KALLON KITSE PRT (24)
Tace, wannan ai mai sauki ne, tana iya hanashi, yace ba damuwa sannan kuma zata rinkayin hayaki da daddare, amma zata ringa shiga da bakaken kaya a duk lokacin da zatayi hayakin, ta amince da haka, data tafi gun dayan bokanta, shi kuma cewa, yayi intana so ta rike jafar sosai, saita rinka bashi hadin kai gurin kwanciya, sannan ya bata wasu layu huda biyu, yace ta rinka sawa a kasan filo duk in zasu kwanta,.
Daga nan ta wuce bauchi gun malaminta na can, shima haka din yace da ita, ta rinka saduwa da mijinta sosai, danshi kuma yanada sha'awar mata sosai. Tun anan ta zama comfuse ta rasa nawa zata dauka, dan dai tafi yadda da aikin shanshani, toh amma ita kuma tanaso ta rinka kasan cewa da mijinta, don dai itama ba baya ba wajen sha'awar da namiji, tun a mota ta yanke daukar shawarar malaman biyu da zancen su ya zama daya, ba tare da ta nemi shawarar shanshani ba.
Jafar shi dama Allah yayi shi da sha'awar mace, dan haka dama sun saba in gimbiyar bata nan, saiya kasance da jamila, suyi yadda ransu keso, in gaskiyane tsafi meyasa basu fadamata ba, ko suma sun gaji da la lurarta ne? Dan sau dayawa zatayi aiki, amma bata bada cikakken kudi, sun san kuma tana samu, dan hakane suka barta duhu? Oho Allah ya ganar da ita gaskiya amin.
Ta iso gida ta iske jamila sanye da da wando, wanda ake kira pencil jeans, da riga 'yar karama, tana zaune suna hira da jafar. Ranta ya baci sosai, sam! Basu san da shigowarta ba, wucewa daki tayi da yake ta gabansu zata wuce, sai a lokacin suka ankara suka mike buzut! Suna yi mata oyoyo, bata tsaya tanka musu ba, ta wuce daki. Dama ako da yaushe tayi tafiya, toh haka zata rinka samunsu acike da nishadi, ta rasa dalili, duk da bata zargin wani abu na faruwa a tsakaninsu, tunda tasan jafar baya iya kasancewa da kowacce 'ya mace sai ita.
Jafar ya bita daki duk ya sukurkuce, ta banka masa harara, "nikam bana son yadda kuke zama da jamila kuna hira, dubi yadda kukayi, kuna cike da nishadi, wai meke tsakaninku ne haka?."
"haba sweety me tsakanin mu kuwa? Kawarki ce fa? Ki tambayeta mana." yana magana ya tausa mata kafadarta, nan fa sha'awa ta birgizo mata, suka hau gado, shikenan ta manta.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, abun mamaki a yau jafar ya tashi da wani azababben ciwon kai, da kyar ya tashi sallar asubahi. Ya tsinci kansa da wasu irin tunani, na ban mamaki, toh wai ya akayi baya jin labarin su inna? A yau yai mafarkinta, tana ce masa "auta ba zaka dawo gida ba mu ganka?."
shi ya manta yaushe rabon da yaji muryar mahaifiyarsa, meke damunsa? Sai a lokacin ya fara tunawa da 'yan uwansa, a ranar sukuku ya wuni, sam ba walwala a tare dashi, meke damunsa, da har zai guji mahaifiyarsa?
Daya fita gun aiki ma sam bai saki ransa ba, daya dawo gida kuwa ya share kowa. Suna zaune a falo koda ya shigo, bai kalli inda sukeba, ya shiga daki. Abun yabawa marliya mamaki, taya zaya shigo yaki gaidata, harma ya wuce ko kallo basu ishe shiba? Ta bishi dakinsu tana wani yatsuna fuska.
"ya ya ka shigo mana gida haka, fuska ba annuri? Bana hana irin haka ba?." kallonta ya rinkayi kamar ma ba dashi take magana ba, karo na farko kenan tun aurensu da zata nuna mata laifi bai nuna mata abun ya dameshiba. Ta karaso gunsa ba dakai nake magana bane jafar?."
idonsa sunyi jajir ya dubeta saida jikinta yayi sanyi, sam bata taba ganin fuskarsa ta zama haka ba, sai yau, yace "banaso a dameni, banjin dadi." haka kawai ya fada ya kwanta, data lura kamar da gaske baida lafiyan, yasa taja jiki ta zauna a gefensa akan gado, ta kai hannunta kan goshinsa, "amma jikinka ba zafi?. Yace, "nadai fada maki banda lafiya inaso in huta."
haka tabar dakin, tana tunani. Jamila ta lura da hankalinta ba a jikinta yake ba, dan haka itama tabar mata falon, ta rika tunanin meke faruwane, koda yake lafiyane bai dashi, dan haka ta cire damuwa a tare da ita.
Sun sami kamar kwana hudu kullum haka yake fita, kuma ya dawo ya shige dakinsa, ya kwanta. Wani soyayya da kasancewa da marliya babu, toh dama ita tana fita taje ta wala a waje, dan haka abun bai fara damunta ba, ansami sati daya abun duniya ya ishi jafar, wannan wane irin rayuwa yakeyi hakane?
Meke damunsa ne, ace yadau dogon lokaci ba tare da yaje yaga iyayensa ba? Anya zai gama da duniya lafiya kuwa? Tambayar kansa yakeyi, alokacin yana zaune a falonsu, yana kallo, duk da hankalinsa ba kan t.v yakeba, marliya ta shigo cike da kasaita, zata shiga dakinsu, saiji tayi daga sama kamar a mafarki, ke daga ina kika fito?
Bata yarda da maganan dataji wai da gaskene ba, dan haka, sai taci gaba da tafiya zuwa bakin kofar dakin. Ta kumaji ance badake nake magana ba ne, ko bakiji abunda nace ba?." ta juyo cike da mamaki "dani kake? "toh dawa nake, koba ke kadaice mutum anan ba da zan iyawa magana ba?."
gabanta ya fadi, "meke shirin faruwane da ita? Kaddai asirinta ne keson tonuwa? Koda yake mallam yace mata yanada tsananin kishi, kaddai ya ganta a hamdala motel?
Na da nan tayi ta maza tasha jinin jikinta tace, yaushe kafara kula da rashina acikin gidan nan,
YOU ARE READING
KALLON KITSE
Narrativa generaleKallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi