36

2.2K 162 0
                                    

KALLON KITSE

tun wancan zuwanka dakayi baba ya fadamin komai, toh ya kana ciki ko kuwa ka hakura?
"dole in hakura muzamil, inna bataso, inban hakura ba ya zanyi ne?."
muzamil ya gyara zama yace, 'dan uwa akwai wata hanya da za abi mai sauki, kuma itace abunyi."
jafar ya kara maida hankali sosai ga muzamil yana sauraransa, "kayi mantuwa jafaru, da wani kakan da yake bunza, kanin mahaifin inna, wanda shikadai ya rage masu, ko ka manta dashi? Kasan Kuma kasan baba sabo yafi kowa rigima a kawunan inna, inace shine dalilin rashin zuwanka gunsa..... ."
jafar ya dada masa duka yace, gaskiya ne muzamil wallahi sam na manta da baba sabo, da tuni angama komai, kasan abunda yasa nadaina zuwa? Saboda maganar aure nefa. Kai Allah ya barka dan gobe, toh amma zaka rakani ko?
"insha Allahu kuwa
saika shirya gobe dan Allah muzamil.
Toh Allah kaimu goben
"Ameen
washe gari tunda safe suka bar kebbi, zuwa bunza, tafiyar kusan awa biyu da rabi suka isa, ba karamin murna Baba sabo yayi ba, dan ya kwana biyu baiga jafaru ba.
Sai dai kuma yayiwa jafaru fada sosai akan abunda ya faru a baya.
Jafaru kam hakuri yake badawa, sai kuma ya fado maganar matarsa marliya, ya kuma tambayi 'ya'yansa nawa? Muzamil ne ke gaya masa bata haihu ba.
Toh me kake jira da ba zaka sake aure ba? Jafaru bafa yaro kake ba, ka duba ka gani, duk kanen ka da yara birjik, amma banda kai, wai kai bature ko?."
a'a baba ba haka bane, inji jafaru, lokacine baiyi ba kawu."
muzamil ya amshe maganar yace, 'ai baba abunda ya hanashi auren inna ce taki bashi matar da yake so, shiyasa ma muka shirya yazo nan, dan ka roketa ta sauko ayi auren."
"ita inna ta hana shi matar da zai aura?
Yayi tambayar cike da mamaki, "haka maganar take baba." nan dai muzamil ya kwashe labari yaba baba sabo.
Baba sabo ya dubi jafar shin ka tashi yin auren ko baka tashi ba?
"wallahi baba na tashi.
"toh shikenan, inaso ran jumma'a da safe kazo ka daukeni muje gun ita shatun nida ita zanyi magana ba sai nayi da inna ba, sannan inaso kai muzamil ka kai mana Alh. Yunusa can jega, dan ya zama shaida dan da yardar Allah ranan zan daura maka aure, saika siyo goro ka kawo sadaki, kuma shikenan sai kunzo."
jafar ji yake kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha dan tsabagen farin ciki, da ya cika masa ciki. Ai tuni ya cika baba sabo da naira, har yayi masa sayayyar kayan abinci.
Cike da murna suka isa kebbi, a wannan dare ko bacci ya kasa, dan murna. Haka yayi ta shirye-shiryen sa saboda jibi ne jumma'a, dan haka ko wuni baiyi gida ba, babu abunda bai tanada ba, wanda yasan zai bukata.
Ranar jumma'a da safe ya shiga gun inna, ya isketa ita kadai a falo, tana kari. Saida gabanta ya fadi, sabo da wani kwarjini na musamman da yake dashi a idonta, duk saita rikice, dan dama har yanzu tana jin tsoronsa fiye da dama. Gab da ita ya zauna, cikin manyan kaya yake, tunda take bata taba ganin yasa irin wannan kayan ba, sai a wannan ranar.
Lallai yau za ayi ruwa." ta fada a ranta, gabanta kuma kamar zai fashe, saboda faduwar da yake, muryarta na rawa tace, ina kwana uncle?." kallonta yakeyi cike da sha'awarta, bai amsa ba saiya dauke filet din data ke cin abinci, ya soma ci.
Tambaya ya jefo mata, "waya gaya miki ni uncle dinki ne?
"uncle wannan abinci na ne." ta fada a shagwabe, dan bakinta ya kalla, ji yake kamar ya tsosesu, toh amma ba hali. Ya lashi labbansa na kasa, yace, shikuma zanci, sai dai ki debo wani." toh ya za ayima ta mike, harta debo wanin, ya wani zauna haka, ya tare ko ina, da yake tana sanye da kayan makaranta ne, farar riga da wando marun, braziya ta saka, dan haka ana kusan ganin zanen bra din awajen rigar.
Tana mikewa idonsa sai a kirjinta, da sauri ta koma ta zauna, tana bakin cikin wannan hali na uncle din nata, wai meke damunsa ne? Duk kwanan nan saiya rika mata wani irin kallo da yake bata mata rai? Ita kuma sam bada gangan takeyin hakan ba, toh amma shi ko ajikinsa. Kallonta yaci gaba dayi
ita kuwa gabanta sai kara harbawa yakeyi, har yanzu muryarta rawa take, tace, uncle zanyi latti kuma ana duka,
ya juya yana ci gaba da cin abincin sa, "na tsare miki hanya ne? Ya tambayeta, "kizo ki wuce mana."
tana nan dai zaune bata motsa ba, har saida ya gama, sannan ya juyo ya dubeta, suna kallon juna, duk da kanta na kasa, duk ta tsargu, ita haushin kanta ma takeji, data saka wannan bra, dama ita ba kasa fai take sawa ba, saboda kunyar asan ta saka bra....
Ya tsinka mata tunani, "kinaji na ko? Inaso muyi magana ta fahimta, nasan da banso in fara magana dake ba, har sai naga abunda zai yuwu, toh amma daga ke, har inna kun dau abun da zafi, so a yau inaso inji naki ra'ayin akaina, kina sona?
Nan da nan yanayinta ya canza, shima ya lura da hakan, ba zato ta mike hannayenta rumgume a kirjinta, abun dariya ya bashi, dole ta koma ta zauna, ta hada kanta da gwiwarta, tana kuka.
Dan nayi miki tambaya shine ya zama na kuka? Toh Allah ya baki hakuri, ina so ki sani, ina sonki, so na gaskiya kuma na amana....." katse shi tayi, "wallahi ni bana sonka." cike da tsiwa take magana,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now