Ashirin Da Hudu

1.5K 184 7
                                    

Karar oven din sukaji dukansu, wanda hakan yayi sanadiyyar tsayuwar maganarta. Dama tamkar jiran duk abunda zai dauke mata hankali take, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta share hawayenta. Bata yarda ta kalli inda yake ba Ramlah ta mike taje ta fiddo da cookies din, tasowa yayi shima ya tsaya gefenta. Yakai hannu zai dauka ta buge hannunshi tana dariya, "Aikau da daga yau baka kara taba abu me zafi ba, ka jira ya dan huce ko?" Dagowa tayi da jajayen idanunta tana kallonshi ga wani murmushin karfin hali da take.

Shidai Rayyan kallonta kawai yakeyi, amma shi kadai yasan irin abunda yakeji a zuciyarshi. Yasan ba yauce rana ta farko daya fara ganin kukan Ramlah ba, amma irin wannan kukan bai taba ganinshi ba. Haka zalika maganganun da takeyi bai tabajin irinsu a bakinta ba. "Zaki sakashi a fridge ne? Bari naga idan akwai lemu, zakici kema ai ko?" Juyawa yayi ya nufi hanyar fridge din ba tare daya jira amsarta ba.

Saida Ramlah ta juye dukansu saman tray sannan ta juya da wanda ta dibar masu a plate, kan table din ya aje kofi biyu ga kuma lemu a gefenshi. "Baba lemu me madara?" Ta tambaya tana rabawa ta gefenshi. Rayyan tsayawa yayi kawai yana kallonta, yanda taketa kokarin ta danne damuwar data taso mata. Ba sai ta fada ba, amma daga ganin yanda take da kuma farkon haduwarsu da Lubnah ya tabbatar mashi wannan kyakywan tarihin nata bai kare da jin dadi ba.

Juyowa tayi da hollandia a hannunta. Zama tayi saida ta zuba masu a cups kafin har zata zauna ta mike, "Bari in wanke fuska ta, duk nayi muju muju da hawaye gashi dama ban iya kuka ba." Yar dariya tayi, shidai Rayyan kallonta kawai yake amma shi kadai yasan irin zafin da ranshi yake mashi a kanta. Ji yake inama ace zai iya yaye mata wannan damuwar da take ciki? Dan ko bata fada ba yasan tana cikin damuwa.

Wanke fuskar tayi ta dawo tana kallonshi, "Idan ban tashi da wuri ba kace ma Lubnah ta debi cookies dinnan ta tafi dashi, ta rage zama da yunwa. Kamata yayi ma ka rika tabbatarwa tana cin abinci wallahi." Dan bata fuska tayi, ji take kamar ta mishi maganar irin san da Lubnah take mashi amma tafi san yaji hakan daga bakinta.

Murmushi yayi kafin ya fara cin cookies din ganin itama ta fara ci, dan tsoro yake ya kune harshe, babu abunda ya tsana kamar kunar harshe. "To ni kuma bawan Allah da babu me kula dani ko? Sai in mutu da yunwa." Hararar wasa ya mata, murmushi ta mishi tana girgiza kai.

"Kula da kai ai hakkin Lubnah ne, indai kula ne saima kace ta daina haka nan, baka da wannan matsalar." Bai kai da bata amsa ba wayarshi dake aljihu ta fara kara, ganin sunan Maryam baro baro yasa wani murmushi subuce mashi, nan take wani tunani ya darsu a zuciyar Ramlah, to kodai yana da budurwa ne?

"Meralli ta Malam Audu." Da yar dariyar wasa ya fara, sai a lokacin ta tuna ya taba fada mata sunan kanwar shi, kila ita ce ko? To amma kanwa ta kirashi cikin dare haka? Yanzu karfe nawa? Saidai budurwa, kila wasa yake mata.

Rayyan yana sane da irin kallon da Ramlah take mashi dukda cewar bazai iya gane takamaimai dalilin kallon ba amma yasan tunanin da take bai wuci na wa zai kirashi ba cikin tsohon daren nan. "Maryam ga Ramlah ku gaisa, cookies ta mana me dadi bakiji ba..."Bai ida magana ba ya cire wayar daga kunnen shi yana mika ma Ramlah, "Duk da dai diyar mijinta ta mawa mu albarkaci mukeci." Yar harararshi Ramlah tayi kafin ta amsa wayar.

"Hello Maryam? Ina yini ya gida?" Ta gaidata tana me murmushi, idan mutum yaji muryarta bazai taba cewa bata dade da kuka ba, idanunta ne kawai har yanzu a rine suke kamar jan fenti.

"Wai ina yini, Ya Rayyan fa yace shekarunmu daya." Da dariya Maryam ta ansa mata. "Ya kike ya gida?"

Itama Ramlah dariyar tayi, "Lafiya lau, Maryam. Ya Yan biyu?" Yar fira sukayi dukda maganar ba wata ta arziki bace ba, dan madai daga dukkan alamu Maryam tana da saurin sabo da mutane, dan duk yanda Ramlah taso ta zille sai janta da magana take. Nan take fada mata next week zata dawo Nigeria shine ta kirashi ta fada mashi ya mata alkawarin zai daukota daga airport. Koda suka gama magana da Ramlah data mika mashi yar magana kadan sukayi suka aje wayar.

"Ramlah bacci nakeji." Abunda ya furta kenan yana dan bata fuska yana kallonta. Ita tsayawa ma tayi tana kallonshi kamar wani karamin yaro sai can ta fashe da dariya, "Yau naga ikon Allah, to da hanaka bacci nayi? Ai kaci ka koshi ko? Saida safe."

Shima murmushin yayi ganin yanda take dariya tana magana, babu abunda yakai kasa wanda yagama kuka dariya. "To ai ni bakice in dauki cookies din naje dashi wajen aiki ba ko? Ko ni banda bakin cin abinci?" Mikewa tayi tsaya tana girgiza kai, "Cookies dai gashi nan, inma ya kare sai nayi wani ni ba bakuwar zafi bace ba. Amma dai a ajema diyata."

Mikewa yayi yana murmushi, "To masu diya munji, wai a haka ma yar mutane ce, idan taki ce halak malak ai mun shiga ukku da gori. Nima me diyar zanje in nemo sai muga ta gori."

Hanyar fita kitchen din ta nufa bayan ta dauki ruwa dan akwaita da shan ruwan dare, "Ashe ma sai ka nemo ta mutane, kayi zuciya kayi taka." Dariyar mugunta take mashi ganin yanda ya bata fuska. "Zan rama, Ramlah." Daga kai tayi tana dariya, "Koma dai menene." Saida ta rufe kofar bayan ta fita sannan ta koma nata dakin, sallah tayi tana rokan ma dukkan mutanen da suke da mahimmanci a rayuwarta gafarar Allah, ta dan zubda hawaye akan Hanan amma daga lokacin da tunanin Abban Hanan ya nemi zuwa ranta tayi hanzarin kauda shi.

Bata tashi da wuri ba dan bata kwanta da wurin ba. Koda ta tashi hatta Mama babu wanda yake gidan, tana fita taga an aje mata cookies dinta cikin roba ga rubutu nan daga gefe. 'Kin manta baki kwashe ba ko? Nasan aso diyar mutane ta ci abu me lafiya. Kuma na diba dukda ba'ace na diba din ba.' Wani irin kawataccen murmushi ya subuce mata wanda batasan lokacin datayi shi ba. Ko ba'a fada ba tasan Rayyan ne. Abinci taci sanna ta koma daki tayi wanka.

Tana cikin editing pictures dinta wayarta ta fara ringing, ganin sunan Lubnah ne yasa wani kyakyawan murmushi kan fuskarta. "Na dauka zaki tadani kafin ki tafi?" ta fada tana murmushi.

"Na isa na tada amaryar Dr? Ai mun gafara, godiyar cookies zanyi dama kuma ince maki ki shirya masu aikin shagonki na nemanki. Ni ban taba ganin mutun irinki ba, halan kinma manta da shagon ko?" Dariya Lubnah takeyi, ita kuwa Ramlah tunaninta bai wuce ashe ya fada mata ba.

"Wai amaryar Dr, ni dai dan Allah ku daina kar mala'iku su amsa ku. Haba dai? Driver yana waje ko? Bari naje."

Saurin tarar numfashinta tayi, "Sun fita da Mama gaskia, amma Rayyan yace mun ya manta wasu takardu a gida yanzu zaizo ya dauka, ki kirashi idan ya iso ya miki magana kuje tare ko?" Kammala magana sukayi nan Ramlah ke fada mata cewar za'a kawo mata Hafsah weekend, taita janta tana dariya kafin suka kashe wayar.

Kiran wayar Rayyan tayi, saida kiran ya kusa tsinkewa kafin ya dauka. "Sorry Ramlah, ina can neman documents din banga kiran ba. Kin shirya ne?"

Mikewa tayi tsaye bayan ta kashe system dinta tana warware gyalen dake kanta, "Eh, ka gansu ko?"

"Aa wallahi, ko zakizo ki tayani nemansu dan Allah? Sauri nake wallahi, nan da minti talatin zamu shiga meeting kuma dole saida su, gashi har da directors din da sukazo daga Lagos, idan nayi mistake na bani da Baba."

"Subhanallahi, gani nan bari nazo." Jakarta ta dauka ta maida wayar ciki kafin ta fita daga dakin, tazo fita falon ta hadu da mai aiki sai take ce mata, "Dan Allah yanzu zanje shagon na dawo, babu kowa ki kula da gidan."

Saida ta fita tsakar gidan ta tuna ita bama tasan inda part dinshi yake ba, har zata dauko waya ta kirashi ta hango wata hanya, binta tayi nan kuwa taga hadadden apartment guda me zaman kanshi. Da sallama bakinta ta shiga parlour din, "Gani nan, Ramlah, shigo!" Daga dakin yayi magana, har tayi taku daya sai kuma ta tsaya. Amma tunawa da taimaka mashi zatayi ya dubu takardu, babu wani tunani a ranta ta karasa dakin, dukda cewar komai na wajen ta san Mama ce ta saka amma hakan bai hana dakin yi mata kyau ba, shi kuwa yana can cikin drawers sai dage dage yake.

Juyowa yayi jin sautin tafiyarta, "Ga wasu files can, Ramlah, duk wanda kikaga 'The Elephant Project' a jiki shine sai ki fada man kawai, kinji?" yana fadin haka ya juya, amma sai bayan ya juya ne ya tuno abunda ya gani a fuskarta. Fayau take babu komai amma tunda yake bai taba ganin kyan wata ya mace ba kamar Ramlah, amma a halin yanzu takardun sune gabanshi, anjima ya cigaba da tunanin daya darsu a ranshi.

"Ka ganshi nan fa gefen system dinka, Rayyan." Ta fada tana dago da file din, wata irin ajiyar zuciya ya sauke, yana juyowa yaga tana mishi murmushi da kyakyawar fuskarta, Rayyan bai san lokacin daya mata nashi murmushin ba.

MIJINA NE! ✅ Место, где живут истории. Откройте их для себя