4

4.2K 243 0
                                    

KALLON KITSE PRT>>>>>>> (4)

yace na gode inna, ki tayamu addu'a muma abun na damunmu. Tace toh Allah ya shirye ku da dukkan musilmin (ameen). Su duka suka amsa, maza ka tashi kaje kayi wanka, duk warin mota kakeyi, ya mike yana sosa keyarsa.
Haka rayuwa taci gaba, gashi har yakai shekara biyar a karatunsa.
***** **** ***** ****
washe gari saida inna taje kasuwa tasaiwa uwani sabbin kaya na kanti, kala bakwai, sai silippers. Tasa indo ta tsefe mata kanta. Indo tsab ta kwance kan, ta wanke shi tas, nan danan ta canza, tayi kyau, inna tace toh ko kefa, duba kiga yarinya da sha'awarta, amma sam bata samu kula ba, zo uwani inji inna, ta kalli inna ta tako inda take, ta rike hannunta tace kina zuwa makaranta kuwa? Uwani tace a'a.
Toh islamiya fa? Ta karace a'a muna zuwa na allo.
Ok wace sura kike a makarantar allon?
Kulhuwallahu. Tace toh yayi kyau.
A lokacin jafar ya shigo ya zauna ya dubi inna ya gaidata da kwana, wai yaushe zaka koma makarantar ne? Yace ai sai next weeak.
Ok zamu shiga insha Allahu, toh dama so nake anema wa uwani makaranta nan kusa damu, ya dubi Aisha wanda tun shigowarsa ta nutsu, tun jiya ta gane shiba na wasa bane.
Toh basai asata makarantar nan ta high standard ba, kin san inna tanada kyau.
Eh gaskiya ne, sai kaje ka bincika, dama a yanzu first term ake dauka kafin ayi nisa.
Da yamma likis ya dawo ya shigo, ya iske uwani batada riga, daga iita sai dan wando, yayi mata tsawa ke ina rigar ki? Jikinta na rawa ta shige daki da gudun ta, sai bayan dake kwance, ta mike zaune kedawa uwani? Ta nuna bakin kofa. Inna itama kofar take kallo. Jafar ya shigo ciki yana magana, in nasake ganinki baki da riga saina dokeki, yarinya sai kazanta, saikace wata....., inna ta kaste shi "wai kai dan Allah meya dameka da ita? Sam ka hana yarinya sakat, saboda me? To bara kaji gaskiya kada ka takura mata. Yana zaune yana aikin hararar uwani, ita kuma tayi kamar bata wurin dan inna rungumeta tayi akafarta. Ya batun makarantar ka nemo?
Eh na nema, har na na biya kudin makarantar, gobe zan kaita insha Allahu.
Toh an gode Allah shiyi albarka, uwani maza kira min indo ta kawo masa abinci, ta kama hanya da gudunta, ta fice daga falon.
Tun daga ranar ta fara zuwa makaranta, ansata nusery one, cikin satin da kyar take barin inna saboda kukan, ta ba zataba, saida jafar yayi da gaske, dan ranar saida ya doketa, inna kuma in banda fada ba abunda takeyi, tace ma bazata ba, saida indo tasa baki. Inna ta maida indo abokiyar shawaranta, saboda ta fahimci indo mutum ce mai rike alkawari, kuma ba munafuka bace, sun sami kusan shekaru shidda tare, amma sam basu taba samun sabani ba a tsakanin su, a ko da yaushe indo tana gudun zuciyar inna, shiyasa suke zaman lafiya.
Jafar ya koma makaranta don haka yasa uwani keyin abunda taga dama, musamman inna ta dauki direba yana kai uwani makarantar boko da islamiya. Yadda uwani ta zmz yar gata gun inna yasa yarinyar har shagwaba ba wanda batayi, bazaka taba cewa bata da jini da inna ba, da yake inna ta dauketa tamkar yadda ta dauki jikokinta, harma ta hadasu da sauran 'ya'yanta, dan in sunyi waya idan tana kusa saita bata su gaisa. Har suma suna tambayarta in suna magana.
Abunka da mai jiki mai saurin girma, nan da nan cikin 'yan kwanaki uwani ta warware, tayi kibanta gata bul-bul gwanin sha'awa, gata da saurin shiga rai, saboda suffanta irin ta larabawa ce, duk da ita ba fara bace, wakan tarwada ce, amma msi haske, ga gashi irin mai murdewan ga cika, saidai uwani bata son abinda ya taba mata kai, kullum sai sunyi da gaske, za'ayi mata kitso. Inna dole ta rinka sa indo tana lallaba mata kan, shima sama-sama, dan haka ne kullum zaka ga kan a yakuce, sam inna bataso taji kukan uwani ko akan menene, uwani gata da surutu kamar me, inna kam har ta saba dan kullum suna tare bata zuwa ko ina, indai ta dawo gida toh tana manne da inna.
Mal. Mamman sunan direban inna, zai iya kai shekaru hamsin da wani abu, yanada iyali anan cikin garin, saidai matarsa ta dade da rasuwa, tanada 'ya'ya bakwai, tare dashi. Dukkansu matan sunyi aure, da yake 'ya'yan sa maza biyu ne, kai su suka rage, shi yana son auren indo, ita kuwa indo sam taki ta amince kuma taki ta fada dalili.
Inna na zaune a daki taji ana sallama daga can falonta, tace uwani, maza jeki fadi waye? Ta fita a guje, kamar ma zata fadi, inna tace, wai uwani bana hanaki guje-gujen nanba, salon kije ki fadi ko? Ina? Uwani kam bata saurara ba, tanufi falon ta iske mal. Mamman, ta fada jikinsa tana fadin baba dama kaine, inna tace in duba wanda ke sallamar?
Eh nine jeki fada mata. A guje dai ta koma sukai karo da inna, toh 'yar fama nidai kar kije kiji ciwo. Ta karasa falon, ta zauna, uwani ta dare kan cinyarta, tace a'a mal. Mamman kaine ashe, ka wuni lafiya?
Lafiya lau inna"
ina fata ba uwani ta kara yin wani abun a makarantar bako? A'a inna aita daina.
Kasan Allah bata daina ba, don da naje opening day dinsu, saida malamar takara min magana akan uwani, bata...........

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now