37

2.1K 165 0
                                    

KALLON KITSE

cike da tsiwa take magana, "kuma bana kaunarka, ni inada wanda nake so.... ."
da sauri yayi mata bal a baki, idonsa tuni sukai ja, abun ya bashi haushi, da sauri takai hanunta baki, wani kuka ta saki.
Kuma bakin nata bai mutu ba, "ni har abada ba zan taba sonka ba, mugu kawai." ta mike zata wuce, ya rike hannunta, tayi iya fisge-fisgenta harta gaji, amma shi ko gezau.
Ke wai bakiji ina magana bane? Nace ki saurari abunda zan fada miki, kin sani bana son raini, ni 'yan mata keso, dan ma kin samu harna furta miki kalmar So? Toh bari kiji nidin nan dole ki soni, dan dole ki aure ni, in Allah ya yarda.
Ya saketa tare da kuma tsareta, "saboda inna ta lalataki, har ya zama bakya shakkar fadawa gwarzon namiji iri na magana, an gaya miki inda nayi saurin aure, ai dana haifi kamarki, dan haka ki iya kanki, dan nace ina sonki, toh bazan yadda ki raina niba."
ya kauce mata, a guje tabar falon, tana mita, "nidai nace bana sonka, kuma bazan soka ba."
"yarinyar nan ta rainani sosai, koda yake yasan halinta, tun ba yanzu ba, tsiwanta dama yayi yawa, sai dai ba karfi. Hannunta daya rike ma kamar auduga, tun tana karama ya sha zuwa ya iske malamarsu, an kawo karanta tayi fada, kuma itace da tsokanar fadan, "toh amma ni zan gyarata ne." ya fada afili, kuma saina aureki, insha Allahu yau dinan basai gobe ba."
haka ya wuce bunza cike da tunanin, yarinya tana nema ta juya shi, yana mamakin yadda ya biye mata, shima ya koma sa'anta, amma lokaci yazo dazai goge raini tsakaninsu.
Karfe sha daya saura suka hadu jega, harma su muzamil sun isa, su kawai ake jira. Shatu babu abunda zatace, dan dama ai yarinya a hanunta take, dan haka aka shirya in ankidar da sallar jumma'a sai a daura.
Haka kuwa akoyo, ana kidar da sallar jumma'a aka daura auren jafar alkali bello da Aisha dalhatu. Mijin shatu mal. Tasi'u shine ya zama wakilin Aisha, shikuma Baba sabo shiya wakilci jafar. Haka aka tashi, anata zuba addu'a. Jafar ji yake kamar aranar ya fara aure, sam baya shakkar yaga inna, dan dai Allah ne yayi zai lamince duk wani abu dazai biyo baya, amma bazai rabu da itaba.
Wajajen karfe uku suka isa kebbi, harda Baba sabo dan yace, yanaso yaga inna da kansa ba sako ba.
Tana kicin kuwa suka shigo, da sauri ta isa gunsu tana gaishesu, yadda ta lura da yanayin Baba sabo tasan akwai muhimmin daya kawoshi, kuma abun ba karami bane, dan tasan halin kawun nata, tun suna yara shikam suna tsoron shi, dan baya daukar raini, toh amma meya faru haka da bata saniba? Ta nemi wuri ta zauna, bayan ta gama jera abinci agabansu,, tana kara gaishesu.
Baba sabo ya buda baki zaiyi magana, saiga jafar, yace yauwa, dama inaso inyi maganar kana nan, fatima." ya fada, inaso in fada miki ta farin ciki."

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now