KALLON KITSE PRT (16)
Babu abun banza aciki, duk kayana ne masu tsada, hatta takalma daga gucci sai vince ire-irensu aka saka, ko waye abun na bashi mamaki, zainab tace, lallai kuwa Allah yasa alheri.
Da daddare suka kwashi akwatuna musamman akori-kura aka samo musu suka kwashe, sukuma suka shiga jeep, saidai ba dukkansu suka tafi, daga zainab sai salaha, goggo mariya da goggo zulaihat matar Alh. Yunusa, su shida suka kama hanya,.
Suna isa aka bude get suka fito, abun mamaki ba wacce ta fito tarbarsu, har saida sukayiwa mai gadi magana, "shin mutanen gidan na nan kuwa? Yace suna nan, inaga suna sama, bari inyi musu magana.
Da yake babu wurin zama a kasa haka sukayi cirko-cirko a tsaye, sunfi karfin minti goma sha biyar, har zainab ta fara tsekuwa tace, "kodai ba a fada musu zuwan mu bane? Uhm! Bari ku gani".
Ta hau har sama abun mamaki mata ta gani sunkai su bakwai a zaune, ko wacce ta kame a kujera kamar sarauniya, sun caba kwalliya, tayi sallama ta karasa ciki da fara'a tace, "mutan gidan ashe kuna nan, muna can muna jira azo ayi mana iso? Ga kaya can dan Allah azo a tayamu dauka.
Dayansu tamike tayi ciki, sai tafito tace "sannu dai, ai sai kuyi kokari ku dauko, dan gaskiya mu bazamu taimaka mukuba, haka zaku rike mana 'ya kenan sai mun taimaka muku?.
Baki daya falon suka kwashe da dariya, suka shareta, ta koma kasa, fuskarta ba kyau, salaha ta biyota, "ya akayi yaya?
"menene ba ayiba, wai mu dauki kayan mukai sama, su bazasu iya taimakawa ba.
"tabdijam me suke nufi? Mu zamu dauki kayan mukai sama?.
Goggo mairo tace ba komai kuzo mu dauka, ai mune muke nema, kila al'adarsu ce haka.
Haka suka dunga daukar kaya suna kai sama, ba abunda yafi baya musu rai, kamar yanda suke masu wani irin kallon ko in kula, wani lokacin kuma suyi dariya. Saida akazo kan manya jakuna, salaha tace gaskiya goggo bazamu iyaba, musa mai gadi yakai da direba."
"toh ai kila basa so namiji ya shigar musu gida.
Zainab dama haushi ya kamata, tace wallahi goggo saidai suji haushi, amma ba yanda za ayi mu wahalar da kanmu a banza, kai direba kira mai gadi kuzo ku tallabi kayan nan zuwa sama.
Mai gadi ya zaro ido yace, "kiyi hakuri basu bani iznin shiga gidansu ba, ai sai akoreni dan Allah kuyi hakuri.
Zainab taji haushi tace, kuzo sama goggo ku huta, ko ruwane kusha, dubi yadda kuka gaji? Basuyi musu ba dan gaskiya zainab ta fada, da suka isa falon saima juya musu baya da sukayi, can gefe suka samu wuri suka zauna, sai kallon-kallo akeyi. Can goggo ta mike ta isa tsakiyar falon tace "wai wannan mutane kunsan darajar mutane kuwa? Ku sanifa aure muka zo nema, sannan kunsan dai inda ba dan ya so 'yarku ba da baku ganmu nan ba, toh ga kaya nan, mun kawo Allah yasa ayi lafiya, ku tashi mutafi.
Da suka fita cema driver sukayi su wuce masauki, acikin mota mita sukai tayi jafaru ya dauko musu wulakanci. Salaha tace ni ai matsuwa nayi in fito kunji wani karni a gidan, anya 'yan maiduguri ne mutanen nan kuwa? Kowa dai yasan 'yan maiduguri da turare.
"a toh kedai kya fada, nikam bari mukai dole in kira inna in fada mata irin mutanen da jafar ya jajibo mana."
"a'a zainab kada ki tada mata hankali, kin san fa bazataji dadi ba. Saboda haka ki bari har sai munje gida, duk abunda za ayi sai ayi.
Zulaihat tace ko kunsan sadakinta dubu dari uku da hamsin da wani abune?
"ke don Allah? Amma jafar cewa yayi dubu dari ne."
"uhm haka suka shirya da iyayensa maza, suma haka suka cewa inna, saboda jafar kuka ya rinka yi musu tamkar karamin yaro, shiyasa suka rufe abun, don haka muma ba ruwan mu, dan sun ja mashi kunne yaki.
Zainab tace shikenan kuma sai musa masa ido, dan ya nawa?.
Inji zainab shine karami dole shi ya kamata ya bimu, bamu zamu bishi ba."
"amma kinsan ba yaro bane, da yanzu haka ya tasamma talatin ko?
"hakane, amma ai babba, babbane ako da yaushe karami take ganin na kasa dashi, dole muyi masa magana."
sun isa gida sun iske shi zaune anata hira, yana jin horn ya fita da sauri ya taryesu, yanda yaga kowacce ta sha jinin jikinta, ya san akwai wani abu, ya nemi wuri ya zauna, su zainab kam kwanciya sukayi, dan sun gaji. Goggo mairo ce tace "jafaru anya mutanen nan sun san darajar 'yan uwan miji kuwa?
Ya dan saki murmushi, "goggo su haka al'adarsu take.
"eh hakane tunda kai ba ayi maka, baka ga yanda suka wulakanta mu bane.
A take ya dauki waya ya danna numbers din marliya, kamar da gaske, nan kuwa duk barazana ce, dan ba abunda zai iya.
Goggo tace wa zaka kira?.
Yace "marliya zan kira in fada mata magana, dan menene zasu wulakanta min iyaye?.
Tace, toh ai ita bata saniba, iyayenta ne da laifi, in baka saniba ko ruwa basu bamuba bare kujerar zama."
"tabdijam ai dole in samu Ammi in fada mata a yau suka karbi kudi guna, wai zasu taryeku, dole su shiryawa baki........zainab ta katse shi, "nikam kasan Allah auren nan ba dole bane jafar, kayi hakuri ka nemi wata, kasan inda shanun gaba tasha ruwa, toh na bayama nan zata sha, ka hakura da auren nan ka nemi wata.
Idonsa sukayi jajir kamar garwashin wuta, ya dubi zaiba, "haba yaya ya zakice haka?
YOU ARE READING
KALLON KITSE
Fiksi UmumKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi