KALLON KITSE
Baidai ce mata ci kanki ba, ya wuce ya shiga dakinsa.
Yayi wanka ya shirya, ya fita wurin jamila ya nufa, da yake tunda sukayi fada ya raba musu wurin zama, dama tuni ya fada mata yana gari, dan haka ta shirya masa abinci, yana shigowa harabar gidan ta taho da gudu ta rungumeshi, tun a waje suka fara shegantakar tasu, har suka isa falo.
Nan suka baje, bayan ya gama cin abinci, ta jawoshi suka shiga daki, sukayi ta shedancin nasu. Allah dai ya shirya Ameen.
Sai sallar mangariba ya shiga yayi wanka, ya wuce masallaci, daya dawo ya isketa zaune bakomai ajikinta.
Wata sha'awarta ne ya bijiro masa, suka ci gaba da abinsu cike da nishadi, shiyasa yake son jamila, sam bata gajiya da irin wannan harkar, ga shi mabukacine kwarai da gaske, yana da sha'awar mace a tattare dashi.
Da aka neme shi yaje jaji completing din cos daya soma, kafin ya samu major, tareda jamila ya tafi, zaiyi kusan wata uku a can, ita dai marliya ta nan abun tausayi, duk tabi ta lalace, saikace ba itaba, duk ta rame ta zama kamar mai ciwon kanjamau, saika ce wanda iyayenta suka tsine mata. Ashe rayuwa na iya juyawa mace acikin kankanin lokaci?
Toh gashi dai marliya ta shiga,kuma taji abinda takeji, shin dama duk mai irin halina marliya wadda bata da wurin zuwa sai na bokaye da malamai a zatonta sune gatanta, toh sai gashi ita da banza duk daya, toh saimu dage mu roki Allah shine yasan abinda ya dace damu, dan haka mu rokeshi abin daya fi zama alkhairi, shine zai bamu.
Ubangiji yasa mufi karfin zuciyarmu(ameen)
a kebbi kuwa tunda aka daura aren jafar da uwani, sam inna ta kasa samun kwanciyar hankali, dan yadda ita uwanin ta tada hankalinta, abu daya inna ta fada ta kwantar mata da hankalinta, idan jafar ya dawo zatasa ya saketa.
Tunda inna ta furta haka, sai uwani ta koma sha'aninta kamar da, a makaranta kuwa lawisa ma bata san an daurawa uwani aure ba, dan ita a ganinta abun kunya ne ace tanada aure, kuma tana zuwa makaranta.
A haka ma saita rika hira da hamza, acewarta ai inna tace za a raba auren da aka daura mata, dan haka basai ta daina ganin hamza ba, yarinta kenan.
A yau watan jafar hudu rabonsa da kebbi, ita kuwa uwani ta samu hutun 1st term dinsu dan haka tana gida.
Tunda safe ta shirya ta tafi gidan su lawisa, a ranar jafar ya shigo gari. Yana isa cikin gida, inna ta tareshi da fada, ta inda take shiga bata nan take fita ba, a karshe dai cewa tayi ya rubuta takardar saki ya bata, biro da paper ta mika masa,
jafar bai amsa ba, kuma baice mata kala ba, amma duk yanayinsa ya canza, hardai kalaman daata fada na karshe, duk hankalinsa ya tashi, ya rasa inda zaisa kansa, sai a lokacin yace inna kiyi hakuri, amma bazan iya sakin uwani ba." jin mari yay a fuskarsa, "ni kake fadawa magana? Toh wallahi baka isa ba, baka barin gidan nan saika rubuta mata sakin nan, inba haka ba kuwa, duk abunda na maka kai ka ja.
Har yanzu kansa a kasa, can dai yaga abun yana so ya zama haka, saiya karbi paper da biro tare da mikewa tsaye, cikin sauri ya fice daga falon.
Ta biyo shi tana fada, shikuma tuni ya bar gidan.
Gidan Alh. Yunusa ya tafi, yayi sa'a kuwa yana nan, dan haka ya zayyane masa abunda ke faruwa, lallashi Alh. Yunusa ya far dashi, dan yadda yaga jafar ya fita hayyacinsa, ya kuma saka aka kawo masa abinci, "bari inke in ganta."
shi abun yana bashi mamaki, wai dama haka inna takeda taurin kai?
Bari insha Allah yanzu gunta zanje."
daya je gunta, nunawa Alh. Yunusa tayi ita batayi kananan furuci ba, yadai zauna ya mata nasiha tare da tunasar da ita abubuwa da dama.
Nan da nan jikinta yayi sanyi, itama ta rasa dalilin data keyiwa jafaru haka, kodai abunda ya fada gaskiya ne, bata yafe masa ba? Ta tambayi kanta.
Toh Allah yafe mata, Allah ya shirye shi." ta fada afili, Alh. Yunusa yace "amin, abunda ya kamata ki ringa yi masa kenan fatima, kiyi ta yi masa addu'a Allah zai amsa addu'arki, haka dai Alh. Yunusa yata bata baki, harta sauko, dan yanda yanayinta yayi.
Tunda ga ranar bata sake yiwa jafaru maganar takarda ba, amma kuma bata sake masa fuska, ita kuwa uwani tunda taji labrin yazo ta faman buya a tsakaninsu.
Yau kwanansa biyu da yini daya, amma baisa ido akan uwani ba, yanzu ma ya shigo cikin gidan yanata kwala sallama, amma shiru ba a amsa ba.
"toh ina mutanen gidan suka shiga ne? Ya tambayi kansa.
Can daga kicin yaji faduwar tangaram, ya isa kicin din da sauri.
Uwani ya iske tsugunne gaban tangaran din, a tsorace ta mike, saika ce wadda taga kura.
"dama kina jina ina sallama, amma kika yi banza dani? Ya shiga kicin din, ita kuwa sai ja da baya takeyi, can ta tsinci kanta da gaishe shi, ina wuni uncle?
Bata san sanda ya isa gabanta ba, waye uncle? Bata iya amsa masa ba.
Yaci gaba ina kika shiga kwana biyu ina nemanki a gidan nan ban ganki ba? Da sauri tace ina nan."
ke baki san miji tattalinsa akeyi ba? Yayi tambayar cike da sha'awarta,
YOU ARE READING
KALLON KITSE
General FictionKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi