50

2.8K 172 0
                                    

KALLON KITSE

Haka ta tashi ta wuce dakin ta. Shikuwa duk hankalinsa ya tashi, ya zaiyi da ransa ne, wai me yayiwa inna da bata kaunarsa? Tuni idonsa sukayi jajir, kamar gauta. Ya mike ya fice.
Motarsa ya shiga kai tsaye makarantar su uwani ya nufa. Kowace ta tsurawa motar ido dan ta hadu, gashi wanda ke cikin motar ma ba abarshi abaya ba, sarai uwani ta ganshi kuma ta gane shine, toh amma ta kauda kanta gefe daya, suka ci gaba da hirarsu da lawisa, shima ya gane manufarta, saiya share ya bude motar, idonsa sanye da spider space, ina nufin irin madubin nan mai makalewa a idon mutum, yayi kyau sosai dan dama yana sanye da farar rigar nan da wandon kakinsa.
Duk wurin shi ake kallo, lawisa ta dubi uwani, ke wancan ba uncle bane kuwa? Uwani da tuni gabanta ke faduwa tace, haba dai, wane uncle kuma, shida baya gari."
toh nidai gashi nan dan bazaki cemin ban san uncle ba...."
hamza ne ya katse musu maganarsu, "ku tashi mu tafi." su duka suka kalleshi, tuni hankalinsu ya koma gun hamza dake yi musu magana, sannan mamaki cike a fuskarsu, "yaya yaushe ka shigo garin namune? Ya amsa idonsa akan uwani. Itama kallonsa take yi cike da kaunarsa a idonta, gashi shima yayi kyansa, duk da hankalinta baki daya baya gun hamza, yana gun uncle din nata, ta sani sarai komai na iya faruwa, amma tayi karfin hali suka tashi, suka shiga motar hamza.
Jafaru kuwa in ransa yayi dubu ya baci, dan ma ya manna glass a idon nasa, da ba haka ba da abun yayi muni. Tuni ya koma gun motarsa, ransa a bace yabi bayan motar hamza, saida yasan yanda yayi ya wuce hamza, yasha gabansa. Da sauri hamza ya ja burki ya tsaya, dama shima hamza ba a barshi abaya ba gun rugima, dan haka da sauri ya fita cikin motar cike da fushi, shima jafar da fushin ya fito, suka tsaya sunawa junansu kallon tsab! Har na kusan minti uku, sannan ne hamza yace mallam ya zakamin haka, ko kan titin na gidanku ne? Jafar yayi murmushin mugunta, sannan ya cire space din idonsa, idon nan nasa kamar garwashin wuta, "menene dalilinka na daukar min mata? Tambayar yazo masa a bazata, "mekake nufi, taya za ayi in dauko matarka?
Matata na cikin motar ka, bance mu tsaya muna exchange word ba, ita kawai nake so ta fito mu tafi." ya juya ya kalli inda su lawisa suke yace "dama akwai matarsa a motar nan, ya tambaya yana kallon 'yan matan guda biyu.
Lawisa da kyar ta iya magana, saida ya kara maimaitawa acikin tsawa, sannan tace, eh akwai."
ban ganeba?
"yaya gaskiya ya fada uwani ce matar tasa." hankalin hamza ya tashi sosai, ya kara matsawa kusa da kofar uwani, "hakane uwani wai wancan mijini ne? Tuni hawaye ya cika mata fuskarta, in banda tausayawa hamza da bakin cikin abunda jafar ya aikata shike damunta, bata iya cewa komaiba, sai shima jafar ya matso inda hamza yake yace, kaga kada in kara ganin matata a motarka dan in fada maka she is carring my baby, so ina so inja maka kunne, kar in sake koda wasa inga hakan ta kara faruwa."
in hakan ta faru fa me zakayi? jafaru ya kara yi murmushi, na inya san yayi nasara akan abu, amma baice komaiba ya bude motar inda uwani ke zaune, ya jawo hannunta dole ta amince saboda tasan halinsa, inma taki yana iya daukanta, ya kuma dauki jakarta, har saida ya bude mata gaban motarsa ta shiga, ya zagayo ya bude tasa, sannan ya dubi hamza yace, da kuwa ka gane kurenka, idan har na kara ganin matata a motarka." ya shiga ya wuce ya tayarwa hamza kura.
Jikin hamza yayi sanyi lamai, a haka ya daure ya shiga yabar wurin.
Cikin motar ba wanda ya kara cewa ci kanka har saida suka isa gida, da sauri uwani ta bude kofa ta fita. Ji tayi ya riko hannunta, "ina zaki? Zo nan saikin fadamin dalilin wulakanta ni."
nan da nan ta kidime, tana fidda hawaye tare da kokarin kwace hannun nata daga rikon da yayi mata. Suna shiga daki ya cire mata hijabi din dake jikinta, yana yi mata kallon kurillah, "wancan dan iskan shine hamza ko? Yayi tambayar cike da bacin rai, bata taba ganinsa hakaba, duk irin fushinsa na yau yafi na kullum, ta marairace fuskarta kayi hakuri. Ya dubeta kada in sake ganinki da wannan mutumin." da sauri ta amsa toh.
Ita dai so take ya saketa, dan rikon da yayi mata, ya koma ya kulle kofar da key, dan Allah nace kayi hakuri, bazan sake ba.
Ai na hakura, ya fada yana cire shirt dake jikinsa, 'kijirani inyi wanka. Ya shiga bandaki, dole ta zauna kan kafet din falon, inka ganta kamar wadda aka sato, gashi batada ikon yin ihu inna taji, dan gabaki daya ya gyara dayan sashen dake cikin gidan, ya maida shi salfcontent, gashi ya shirya wurin sosai, ita dai ta zare ido sai kallo take yi, bata san lokacin da aka gyara sashen ba. Yayi mata kyau a ido gashi ya makala hoton mahaifinsa data inna a falon, kujerun falon su suka fi yi mata kyau.

Da karfet ya shirya falon da kalar lemon green, sai aka dan jefa orange kala aciki, gaskiya falon ya kayatu kwarai ainun.
Shigowarsa falon ya katse mata tunani, "meye haka kin wani takurawa kanki? Ta daga ido ta dan dube shi, yana sanye da gajeren wando da singileti fara tas! Yazo ya riko hannunta, 'haba baby ki saki jikinki mana, gidan mijinki fa kike."
"ni zan shiga gun inna.
Wace inna kuma? Sai naji bugun zuciyar dan cikinki, sannan zaki bar wannan wurin."
ta dan tsuke fuskarta, "wane irin da kuma? Don Allah ka bari in tafi, Allah yunwa nakeji."
da gaske toh ki bari in dan duba ki mana, kafin ki tafi, ke ko irin tarba da akewa miji ke bakya yi, munfi wata biyu bama tare amma ko nuna min farin cikin zuwa na?
Ai kana da matar da zatayi maka wannan nikuma aro ce a gareka." murmushi yayi sannan ya jawo ta dakin barcin shi, "zo kiga wani abu." dakin barcin nasa ma yayi kyau, gado ne har gado aciki, komai an shirya shi yadda ya kamata, ji tayi ya sureta sai tsakiyar gadon, wani sabon kuka ta saki, sai dai shi baiko damuba, data gano abunda yake shirin yi, saita mike da sauri tayi sa'ar sauka daga kan gadon, a guje ta nufi kofar ta bude tayi falo, ya biyota yana fadin 'yar tsoro, ba komai zanyi miki ba, ai nasan bakya jin dadi. Nidai ka bude min in fita." kuka data keyi ba sassauci ya bashi tausayi, ya bude mata kofar ta fita, da sauri ta fice.
Tun daga wannan rana shiyake zuwa daukota daga makaranta, har ta gama rubuta jarabawarta, sannan laulayi ma ya mata sauki sosai, dan harta fara ciye-ciye.
Shikuma jafar tunda ta gama rubuta jarabawarta ya wuce kaduna.
Sam bai yadda sun zauna da inna ba, dan ko sun zauna ba hirar daya ke so take masa ba.
A kaduna kuwa, marliya sai addu'a
rayuwa kenan, inka ganta saika rantse da Allah ba ita bace, abun har yaso ya zama mata tabin hankali. Sau dayawa inka sameta saika ji tana ta surutai bartai, idan ma ka saurara bazaka gane abinda take fadi ba, Allah ya sauwake (ameen)
sabo da hakane randa jafar ya dawo, sun shigo tareda bashir, yana bashi labarin abun farin ciki daya sameshi, "kai aboki wallahi ako da yaushe inajin dadin shawararka, gashi a yau na tashi matata nada ciki."
kai don Allah kace munyi kusan shan suna?
Eh! Mana sai dai tana wahala fa, tausayi take ban wallahi, dan ma tanada karfin hali ahaka take rubuta jarabawarta.
Da kyau, ashe harta gama kenan?
Alhamdulillahi, ta gama sai dai kai har yanzu inna taki bani hadin kai, kasan cewa tayi inta haihu, saina saki uwani? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ka bata hakuri kuwa jafar?
Uhm wane hakurine ban bada ba, tun abun na damuna harna sa ido, yanzu Allah kawai nasa agaba.
Daga bayansu sukaji an kyalkyale da dariya, da sauri suka juya suka ga ashe marliya ce, gashin kanta a tsaye kamar shuka, sannan kayan jikinta kamar wadda tai shekara batai wanka ba, fuskarta kuwa baza ce ita bace, dan yadda tai baiki.
Ta kyalkyacewa da dariya. Har tana dukawa, su kuwa ido suka sakar mata, "me naji ka fadi doctor? Matarka ciki ne da ita? Hummm lallai matarka ciki ne da ita? Saita kara kwashewa da dariya. Jafar ya juya mtss! Zo mu shiga gida bashir. Da gudu ta karasa ta sha gabansu, "ba inda zaku, saina fada muku gaskiya, nice...nice." ta kara maimaitawa tare da zare idanunta, "wadda ba a gani a kyale, nice wadda nake yin abunda naso a rayuwata, idan ina son abu dole ne in sameshi, kota hali kaka. Kasan ya akayi na sameka? Ta fada tana kallon fuskar jafar, shikuwa tsura mata idonsa yayi, ina son sani marliya, dama abunda naketa jira kenan ko baki lura ba?
Toh yanzu zaka ji..."
bashir ya katseta toh ke mu isa falo mana kada...
Ta katseshi ba ruwanka gwani, bada kai nake magana ba.
"watch your mouth, marliya kada ki..." ta katse shi da cewa, "na bada kaina gun boka shanshani dan kawai in mallake ka jafar, saida yayi amfani dani sau ashirin da bakwai a yini daya, sannan na mallakeka jafar, ina sonka doctor, ban taba zama nayi tunani da namiji ba sai kai doctor, saboda hakane sonka ya makantani, nayi abunda ban taba yi arayuwata ba." kuka ta saki mai ban tausayi. Duk jikinsu yayi sanyi, duk da bawai tausaya mata sukayi ba, illa takaici data basu, a take jafaru yace toh na sakeki saki uku! Babu aure a tsakanina dake har abada, na sakeki..." haba aboki ba ayi haka ba.
Haka kai ka gani, amma bazan iya zama da karuwa ba, na dauke shi tuntuni a matsayin kaddara, dan inba kaddara ba, da bazan dauki tsohuwar kilaki a matsayin matata ba. Yana gama fadin haka, ya kama hanyar falonsa, da sauri ta rike masa kafa, tana kuka doctor ina sonka! Kayi hakuri na gano kuskurena." da karfi ya tureta, saika ce dabbar data gudiri mutum, nace na sakeki ko bakiji ba? Bana sonk ni! Sannan inkin manta in fada miki, in anyi saki uku babu aure tsakanin ma'aurata, kayan dake cikin gidan nan na baki, in kina so kisa mota tazo ta kwasan miki, zan baki daga yau zuwa karfe tara na safen washe gari, idan na dawo na sameki cikin wannan gidan, wallahi saina kasheki."

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now