KALLON KITSE
Aka kwashe da dariya baki daya. Tun daga nan aka shiga surkunci tsakaninta da aunty nata, dakin indo ta koma baki daya da zama, saboda bakin da suke dakinta.
Ana gobe daurin aure jafar ya shigo gari, tunda ya shigo yake neman uwani, amma bai ganta ba, saboda 'yan uwa duk an zagaye shi, ana masa tsiyan abunda yayi, sai cewa yayi ai matarsa ce, tunda aka riga aka daura aure, wani zance ya kau, "ni inama take dan Allah a nemo min ita mana."
aka kwashe da dariya.
Shikenan ka hana ayi mata biki ko?
Eh! Aikai ta zolayarsa, ita kuwa gimbiyar suna can dakin indo ita da sauran mata da amare, hafiz ne ya isa dakin ya mikawa uwani waya, "gashi uncle nason magana dake. Da sauri ta karba, tare da barin wurin.
"hello." ta fada cike da kissa.
Haba baby bakisan na iso bane?
Kai uncle?
"tun fa biyar saura na shigo gari, wai ina kika shiga ne?
"ina dakin indo.
Toh gani nan zuwa.
A'a uncle ka bari har anjima.
Bakiyi missing dina ba kenan? Tayi shiru a ranta tace, kaima kasan nayi missing din naka sosai...." ya katse mata tunani, "promise me" zaki zo bayan sallar isha?
"yes zan zo insha Allahu.
Toh shikenan sai mun hadu i luv u." sai tayi murmushi kaman yana kallonta, amma bata ce komaiba.
Ana idar da sallar isha kuwa tayi wanka bata yi make up ba, sai dai ta shafa turare, ta jawo hafsat zoki rakani wurin uncle." a sanda suka isa saida suka kai baki kofar ta rike hafsat, "don Allah kada ki tafi, ki tsaya kila shi zaisa uncle yayi saurin bari na.
Toh shikenan a hankali suka bude kofar suka shiga.
Yana zaune gaban computer, da sauri ya tashi ya karaso gunta ya rungumeta, sam bai lura da hafsat ba, sumbar ta yake yi ba sassauci, ita dai hafsat tana tsaye amma ta juya musu baya, bakinsa akan nata ciki dabara ta janye, "i miss u baby, tell me u luv me?
Tadan ja da baya tace hafsat fa tana na, sai a lokacin ya lura da ita, a'a daughter ashe tare kuke? Ba tare data juya ba tace "uncle sannu da zuwa.
Yauwa, ya shirye-shirye?
Lafiya lau uncle.
To shigo mana kunyi tsaye waje."
ta shigo ta zauna, shiko riko hannun uwani yayi, "zo muje dakina in nuna miki wani abu."
uhm...ya lura nauyin hafsat take ji, sai ya juya ya dubi hafsat yace, daughter yi hakuri ki shiga gida inaso in gaisa da wife ko ya kika ce?
Kwarai uncle hakane." zata mike uwani tace, a'a kada ki tafi ai yanzu zan fito.
Ba yanzu zaki fito ba baby tunda kika zo nan, saina gama ganinki sannan zaki tafi." ta marairaice fuska, uncle gidan nan a cike fa yake.
Toh me ruwana da gidan?
Don Allah kayi hakuri.
Kema kin san bazai yuba, kin manta wata nawa mukayi bama tare." uncle...." yasa hannunsa ya rufe mata baki, "daughter sai da safe." hafsat ta kama hanya ta fice, suna shiga daki ya kulle da makulli, "bari inyi wanka, ko zakiyi?
Da sauri tace a'a. Yayi murmushi dan yadda ta hade fuskarta, sureta yayi suka shiga bayi, bata yi musu ba, sai dai sam! Bata so hakan ba, amma ya zatayi? Dole ta bashi hadin kai. Bata shigo cikin gida ba sai sha daya saura.
Tana shiga bayi tayi wanka, tazo tayi sallah, tayi sa'a babu kowa a dakin, inna tayi bacci, hafsat ta shigo, "toh magulmaciya me kika zoyi?
Kai uwani, Allah yasa isma'il haka yake, ya rinka nuna min soyayyarsa a fili, gaskiya kinyi sa'a uwani, Allah yasa mu a danshinki, amin. Ita dai tanata shirin barcinta, bata ce komaiba."
washe gari da karfe sha daya da rabi dai-dai aka daura auren hafsat da isma'il, sai kuma na hamza da fa'iza, gaskiya an cika sosai, ana daurawa akace za a wuce da amare gidajen su, dan haka rabawa akayi, wasu suka wuce kai fa'iza jos, ita kuwa hafsat aka wuce da ita abuja, da yake nan mijinta yake. Mirsisi jafar yace uwani bazata ba, danta tsufa, inna ma dama bata so tafiyar tata ba, dan gaskiya jafar ya fada.
Bayan baki da kwana biyu jafar yace zai wuce, yana shirye-shirye amma uwani na biye dashi a bayansa. Ya lura data shiga damuwa sosai, dan haka ya shiga kwantar mata da hankali.
"uncle ka kara kwana biyu mana."
a'a baby kinsan nace maki course na tafi Imo state zuwana ma nan akan dole ne da banzo ba, kizo mu tafi mana.
"uncle inna bazata yadda ba."
zata yadda inhar ke kika mata magana.
Niba zan iyaba.
Ajiyar zuciya yayi na rashin jin dadi, toh shikenan Allah sadamu da alheri." da sauri ta rungume shi tana kuka, rungumarta shima yayi yana lallashi, cike da sanyin jiki ya shiga falon da inna take zaune, ya sami wuri ya zauna, "inna zan wuce. Ta dubeshi cike da fara'a, toh Allah yayi albarka ya kaika lafiya." har zai mike sai kuma ya zauna., inna tace da wani abun ne?
Inna don Allah ki bari intafi da Aisha.
Uwani dake zaune gefen inna sai duk illahirin jikinta ya kara sanyi.
Inna taji tace kaima kasan bazai yuba....." uwani ta katseta "inna...zan...bi....shi" da sauri inna ta dubeta. Zaki bishi?
Da sauri ta sunkuyar da kanta kasa, "inna kiyi hakuri, ajiyar zuciya tayi, "ai baki komai ba uwani, na gani cikinki ya tsufa na san auta sarai da rigima.
Inna kin manta autan naki doctor ne, insha Allahu inna zakiyi alfahari dani."
ai ni koda yaushe ma ina alfahari dakai auta.
Bawai kuma bana sonka da alkhairi bane. Nidai inaso ka kulamin da ita kaji ko?
Da hanzari uwani ta rungume inna tana kuka, "inna kiyi hakuri.
Babu komai uwani duk abunda kike so shi nake so, dan haka ki tafi Allah yayi miki albarka, ya tsare minku baki dayanku. Amin suka amsa baki daya.
Har suka kama hanya amma uwani bata daina kuka ba, saida tayi mai isarta sannan ta hakura tayi shiru, suna isa Imo state da yake acikin barak akayi musu masauki, yana kula da asibitin dake cikin barak din. Masaukin dan dai-dai kuwa, saboda bed room biyu ne, da bandaki a kowane daki, sai falo da kicin.
A yau uwani tana zaune gaban T.v tana kallo, dan dama aikin kenan daga barci saici sai kallo, bata ma girki saita ga dama, amma koda yaushe suna cike da abinci kala-kala, kullum sai sunyi waya da inna, hatta abinci sai inna ta tambayi uwani kota ci a yau?
Kamar kullum sun gama hira da inna saita bugawa lawisa, duka biyu ta dauka, a'a amaryar yusuf ya ake ciki?
Ke dai uwani abun ba a cewa komai, kin san shekaran jiya saida uwar gidanmu ta gano bata da wayo.
Meya faru? Shafa min inji
a shekaran jiya matarsa ta biyu ta haihu, kina ji gobe ma suna. Toh a shekaran jiyan baban Al'amin (haka take kiran yusuf) ya kiramu yace, zai bawa kowacce kudinta a hannu, taje ta sayi abunda take so, ya bata one hundred and fifty thousand naira yace, na yaranta, sai kuma ya bata dubu dari yace, tayi tata sayayyar, kinga ya zama 250,000 kenan.
Ita ma maibi mata saiya bata hakan, amma kin sani itace mai haihuwar, sannan itace mai jama'ar, amma sai cewa tayi, ita bata yadda ba, ba yadda za ayi a rabashi dai-dai saidai ya bata dari uku, shikuma yace bazaiyi hakan ba, shine fa ta soma tayar da jijiyoyin wuyanta, shima da yake akan hakan nan yay niyya, a haka zai barshi, shine ta ajiye kudin tace, a bawa aunty murja ta hada, nan take yace ta dauka, ita kuwa ta kwashe tayi gaba abunta, shima din biris yayi da ita, shine jiya muna zaune dashi yana cikin bani labarin abunda ya faru texr ya shigo cikin wayarsa, ashe itace, wai tunda wulakancin da zai mata kenan to ita zata gida, kin san meya aika mata?
Uhm cewa yayi, ta tafi mana, yama bata saki daya, taje baki daya ta huta in kuma bata bukatar hutun taje tayi aurenta. Sam abun baimin dadi ba.
Sai dai bansa kaina cikin al'amarin ba, daya nemi shawarata kuwa da bai aikata hakan ba.
Nima banji dadin wannan labarin...." daga mota taji ance wani labari aisha?
Saida ta dan firgita, sannan ta dago ta dubeshi tace "Oga sannu da zuwa, tare da mikewa dakyar, "lawisa sai anjima" autan inna ya shigo. Ba lawisa kadai tayi dariya ba harda shi. Anan falo suka ci abinci daya shigo dashi, nan da kwana biyar fa za a fara azumi kin shirya ko?
Aikuwa zanyi abina, sam! Bana son a bini bashin azumi.
Toh Allah yasa zaki iya. Haka ya shigo da provision din daya shigo dasu. Sallah na saura kwana biyu suka shiga kebbi, murna a gun inna kaman ance zata shiga aljanna, saida suka samu nitsuwa sosai sannan suka kebe ita da inna, sai hira sukeyi, abun nasu gwanin sha'awa, shikuwa jafaru ya zama dan kallo dan yasan sun manta dashi a falon.
Dan haka ya mike zani gidan Baba yunusa mu gaisa. Basu ma san yayi magana ba, haka ya wuce ya barsu,
da dare uwani ta fito da kaya da gyale, harda set din sarka na english gold, ta mikawa inna, ita kuwa sai sa albarka takeyi, tare da nuna farin cikinta matuka. Lace ne kala biyu sai super halandis guda uku, da kuma shadda tasha dinki, kowacce da inna ta gwada sun mata kyau ainun, kamar an gwada.
Washe gari gidan ya cika dan ba wanda aka bari abaya, da yake dama kowacce sallah a gida suke yinta, kuma a lokacin suke meeting dinsu na cigaban rayuwarsu, bayan sallar isha suna zaune a daki, sunata hirar zamantakewarsu da mazajensu, fa'iza tace nifa akwai abunda ke damuna fa da hamza." hafsat tayi saurin cewa "wace irin matsala kuma?
Ya cika fada dayawa, sannan yanada fushi, abu kadan nayi sai kuka ga kamar zai cinye ni, akwai ma ranar daya dokeni! Su duka suka hada baki, "ke ko kina zaune ya dukeki?
Hawaye ya gangaro mata, "niban san yadda zanyi ba, komai nayi bayyi ba ko fushi nakeyi dashi sam ba abunda ya dameshi.
Sau nawa ya doke kin?
Sau daya ne shima a baya nane yayi min dundu guda daya, ni kuma Allah ya taimakeni akwai sandar mofing ita na kwala masa, to shine fa na samu nutsuwa.
Allah ya taimakeki da kullum kuka yi fada saiya dokeki.
Wata ran ma ni rasa abunda yake nufi nakeyi, dan am totally confused "
kin fadawa aunty kuwa?
A'a ai in na fada mata, dakunji.
YOU ARE READING
KALLON KITSE
General FictionKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi