Da hanzari ta tsallaka titin dake gabanta, gudu take kar ace ta makara, kar wani abu ya samu tilon y'arta. Yanzu idan wani abu ya faru da Hanan ina zata saka rayuwarta? Hawayen dake zubowa saman kuncinta tayi kokarin sharewa a hankali. Zata daure, Insha Allahu duk ynda zatayi dole ne ta sama ma kanta yanda zata sama ma Hanan lafiya.
Tsayawa tayi bakin kofar asibitin tana kallon shige da fice na mutane. Wasu suna fita da ihu da kururuwa alamar wani nasu ya rasu, wasu kuma suna dariya alamar lafiya ta samu. Wasu kuma suna shiga cikin rudu, firgici da tunanin yananin da dan'uwa ko yar uwarsu take ciki. Duniya kenan, nan ita yanda take a hakan tana ji duniya ta mata kunci, wani nacan yau yake farin cikin da bai taba irinshi ba. Share hawayenta ta karayi tana mai kokarin fitar da murmushi saman kyakyawar fuskarta, wacce a yanzu idan ba mutum ya kura mata ido ba bazai taba cewa tana da kyau ba.
Takawa tayi har dakin da aka kwantar da Hanan. Ko yanzu taga likitar data kawosu dakin nan sai ta kara gode mata, dan baccin ita da batasan abunda zatayi da ranta ba. Dan kila ko ciwon Hanan bai dauki rayuwarta ba, to allergy din da take fama dashi sai ya dauki rayuwarta. Hanan bata san mutane ko kodan, idan a waje mutum ya wuce biyar to tabbas yanzu zata fara numfashi kuraje su fara fito mata, musamman yanzu lokacin zafi, gashi indai maganar zafi ake akazo Katsina an gama magana.
Saboda Hanan ko fita batayi...kukan dataji tanayi ne ta window yasa ta katse duk wani tunani da take ta ruga ta shiga dakin. Da hanzarinta ta karasa gadon Hanan tana me rungumo ta a jikinta, "Hanan, har kin tashi baccin? Sannu, ya jikin?" Tambayar da take mata kenan tana tallabota a hankali kamar wacce tsoron ta fashe.
"Akwai zafi Ummi, ban iya numfashi sosai," fadin Hanan kenan hawayen na fita tana wani kuka a hankali wanda dagaji kasan ba karamin jin jiki take ba.
Saurin maida hawayenta tayi tana murmushin karfin hali, "Karki damu kinji, Hanan? Insha Allah zaki samu lafiya, ai yau da sauki kadan ko?" Duk yanda taso ta daure ta nuna ma Hanan cewar babu wani abu, duk tazo magana sai ta kasa.
Sauran kashe da tsokar daya rage a jikin yar shekara biyar shine take girgizawa a hankali tana juya kanta, "Ummi ance idan aka mutu ba'a jin zafi ko? Bacci kawai zanyi kafin a kaini makarantar Annabi Ibrahim."
Hawayen da take kokarin maidawa ne suka zubo, duk idan Hanan tayi maganar nan sai taji zuciyarta ta kare. Hannayenta ta riko a hankali tana mai sumbutarsu a hankali, hawayenta na diga a sama, "Kinaso ki tafi kibar Ummin ki ne, Hanan? Ni in kika tafi ya kikeso inyi?" Kawo yanzu kuka yaci karfinta, ta rasa duk fadin duniya inda zata saka rayuwarta.
"Ummi ki daina kuka, kinji? Idan ina nan nike saki kuka, amma idan na tafi ai zasu barni inje inga Abba na ko?" Wani irin gunjin juka ne ya kubce mata, kasa tsaida kanta tayi sai kuka take rizgawa babu kama hannun yaro. Tasan a fadin duniya akwai mutane dayawa wadanda suka fita shiga kunci, amma kuma tasan abunda takeji a cikin ranta yafi karfin misali.
Nurse din databa ajiyar Hanan kafin ta fita ce ta shigo, da hanzari ta karaso wajenta ganin irin kukan da takeyi. "Subhanallahi, yanzu Ramlah tsakani da Allah ba munyi dake ki daina kukan nan ba? Shifa yaro yanada wani abu, idan taga kullum kin tasata gaba kina kuka sai tayi tunanin itace silar damuwarki..."
Ramlah bata jira ta gama magana ba ta dago idanunta da suka rine sukayi ja tsabar kuka da kuncin da yake kwance male male a kasan zuciyarta. "Ya zanyi? So take itama ta tafi ta barni, Nurse. Idan na rasata shikenan bani da kowa?" Yanda muryarta take karewa ko bakayi niyya ba sai ta baka tausayi.
"Bazan tafi ba indai bakyaso in tafi, Ummi. Ki daina kuka kinji?" Hanan ce ke magana tana dago yan hannayenta wanda babu sauran tsoka jikinsu, daga fata sai kashi.
"Kinji ko? Sannu Hanan kinji? Rabu da Ummin ki saurin kuka ne da ita. Ramlah ina fatan kin samo? Muje dai waje muyi magana." Dan lallabata ta samu tayi kafin tabi bayan nurse din zuciyarta tana bagawa. Ya Allah kasa ba wani mummunan labarin zasu fada min ba, abunda ta ayyana a ranta kenan kafin tabi bayan nurse din har nurse station tukun suka zauna.
"Ramlah ina fatan zaki iya biyan kudin ko? Dan a bayanin da Dr Zubair yamun yau da safe, gaskia Hanan tana bukatar surgery dinnan yau latest ko gobe da safe. Hole din dake zuciyarta yayi tsanani dan dakyar jini yake circulating a jikinta..." bata karasa ba Ramlah ta dora hannu saman kai ta fara salati, shikenan ita rayuwarta, yanzu tata tazo karshe kenan? Dan in har ta rasa Hanan, babu ita babu rayuwa a doran kasar nan.
"Yanzu ya zanyi? Bari naje..." zumbur ta kara mikewa tana kallon nurse din da tsantsar tashin hankali. "Dan Allah kiyi hakuri ki kara kular man da ita, zanje na dawo." Bata jira komai ba ta fice daga asibitin, dukda cewar marece yayi hakan baisa ta saduda ba ko tayi tunanin bazata iya samun kudin aikin Hanan ba.
Gidansu ta koma, dan akurkin dakin da suke kwana ta zube tsakiyarshi. Juyawa tayi tana kallon dakin a ko ina babu abunda zaka daga kace zaka siyar kuma wai har ka samu me siye. A tarkacen dake dakin ma babu abunda zaiyi darajar dubu biyu.
Jikin bango ta koma ta rabe, tana me kwantr da kanta saman guiwowinta. Kuka takeso tayi, amma komai nata ya tsaya, numfashin ma dakyar take yinshi. Tunanin rayuwarta takeso tayi amma ko kadan babu wani abu mai dadin tunawa a rayuwarta. Kiraye kiraye sallar magriba shi ya maido da hankalinta ta mike tsaye zumbur.
Kar ace dare yayi kuma bata san yanda zatayi ba. Dakin ta kulle dukda cewar ko barawo ya shigo babu abunda zai samu wanda zai amfane shi. Kamar yanda ta saba, duk inda tasan sun taba zuwa sun hadu da wani wanda suka sani wanda take tunanin zai iya taimaka masu saida taje. Kafafunta har sunyi kanta saboda tafiyar kasa, bata ma tunanin cikinta dan in har bata samu kudin nan ba yau bata san inda zata saka rayuwarta ba.
Karshe dai dataga alamin dare yayi sosai hawaye ne kawai ke zubar mata ba tsayawa ta nemi hanyar komawa asibitin. Kila idan ta rokesu suyi mata a bashi zata biyasu daga baya. Ko aikin shara ne zata masu karsh rika biyanta albashi. Da wannan tunanin ta karasa asibitin saidai tun kafin takai kofar dakin ta lura cewar akwai mutane dayawa, ita ba dangi ba balle ace dubiya suka zo mata.
Da gudu ta karasa dakin amma ganin likitoci ne saman kan Hanan yasa taja burki ta tsaya. Komai na jikinta tsayawa yayi, dif kamar daukewar wuta. Daga bakin kofa ta tsaya tana kallon duk abunda sukeyi, dan kawo yanzu sun saka dan tube wanda zai kai mata numfashi. Kallonsu kawai takeyi babu abunda yake motsi a jikinta, tana jira taga me zai faru da rayuwarta. Kamar a mafarki taga idanun Hanan wanda suke rigi rigi kamar zasu rufe, rufewa ta har abada sun dago sun kalleta. Da alamu ma jikinta baya responding ma treatment din da ake mata.
"Ummi..." dukda hayaniyar likitoci da nurses din dake cikin dakin ana karba da mayar da kayan aiki, taji sanyayyar muryar Hanan tana kiran sunanta. Kamar wacce kwai ya fashe mawa a jiki haka ta taka har bakin gadon, koda doctors din suka lura ita Hanan ke kallo sai suka bata wuri taje har bakin gadon ta zauna ta riko hannayen Hanan. "Kice su daina, Ummi, tafiya zanyi suna kara sawa ina jin zafi." Har wani likita yazo zaiyi mata allura Ramlah ta rike hannunshi tana girgiza kai.
Babban cikinsu ne yayi ma sauran da alama su tafi kawai su kyalesu, iyaka sunbar nurse daya wacce zata lura da vital din Hanan din. "Hanan, karki tafi dan Allah..." jin muryar takeyi kamar ba tata ba, jikinta ko ina ya kame ya zama tamkar kankara, tsoro takeyi, fargaba ce fall ranta.
"Ummi ki dauke ni a jikinki, gadon nan baya mun dadi." Ramlah a hankali ta dauketa ta dorata kan cinyarta kafin ta kwantar da ita saman kirjinta. sai a lokacin hawaye suka balle saman kuncinta, wani irin duhun bakin ciki ne yayi kwance male male a kasan ruhinta. "Ina sanki Ummi, nasan Abba shima yana sanki Ummi. Ki daina kuka dan Allah." Da yan kana nan hannayenta haka ta dago tana sharema Ramlah hawayenta. Dukda cewar Ramlah ta lura da yanda yanzu numfashinta kiris ya rage ya tsaya gashi ECG machine din ta fara kara kuma nurse din ta ruga dan kiran likitocin, rufe idanunta kawai tayi ta rungume Hanan tsam cikin jikinta.
"Ina kaunarki Hanan, dan Allah..." bata karasa ba taji jikin Hanan ya saki yayi sanyi gaba daya. Ba sai ta jira likitoci sun fada mata ma'anar hakan ba. Ba wannan bace farkon ganin ta ba kuma bazata ce wannan ce mafi kunci ba, amma tabbas wannan itace wadda har itama ta komama nata mahaliccin bazata taba mantawa da ita ba. Kare rungume gangar jikin Hanan tayi a jikinta tana fashewa da wani malalacin kuka, "Allah yasa kin huta Hanan, Allah ya kyautata makwancinki."
ESTÁS LEYENDO
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...