Kallon kitse
bare aje ga batun girki, ga baby zahra tana ta tsala ihun yunwa, ta hanata ko nono, kuma ko kofa bata bude ba, bare taje kitching.
Ya shigo gidan yana fadin my baby kina ina ne? Kukan zahra ya jiyo tanata tsalawa, da sauri ya nufi dakin ya murda kofar amma yajita gam.
Ya soma kwnkwasa kofar, yana kiran Aisha! Aisha...toh ko tana bayi ne? Ya tsananta bugun kofar, shiru sai zahra ma da kukanta ya tsananta, wata zuciyar tace mishi, kodai ta mutu ne a ciki? Ko kuma wuta ta kama? Wannan tunani yana zo mishi rai, nan da nan ya kama kofar duk da karfinta ya jijjigeta, ya aje a gefe, da sauri yayi cikin dakin da gudu.
Sororo ya tsaya ganin uwani kwance kan gado tana risgar kuka, kasa kuma ga zahra tayi kuka harta gode Allah, hawaye share-share ga majina, sannan ga fitsari nan duk dai abun sai godiyar Allah.
Ya daga zahra ya nufi uwani, "lafiya Aisha? Ya zaunar da zahra kan gadon, sannan ya dgo uwani, "meya faru? Ta kwace jikinta, sannan ta kuma kwanciya, zai tabata tace kada ka sake tabani, na tsaneka! Ta soma rusa sabon kuka.
Yace me nayi miki? Ya kamata ya girgizata yace, "nace meya faru ne? Ta tashi dole kace meya faru, ai ka fini sani, waccen matar da ka ajiye menene matsayinta, karuwa ce ko matarka ce?
Gabanshi ya fadi badai marliya bace ta dawo ba? Yace ina take? Ya fita da sauri ya duba ko ina, baiga komaiba, yace ni banga kowa ba, ko ko baby kin kwan....." ta katse shi, "kada kace min komai tunda duk kokarin da nake maka baka gani, saika bi matan banza." yaso ya lallasheta, amma taki sauraron shi, shida kanshi ya shiga toilet yama zahra wanka, ya saka mata kaya. Yace toh maganar abinci fa? Ta mishi wani duba sannan tace, "banyi ba, ka duba in akwai sauran wanda dadiron tayi ta rage saika ci.
Yace "kina haukane zaki rinka kiramin dadiro? Tace, "toh mace bata sanka ba haka kawai zata zo nan gidan? Kaifa tace take nema, sannan kai tsaye dakinka ta wuce, ni nafi karfin wulakanci."
taci gaba da kuka, yace, "toh wannan yarinyar me taci?
Uwani tayi tsaki, ta mike ta shige toilet, yace, "ni kike ma tsakin? Bata tanka ba, tayo alwala tazo ta dora sallah. Ya dauki 'yarshi ya fita yaje ya hada mata tea, nan ta kama sha, tausayinta ya kamashi, ya fito ya zauna a falo yanata tunanin wannan wacece? Wacece tazo mishi gida ta rusa mishi zaman lafiyarshi.
Zahra kam ta koshi, saita sauka ta nufi gurin mummy dinta, ta hau cinyarta ta kwanta, sai bacci.
Da dare ma haka akayi ta rigima, yana sone ta bashi hakkinshi, tace, ai ita sam! yajegurin karuwarshi, yayi niyar gwada mata karfi, saita tashi zahra, nan ko ta soma tsala ihu. Ya fita rai bace, kaya yasa ya fita, kai tsaye ya nufi club, ya sha, ya sha, yayi tatul, har ya manta rabon daya sha barasa irin haka, nan take ya bugu har hankalinshi ya kauce.
Jamila wanda dama tasan hakan ce zata kasance, tana gurin sannu a hankali tazo ta kamashi cikin motarshi taja shi sai gidanta.
Suna isa tun daga falo aka soma lalacewa, dama sunyi missing din juna, a takaice sai karfe biyun dare ya dawo, da safe ma ya shiga dakin suna kwance ita da zahra, zahra dai bacci take yi, amma ita uwani idonta biyu, ciki-ciki ta amsa mishi sallama, don sanin muhimmacin sallamar ne ta amsa, daga nan yace zai wuce, ta dube shi dama rikeka nayi?
Ya shafi fuskar zahra yace saina dawo." tayi banza dashi, ya matso, "bazaki ce in dawo lafiya ba? Tace kadawo koma yaki mana ina ruwana? Kamar zaiyi magana saikuma ya fita.
Lallai jamila ta lalata zaman lafiyar gidan, domin tundaga ranar kwanciyar hankali yayi kaura a gidan duk da inna suna waya kullum amma bata sanar da ita ba, saboda tasan in inna taji, lallai ranshi zaiyi mugun baci.
Ita kam tana son mijinta, saidai dole ta nuna mishi cewa ya tabota, shikam jafar club ya dawo sabo, sannan jamila da sauran irinta, don haka uwani ta jika nata tasha.
Kafin wani lokaci uwani ta fita hayyacinta, duk ta rame ta lallace, kai hatta zahra ta rame domin bata samun kulawa kamar da.
Yau kusan sati biyu kenan da samun wannan matsalar, jamila tace tafi son zama a gidanshi, yace ta bari zai duba, duk yanda yaso ko magana su ringayi da uwani, amma abin ya faskara, ta daina abinci ta daina kwalliya, duk ta rame ta kare, haka nan suka ci gaba da zama, har tsawon wata uku, daka shigo gidan zaka san gidan babu zaman lafiya.
Yau lahadi tayo wanka, zahra na bacci, don haka tayi niyyar zuwa nan kusa dasu, donyin kitso, ta gaji da gashin haka. A falo ta wuce shi, ya kalleta duk ta rame, still tanada kyau, kuma yana sonta, yace "ke uwani ina zaki je? yana magana ne cike da iko.
Kallonshi take yi, yau uncle ne kece mata uwani? Tayi kamar bata jishi ba, yace toh bada iznina ba." ta tsaya kamar ta wuce, amma saita share ta dawo ranta bace.
Da dare ya shigo dakinta ya rasa zuciyarshi tana mishi kalatarta. Zahra tana bacci ya dauketa ya kaita dakinshi ya dawo, uwani tana zaune tana kallon rashin ta ido gurin namiji.
Ya dubeta nazone ki bani hakkina, kota dadi kota rashin dadi...tace kasan Allah nifa bazan yarda asakamin kanjamau ba."
ya falla mata mari.....Ya falla mata mari yace, "ina wasa dake ne, wake da kanjamau? Duk da hakan kun san uwani da tsiwa, sai cewa tayi ka mareni? Toh ai ba karya bane, baka bin mata ne? Yace na bisu, yanzu ma na fara indai bin mata ne zaki zauna keda dadirona a gidan nan." ya fita tace, "oho dai, ba zan yarda a manna mini ciwo ba.
Yana fita sai gurin jamila, ya cebota da kayanta, yazo ya ajeyita dakinshi.
Uwani ta fito da safe don shiga kitching ta dan sama musu abun kari, ita da 'yarta, sai kurum ta samu jamila tana faman girkin soye-soyenta take yi, hankali kwance, ko ajikinta ko tana sanye da rigar bacci wadda bata hana aga jikinta ba, daga inda uwani take tana kallon pant dinta.
Hakanan jikinta babu bra, mugun bakin ciki da mamaki ne ya hana uwani magana, ga mamakinta sai ganin uncle tayi ya fito daga dakinsa, yana sanye da singileti fara tar! Da gajeren wando na kaki, ya wuceta ya shiga kitching din batare da ya kalli inda uwani din take ba, rungume jamila yayi ta baya, hannunshi tsaf kan kirjinta, ya jata a gado, domin ya bata ran uwani, lallai kam ya bata domin hankalinta ya tashi, taja tsaki tayi dakinta, kuka ta saki mai karfi wai ko zata ji sanyi a ranta, haka zahra ta zuba ma mummynta ido tana kallonta.
Yinin ranar a daki tayi shi, shikam yau dama bazai fita da wuri ba, don haka falo suka yada zango tana jiyo su, ta rufe kofarta gam! Zahra ma tanata kuka tana son abinci, amma taki ta bude.
Shima ya jiyo kukan zahra, duk da kukan yana sukan ranshi haka ya share yayi tamkar bai jiyota ba, yayi hakan ne don ya kara mata haushi, duk da yana da key din dakin tunda ya jijjige kofar da hannunshi ya mallaki keys din dakunan gidan, bayan yasa an gyara. (hmmm namiji kanin ajali lolz).
ikon Allah uwani take gani a gidan na, domin dai jamila ta samu gindin zama. Rayuwarta takeyi tamkar matar megidan, har wani jinkai take tare da isa, da kuma iko, hakan yana matukar bawa uwani haushi, kuma tana hakan saita bar mata abun kwatance.
Haka kullum take rayawa aranta, duk da wannan bakin ciki da jafar yake tura ma uwani hakan bai hanashi jin sha'awarta ba, tana matsa mishi, sannan ga jamila da kullum tana biya masa bukata, sau uku ko sau hudu a rana, bata gajiya tamkar shi, amma uwani daban ce. Sai dai yarinyar ta saka girman kai, ya kyaleta taje ta rike kayanta, tunda yasan akwai irin su jamila a gari da sai ya ture.
Wata safiyar litinin uwani ta fito daga dakinta zuwa kitching, jamila kuma dake kitching tana kokarin fitowa dan jafar na sauri ne zai fita, sauri take kota na sani? Oho! Ta bangaji uwani daga nan ta wuce, nan fa ran uwani ya baci ta bita da sauri, tasha gabanta, tace kina gani kika bangajeni? Jamila tace "na bangajekin ke wacece a gidan nan ne, me zakiyi? Banza wadda miji baisan da zamanta ba...." kafin ta karasa uwani ta sauke mata wani wawan mari, tare da daga kafa ta shureta a ciki, nan take ta zubar da abunda ke hannunta, ta durkusa tareda rike ciki tare da sakin ihu.
Jafar dake cikin daki ya fito da sauri, mari ya sakar ma uwani, sannan ya kama jamila, uwani ta dubeshi nika mara jafarr? Ya dago ya kalleta domin bata taba kiranshi da sunanshi ba, sai yanzu.
Yace "na mareki ko zaki rama ne?
Tace "zan kuma rama kuma zaka gani." ta nufi dakinta.
Washe gari kuma da rana, misalin sha biyu tana dafa ma zahra indomie saboda zahra akwai cin indomie, jamila ta sameta cikin kitching ta soma tsaki, ta dauki kofi da zata fita kuma ta bangajeta, ai ko magana uwani bata tsaya yi ba, ta dauki flate ta kwada mata a goshi, sai ga jini.
Nan ta fadi, jafar na cikin daki shigowarshi kenan tazo dauka mishi kofi, ganinta kwance tana ihu yasa shi jin takaici, "wato ke bakya jin magana ko? Tace Eh bana ji din..." mari ya wanketa dashi, tace wallahi jikin wannan karuwar taka zan rama, aika ban mamaki wallahi, dana san haka kake bazan aureka ba, tunda a cikin manyan laifuka babu wanda baka aikatawa..."
"ke! Ya daka mata tsawa, dai-dai da shigowar inna, wadda tayi niyyar kawo ma uwani ziyarar bazata yau, domin koda ta taso suna hanya tayi waya da uwani, amma bata ce tana kan hanya ba.
Jin hayaniya gurin kicin inna ta nufi can, tsayawa tayi tana kallon uwani wadda ta jeme ta lallace, ta kade, kasa ga jamila kwance cikin gajeren wando da 'yar babi, hannun uwani inna takama suka nufi daki. Shiko jafar hankalinshi ne ya tashi matuka, ya biyo su dakin, nan yasa mu inna kuka uwani ma kuka. Inna ta bude wardrope tana kwashe kayan uwani, tana sakawa cikin akwatina, nan fa sabon tashin hankali ya sameshi.
Da sauri yaje ya rike hannun inna yana fadin, "don Allah inna tsaya kiji. Ai inna tana juyowa sai kurum ta wanke mishi fuska da mari, ya kuma cewa bari kiji." ta sake wanka mishi wani marin, ya kuma bude baki zaiyi magana, wani sabon marin ta wanka mishi.
Hakan ne yasa shi fita da sauri, ya nufi jamila wadda ta tashi ga jini na zuba, ya hauta da duka, yana dukanta tana ihu, inna tace kudai kuka sani." ta hada kaya cif! Suka fita, tasa direba yazo ya fita da kayan. Nan take ko ruwan gidan jafar inna bata sha ba.
YOU ARE READING
KALLON KITSE
General FictionKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi