dan girman Allah ki sauko, wai me kike nufi da jafaru ne? Ki tuna duk dan Adam fa ajizine, bai taba cika goma ba.
Ta kalli Alh. Yunusa tace, "lallai na yarda da maganarka, amma bazan iyaba namijin da mace daya tak ta juya masa rayuwa ba, dan haka ni na gama nawa, kaga babban yusrah ina ganin girmanka, amma wallahi bazan iya yarda da wannan abunba, don Allah adaina." fuuu! Ta wuce daki ta kulle.
"lallai maganar da inna ta fada gaskiya ne." Alh. Yunusa ya fadi hakan a zuciyarsa, toh ammma.....
Sai kuma ya mike tsaye, jafaru da sauri shima ya mike yabi bayan baba yunusa, idon nan nasa kamar zasu fado, don bacin rai.
Su kuwa su zainab duk jikinsu yayi sanyi, sam basa son yadda inna ta dauki zafi akan dan uwansu, ya kamata tayi hakuri haka.
Su kam su uwani suna wurin indo basu san abunda ke faruwa ba, tsokanar hafsat sukeyi, wai saurayinta kato ne, hafsat tace, eh nayarda kato ne ku ina naku samarin? Yauwa uwani ina saurayin nan naki wan kawarki lawisa?
Uwani tayi murmushi sosai tace, hamza? Yana nan wallahi, eh toh bana musaba gaskiya kika fadi, dan hamza ya mallaki abunda nakeso a da namiji, ada banyi tsammanin So wani abu bane, amma akan hamza na gano so wani abu ne, da bazaka san sanda zai shigeka ba." hafsat tace, 'yar uwa nima haka ta sameni, dan haka nasan abunda kike nufi.
Fa'iza kallonsu takeyi, ita dai bata fada wannan tarkon ba, dan haka saurare takeyi, a haka suka cigaba da hirarsu ta 'yan uwa.
Jafaru zaune a dakinsa ya rasa abunda keyi masa dadi, dan me inna bazata amince da hakan ba, abunda bashir ya fada masa gaskiyane, inna bazata bawa wanda bataso uwani ba, gashi danta na cikinta bata amince masa ba, toh wa zata amincewa? Ya tambayi kansa, tare da kai kofin barasa bakinsa,ga kuma taba a dayar hannunsa na hagu, kulle kansa yayi a dakinsa, tunani bawanda baiyiba ahaka ya kwana ranar ko abincin kwari baici ba.
Ansamu kamar kwana uku da wannan maganar sannan ana bawa inna hakuri, amma sam taki, harda kawunsu yazo, musamman saboda maganar wato Alh. Hashimu, amma taki saurarensu, har gori take musu akan jafaru, ya maida su abokan wasan sa, duk ya dauko gantalin tunaninsa sai yaje ya dauko su, yadda suke tsammanin abun zai zo da sauki sam abun ba haka bane, dan har ta kai a yanzu inna bata amsa gaisuwar jafaru, abun ba karamin tada hankalinsa yayi ba, ya rasa abunda keyi masa dadi arayuwarsa, wai ya zaiyine? Ya tambayi kansa, wata dabara ta fado masa, dan haka shiryawa yayi, tunda safe ya tafi jega gun shatu, tana zaune bakin murhu, tana soya kosai abincin karinsu, taji sallama, ta amsa da sauri tana zuba ido, dan ta gane mai muryar. Ta kwallawa danta hafiz kira, shine na biyu, a tsakar gida akayi masa shimfida ya zauna, shatu tasa aka kawo masa kari.
Dakyar yake cin abunda ke gabansa, ba wai kyama yakeyi ba, a'a. Shatu nada bala'in tsabta duk da bakomai gareta ba, amma tanada wafatar zuci, dan bata taba rokonka abunka, indai ka bata zata karba, amma bazata roka ba, ko wani wata inna na hado mata goma na arziki, dan haka tsakaninta da inna sai addu' bayan ya gama itama ta sami wuri ta zauna gefen sa, suna kara gaisawa, ita tasan akwai abinda ke faruwa dan jagaru yazo nan jega da ya dawo gari, amma ba haka yake zuwa mata ba, daka ganshi zaka karanci akwai abunda ke damunsa.
Tace, ina fata su inna duk lafiya suke jafaru? Tayi tambayar ne cike da zakwadin jin abunda zai fada.
Kansa akasa yace, kowa lafiya lau shatu, nine dai banda lafiya." tayi ajiyar zuciya, "jafaru meke damunka? ya dago idonsa da yayi jajir yace, "inaso ki taimakeni, inna bata sona shatu, dan Allah kije ki bata hakuri, ta tsaneni, bata kaunata da rahamar duniya, toh ballantana na lahira.
Shatu ta kara numfasawa, "me yayi zafi haka jafaru, har kake furta wadannab kalaman da babu dadin ji? Lebensa ya ciza kafin yayi magana, "shatu tunda na shigo garin nan naku inna taki sakin jiki dani, nasan nayi laifi, amma nagane kuskurena, da har inaso in kulla abunda ina tunani bazisa nasake afkawa ga kuskuren danayi ba, amma sam inna tayi fir! Taki yarda, toh a lokacin nasan lallai inba haka nayi ba, toh rahamar duniya ko na can lahira bazata sameni ba, dan inna har yanzu tana fushi dani, bata yafemin ba shatu, ki taimakeni, ki tayani bata hakuri dan girman Allah shatu.
Duk karfin halin jafar saida kwalla ya fito masa a ido daya, yayi saurin gogewa, yana sauraren abunda shatu ke fada masa.

YOU ARE READING
KALLON KITSE
General FictionKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi