nafisatuu I love you❤️ As promised.
Ko kallonshi bata karayi ba ta wuce cikin gida, dan ita abunda yake damunta ma yafita karfi. Rayyan ido kawai ya bita dashi har saida ta bace kafin ya wuce ya tafi bangarenshi. Tunani yake wai ita wannan wace irin mutum ce. Yau zai ganta gata nan dai kamar ko wane mutum, wani lokacin ma cikin kwana biyun nan tunda ta fara zuwa koyan photography ya lura ta dan koma daidai, amma yau kuma zai iya cewa ta koma ruwa.
Ramlah tana shiga falo ta iske Mama zaune kan kujera tana kallo, da guntun murmushin da ya kasance wanda tayi amfani dashi wajen maida hawayenta ta karasa wajen Mama ta zauna. "Ina yini, Mama? Ana hutawa?" Ta furta a hankali tana zama kan kujera.
Juyowa Mama tayi da fara'arta. "Ramlah har kin dawo? Nama dauka tare da Lubnah zaku dawo ai."
Girgiza mata kai tayi, "Bata kammala ba, shine Dr Aliyu ya taho dani gida kawai. Bari inje inyi wanka sai na fito, ko akwai abunda za'ayi maki ne, Mama?" Ta tambaya tana mikewa tsaye, dan halin da take ciki babu abunda take bukata daga wuce ta kebe daga ita sai kanta sannan kuma tasha kukanta san ranta.
"Aa ba abunda zaki man Ramlah. Amma dan Allah ki fito muci abinci tare kinji? Bansan zaman dakin nan naki." Dan murmushi tayi ta amsa Mama kafin ta nufi hanyar benen dan ta wuce dakinta. Har kasan ranta take jin Mama da Lubnah, dan yanda suke mata mutum bazai taba cewa ita ba yar'uwarsu bace ta jini.
Tana shiga daki ta tabbatar a rufe yake kawai ta fashe da kukan da saida kirjinta ya amsa. Yanayin yanda taji lokacin dafa rungumi Hafsah shine ya fado mata a rai. Ji take tamkar ita ta haifi yarinyar nan, kuka take tanajin inama ace Hanan dinta bata rasu ba? Da yanzu bata zo Abuja ba, da tana can ita da diyarta suna rayuwarsu.
Wai shin kowa haka yakeji idan ya rasa wani nashi? Dama haka sauran mutane suke shiga kuncin damuwa idan suka nemi wani nasu suka rasa? Mutuwa ta masu yankar kauna? Tunani take da ace tana da kudin maganin Hanan da ta mutu kuwa? Saurin kauda wannan tunanin tayi domin gudun sab'ama Allah.
Batasan lokacin data dauka tana kuka ba saidai taji karar kwankwasa kofa, "Aunty Ramlah, Mama tace ku take jira kuci abinci." Al'adar gidance, duk ranar juma'a sukan hadu suci abinci tare. Batasan ko haka sukeyi ba tun kafin tazo, amma ita dai tunda tazo haka sukeyi koda kuwa basu da lokaci a ranar to sai sun k'uk'uta sunzo sunci abinci tare.
"Kice mata gani nan fitowa." Da hanzari ta fada bandaki tayi wanka kafin ta fito ta saka wata doguwar riga mai laushi. Ita har mamakin yawan kayan da Lubnah ta siyo mata takeyi, dan ita wasu kayan ma batasan ranar da zata sakasu ba. Barta dai da doguwar riga, dan cika duk tafi saka dogayen rigunan, su kadai ma ta taba sawa. Satin daya gabata ma sukaje aka karbo mata dinki, amma tunda tama kayan kallon farko ta saka durowa bata kara kallo ba.
Saida tayi sallah kafin ta sauka falon, tana sauka ta iske har Rayyan da Lubnah sun hallara wajen suna dan fira, wanda kullum firar tasu bata wuce ta aiki sai daidaikun lokuta ne suke maganar rayuwa. Dan murmushi tayi kafin ta zauna, wacce kujerarta tana kallon ta Rayyan.
"Lubnah har kin dawo? Banji duriyar ki ba." Ta fada tana kallon Lubnah, amma sai kauda ido takeyi dan kar su lura cewar tayi kuka.
"Nazo shiga dakin naji kina kuka, Ramlah. To me zan maki? Sai na kyaleki kiyi ki gama tukunna." Daga gani ran Lubnah bai mata dadi ba, batasan wannan damuwar da yawan kukan da Ramlah takeyi. Tasan kukan rashin wani naka kusan zaa iya cewa wajibi ne, amma kuma daukar kaddara ma wani abu ne.
"Kiyi hakuri, Lubnah, bazan sake ba."
Kamat daga sama Rayyan ha fara magana, "Wannan therapist dinne ai, banga anfanin shi ba nikam. An taba therapist din da kuma zaisa ka kuka?"

ESTÁS LEYENDO
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...