KALLON KITSE
karka damu jafar insha Allahu zan sami inna muyi magana, amma wannan abu bakaramin bani mamaki yayi ba, koda yake nasan inna da fushi, in abu yafice mata, toh yana da wahala ta karasa kanta aciki, toh amma inbanda inna harda danta na cikinta bazata raga masa ba? Toh Alla ya sawake, kabari insha Allahu gobe zan shigo kebbi..." bata karasa maganar ba ya dakatar da ita, "nifa shatu gaskiya tare zamu tafi, bazan bar garin nan ba saida ke."
yau naji ikon Allah jafaru har yanzu kana nanda rigimarka da naci, dama asali haka kake da nacin tsiya kamar.....
Lokacin mal. Tasi'u ya shigo, cike da fara'a, a'a mutanen kebbi ne, lale marhabun, saukar yaushe dan nan sammako akayi haka? Ya sami wuri tare da mikawa jafaru hannu, sukayi musabaha. Bayan sun gaisa shatu tayi masa bayani tiryan-tiryan abunda ke faruwa, ta kara da cewa kasan jafaru da kafewa, nace ya bari har gobe inje, yace ba inda zashi saida ni."
mal. Tasi'u yace "gaskiya wannan zancen babba ne, gara ki shirya kije, ko gobe ne saiki dawo babu damuwa.
Atake jafar ya soma godiya, mal. Tasi'u yace haba jafaru kaifa nawa ne, jinka nake tamkar wanda na haifa, dan haka dole in take maka baya, na goya bayanka dari bisa dari, dan haka taje a gani ko za a dace."
tun a washe gari uwani taji wannan labarin, daga ita har inna babu mai samun barcin kirki, dan yadda uwani ta tada hankalinta sosai ko bacci batayi ba, dan haka inna ta dauki alwashi baza ayi auren nan ba, tunda itama uwani bata so, dan haka kullum tana cikin lallashi.
Ranar lajadi su hafsat suka wuce gusau tare da haj. Salaha, daga can zasu wuce abuja, amma sai sun kwana anab gusau, suma sun bada hakuri sam inna tayi jan ido taki saurarensu, har cemusu takeyi basajin tausayinta, dan idan sunji da basu bi bayan dan uwan nasu ba, insun manta ta tuna musu irin bakin cikin da ya cusa musu, da dai suka ga abun 'yar tone-tone ce
dole suka kyaleta.
Da karfe sha biyu da kwata saiga shatu da jafar sun shigo falo, suna kwalla sallama.
Inna da take ciki ta amsa, da yake indo ta fita, ita kuwa 'yar lelen tana daki kwance, bazatayi aiki ba, dan an bata mata rai.
Inna ta shigo falon ba tareda ta saki fuskar ta ba, ta zauna suna gaisawa da shatu, jafar ya gaidata shima, harara ta wurga masa, dayasa jikinsa yayi sanyi sanyi, ya kumayi saurin sa kansa kasa. Shatu tace, inna gunki nazo akan maganar dana, me yayi zafi haka inna? Don Allah kiyi hakuri, laifi fa kowa nayinsa, babu mahalunkin duniya da baya laifi, yo ko Allah munyi masa ya yafe mana, balle mu?
Inna don son annabin rahama, saboda Allah kiyi hakuri." inna ta dubi shatu tace, "kingama? Shatu tace haba inna bansanki da zuciya irin hakaba, kiyi hakuri,"
inna ta dubeta, "gaskiya shatu saidai inki na son ki nuna min a yau ba nina haifi uwani.... ." da sauri shatu ta karbe maganar "haba inna...haba inna ya zaki fadi haka? Ni wallahi har a zuciya ta bantaba sawa raina hakaba." inna itama tayi sauri ta karbe maganar
toh dan darajar Allah da hasken annabi ki fita harkan nan, yaron nan so yake ya hadani daku, amma idan kukayi tunani sam uwani batayi dacen miji ba...." (nima dai nace uwani batayi dacen miji ba lolz) fuuuu! Jafar ya mike ya fita yana huci, duk ya canza kamanninsa, dan tsananin bacin rai, shatu ta kara narkewa inna tana bata hakuri, amma sam inna taki amincewa, saita dauko wani zancen, sunayi.
Can uwani ta fito falon, tanayiwa shatu sannu da zuwa, "ke kuwa meya sameki, duk kinbi kin rame, ko bakida lafiya ne? Inna tace lafiyar ta kalau, saidai ko ku kukeso ku saka mata ciwon, bata son jafaru, kuna nema ku takurawa yarinya, nikuma bazan takura mata ba, dan ba dole." shatu gyara zama tayi, "Allah sarki yarinta, uwani kin iya karfin hali, kiri-kiri ki nuna baki son jinin inna, dan Adam butulu ne,...." inna ta katse ta, "ni batayi min butulci ba, dan dana nuna inason auren nan uwani bazata bani kunya ba, amma da yake ita bamai son bacin raina ba ce, dan haka bazata yiba. Kuma baza ayinba.
Uwani kam wani sabon kuka ta shigayi, shatu ta yamutsar da fuskarta tace, "iye samun wuri, wallahi yarinyar nan dadine ya miki yawa, lallai kin iya zaman duniya, amma kin bani mamaki, uwani kuma kin bani kunya.... ."
a'a nidai nidai na baki kunya ba itaba, dan dai nice nace baza ayiba
dan Allah shatu ki daina...kinfa fara bata min rai, haka kawai zaki sata gaba dan ita bata da gata, ko shi jafaru shine dan gata? Toh wallahi ba wanda ya isa yasamu dole akan wannan al'amarin.
Shima kuma ya dawo ya sameni, inji dalilinsa na gayyato min mutane kan maganar da bata gaskiya ba."
washe gari aka nemi jafaru can kaduna, don wani course daya nema abashi, ya samu, dan haka zai daga hutunsa, har sai lokacin da ya gama course din, ya sami baba yunusa ya fada masa, banu damuwa jafaru insha Allahu za a dace, kada ka damu kanka, insha Allahu uwani takace, sannan inaso kasani matar mutum kabarinsa, indai matarka ce dole ka aureta.
Haka dai yata bashi magana, ya tambayeshi ko wata nawa zaiyi, "wata tara ne baba, can kasar somalia ne,
YOU ARE READING
KALLON KITSE
General FictionKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi