21

2.3K 158 0
                                    

KALLON KITSE PRT (21)

itama kanta abun yana daure mata kai, toh ya ya haka? Ita da ko mainene zai tada mata hankali bata shiru, saita gayawa 'ya'yanta, saboda sune abokan shawaranta, amma ikon allah har yau dasuka samu kamar shekara uku da dan autanta, bata taba kiran wani ta fada masa tashin hankalin datake ciki ba.
Su zainab sune suka damu, inma sunyi mata magana, saita canza zuwa wani tadin, abun yana daure mata kai, sam! Inna bata so ayi hirar jafar, duk da bata nuna fushinta a fili, su sun san tana cike da son fada mata wani abu, amma ta kasa, saita kirata a daki, zata ce mata wani abu, sai kuma kaji tace, barshi kawai, sai kuma ta dauko wani zancen ta rinka yi mata, tun uwani na damuwa har ta saba, dukda basa shiri da jafar itama abun ya dameta, dan dai duk abunda ya zama na inna, toh itama natane.
Uwani na zaune kicin tana yanka alayyahu taji sallamar su kawu, ta mike da sauri ta isa gun, tana gaishesu, suka amsa cike da fara'a,
baba yunusa yace, "toh ina uwr taki takene? Tayi murmushi da har hakoranta suka bayyana, tace, tadan fita amma bazata...." adai-dai lokacin sukaji sallamarta, ta shigo, ta isa cike da fara'a, suna gaisawa ta sami wuri ta zauna, "uwani kawo musu abinci, ko baki gama ba?. Tace "eh inna ban gamaba, amma saura kadan yayi."
toh shikenan.
Ta maida kanta kansu baba yunusa suna kara gaisawa, yo ke fatima babbar magana ce ta kawomu kan yaron nan ne jafaru, mun lura sam ba abunda ya dameki da lalurar data sameshi, amma kisani duk wani fushi da dauke kai kan al'amarinsa duk bata tasoba, mudai hakuri muke badawa, kiyi hakuri ki rinka yin addu'a."
gani yaya ta fadi kwance, nan da nan suka zuba salati, suna kiran sunanta, aikuwa nan da nan hankali ya tashi, suna kwallawa uwani kira ta kawo ruwa, irin kiran da sukeyi mata, shiyasa ta nufo dakin, dauke da ruwa a cup da gudu, indo ma da gudu ta nufo dakin, aikuwa ganin inna a kasa yasa uwani fashewa da kuka, ta karasa ta maida kanta kan cinyarta, tana fadin "inna dan Allah kada kimin haka.
Inna kece uwata, kece ubana, in kika barni na shiga uku! Dan Allah inna ki tashi inna."
indo ma kuka ta fara, dan tsabar tausayin abinda uwani ke fadi, koba komai itama haka ta dauki inna, ta dauketa tamkar uwa data haifeta, nan da nan ta farka.
Hawayene ke zuba sharara daga fuskar inna, bata iya cewa komai ba, asibiti aka nufa da ita.
Nan da nan aka bata gado, duk iya bincike da akayi ba a gane komaiba, dan ba abunda ke damunta, lafiya lau take. Uwani ta kara rudewa, saika ce itace batada lafiyar, duk tabi ta rame cikin kwana hudu. Inna kuwa ita kadai tasan abunda takeji ajikinta, tana tunanin meyasa da anzo anyi mata maganar jafar saitaji batada lafiya? Sam bataso taji an ambaci sunansa, dan da anyi hakan duk saitaji ba dadi, kuma bata isa ta fadawa wani matsalarta ba, wannan abun yana daure mata kai.
A ran kwana na biyar baba yunusa yace, a maida ita gida, su zainab ma a yau suka iso, itada salaha, duk an hadu a falo ana shirin yadda za ayi, kawu yace ayima mal. Kasimu magana yana kan hanyar zuwa, sannan nasa wasu malamai kamar mutum uku anayin rokon Allah." baba yunusa shima ya gyara murya, nima nasa anan mutum biyu da mal. Isa shima yana nan yana yin nasa kokarin, Allah ya bata lafiya."
"amin".
Zainab ta dubi baba yunusa, "baban mariya ma yace, yayi wasu malamai a can zamfara,
toh angode, Allah bada lada." saida mal. Kasimu yazo, aka isa dashi cikin gida, sannan akayi masa iso gun inna, tana kwance, uwani na gefenta rike da hannunta, ba yadda ba ayida uwani ba ta fita amma taki.
Mal. Kasimu yace, "a kyaleta ba abunda zai sameta." nan suka zauna gaban inna shida almajiransa, akasa radio ana karatun Alkur'ani mai girma, suma karatuna sukeyi,
can uwani taji inna ta saki hannayenta ta dubi idanun inna taga sunyi jajir, kamar garwashi, ai saita mike da sauri, tayi waje,
nan fa su mal. Kasimu suka ci gaba da karatu, ita kuwa inna sai wani irin ihu takeyi, kamar makoshinta zai fita. Sun sami kamr minti sha biyar kafin ta soma magana. "wai me kuke nufi? In fita daga jikinta? Toh bazan fita ba, sai kun gaji kun kyaleni, kuda kanku." basu daina karatun ba taci gaba da ihu, can saita fadi kwance, ta kuma tashi zaune, yanayinta gaba ki daya ya canza, idon nan nata kamae gauta, ta mike tsaye tana fizge-fizge, waje tayi, wani almajirin ya rikota, ji sukayi tayi wurgi dashi, kamar kayan sawa.
Nan da nan suka taru a kanta, amma basu daina karatun ba,
mal. Kasimu yace waye kai, bakace bazaka fita ba? Toh ina zaka? Wallahi saina konaka daga sama har kasa, zaka sanni, ayar kur'ani nake amfani da ita, dole ka fita komai karfinka." aikuwa watsi tayi da almajiran baki dayansu, ta nufoshi,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now