Shida

2.1K 246 10
                                    

Har suka karasa bakin restaurant din Ramlah bata daina kuka ba. Saida ya tsaida motar kafin ya juyo yana kallonta, jikinta babu inda baya rawa kuka kawai take. Hinkici ya ciro daga aljihun shi ya mika mata, kamar bazata karba ba sai kuma ta amsa tana share hawayenta. Tausayi take bashi, in baccin ko hata fada ba daga gani kasan tana cikin kunci kuma rayuwar datayi baya tattare take da kunci, dan me daga ganin mata tana bara da yara biyu sai ka fara kuka? Baisan ko itama tayi barar ba a baya, amma tabbas rayuwarta akwai alamar tambaya.

Miko mashi hankicin tayi amma maimakon ya amsa sai ya mika mata robar ruwa, "Ki wanke fuskarki, kar mu shiga mutane su dauka satoki nayi ko wani abun." Ramlah bata san lokacin data galla mashi wata muguwar harara ba, ashe ma satowa.

Dariya ya fara yi, "Dama masifa gareki? Irin wannan harara haka ai sai kisa tari ya sarke ni nima din in mutu." Batace komai ba ta karbi robar ruwan ta bude kofar motar. Daga zaunen da take ta wanke fuskarta sannan tasha ruwan hankalinta ya dan dawo jikinta.

Juyowa tayi bayan ta aje robar ruwan a jikin kofar. "Nagode." Haka kawai sai taji dama batayi kukan a gabanshi ba, yanzu sai ya fara tunanin rainata ko wani abu. Amma kuma sai ta maze, dan har yanzu kukan bai isheta ba, dan ta rabu dayin kuka. Wataran ma neman hawayen take tsaf ta rasasu, amma yau taji dadin yin kukan, koba komai sai ranta ya dan mata sanyi.

"Muje toh, yanzu it's safe ko mun fita a haka." Ba sai ta tambaya ba daga ganinshi kasan irin mutanen nanne masu fara'a da mutunta mutum, amma ita yanzu mutane sune abu na karshe da take bukatar hada koma wace alaka ce dasu.

"Aa, na koshi Allah. Nagode." Ta furta a hankali tana kallon yadda kwayar idanunta ta kada tayi jajir tsabar kukan da tayi. Mutum kallo daya zai mata basai ya kara dana biyu ba zai tabbatar ma kanshi tayi kuka. Bazata iya fita cikin mutane haka ba, dukda cewar ta saba sai ta dade a wuri babu ma wanda ya lura da ita, amma dukda haka bazata fita ba. Kuma ma din da gaske take ta koshi.

"Ki fito muje dan Allah, Ramlah. Nasan bakici komai ba, gabana Lubnah ke maki magana kan cewa kici wani abu, yanzu kuma ga kukan da kikayi, inba so kike ga damuwa ga yunwa ba su idasa rayuwarki to ki taso muje." Da kamar ta mishi gardama, amma ko bata tambaya ba tasan Rayyan daukarta ne kawai bai iyayi ya kaita cikin restaurant dinnan.

Ta madubin motar ta kara kallon idanunta, "Idanuna sunyi ja dayawa, kaje kawai idan na koma gida sai naci wani abun." Baice mata komai ba ya bude dashboard din motar ya dauko daya daga cikin bakaken gilasan dake ciki.

Ramlah itadai tsaye tayi tana kallonshi, sai ji tayi ya saka mata gilas din a ido, wani baya tayi tana kara zaman gilas din a idonta. "Miye haka?" Ta tambaya, tana juyawa ta kalli madubin saida ta kara kallon fuskarta. Tasan tabbas duk wanda ya ganta bazaice mata mai muni ba, amma kuma rabon dataga kyanta shekara aru aru da suka wuce.

"Glass ne mana, babu wanda zaice kinji kuka yanzu. Muje." Daga haka ya fita motar, saida ta tsaya tana kallon yanda ya tsaya wajen motar ya saka hannayenshi duka cikin aljihun wandonshi yana jiran fitowarta kafin ta sauke ajiyar zuciya itama ta fita.

A hankali suke takawa babu wanda yace ma danuwanshi kala. Wuri ya samar masu kusa da window suka zauna kafin ya bada odar abunda sukeso, dan koda ya tambayeta akan me takeso taci batace mashi kala ba, saidai shi yayi mata odar abunda yakeso. Sunyi zaune shiru babu mai magana, amma alama ta nuna cewar Ramlah ta koma duniyar tata tunanin, kawai sauki daya babu wanda zaisan halin da take ciki saboda gilas din dake idonta.

Wayarshi ce tayi kara ya dauka a hankali, "Hello, Lubnah?" Ya fada a takaice, sai lokacin hankalin Ramlah ya dawo kanshi jin ya ambaci sunan Lubnah.

"Na dawo ne naga bata gida, ni duk hankalina ya tashi kar ace fita tayi. Kuna tare dan Allah?" Da muryar wanda hankalinshi ya fara tashi tayi maganar, yar dariya yayi a hankali.

"Eh muna tare, kuka taita mani cikin mota shine na kawota taci abinci." Magana suka danyi kafin ya turawa Lubnah adires din inda suke da cewar yanzu direba zai kawota.

Bada jimawa ba aka kawo masu abincin su, gudun magana yasa Ramlah ta dan fara tsakura amma kuma tuni hawaye sun fara cika idonta. Sau da dama tun lokacin datazo gidan su Lubnah ko bataso shiga cikin wani kuncin ba to tabbas sai ta shiga. Saboda tunawa da yanda Hanan tayi rayuwa kafin ta rasu, da ace dane take samun irin wannan abincin da ta bawa Hanan shi duka ta cinye koda kuwa zata kwana da yunwa ne.

Rayyan ya lura da hawayen da ke niyar sauka kan kuncinta, mika mata hankicin kawai yayi ba tare da wata magana ba. Da dubara Ramlah ta share hawayenta dukda cewar wasu ne ke tafe sunasan zubowa. Suna haka sai ga Lubnah ta shigo, da hanzari ta karasa wajen Ramlah ta dan rungume ta kafin ta samu waje ta zauna.

"Wallahi Ramlah na dauka wani abune ya sameki." Ta fara magana tana murmushi bayan sun gaisa. Sai a lokacin ta lura da gilas din dake fuskarta, "Wannan glass din fah? Rayyan kai ka bata shi ko? Kuma wallahi ya masifan yi maki kyau."

Dan dagowa tayi ta kalli Lubnah wacce ke mata murmushi me kyau. Ji take inama zata iya wanke dukkan wata damuwar dake cikin ranta suyi rayuwar farin ciki da Lubnah da Mama? Dan daurewa tayi tayi murmushi, "Ni dukma ya takuran man..."

Bata ida magana ba Rayyan ya katseta, "Kuka tayi kuma idanunta sunyi ja, dole na bata shi inba haka ba sai mutane su dauka satota nayi ko wata muguntar na mata." Dariya Lubnah tayi tana ciro wayarta.

"Bari in maki hoto, dama banda hotonki ko daga wayata." Da Ramlah kamar bazata tsaye ayi hoton ba sai kuma ta tsaya. Nan Lubnah tayi odar abunda takeso suka zauna sunaci a hankali. Sako ne ya shigo wayar Rayyan bayan ya dauka ya duba kafin ya maida wayar ya ajiye sai yaga Ramlah ta kalli window daga gani tunani takeyi. Haka kawai ya shiga camerar wayarshi ya dauketa hoto ba tare data sani ba ko kuma shi yasan nashi dalilin na daukar hoton.

Saida suka gama cin abincin har sun koma mota Lubnah ta jiyo tana kallon Ramlah dake zaune bayan mota, "Ramlah, Dr Mahmud ya kirani. Ashe kinasan photography. Muje yanzu a siyo maki camera kinaso?"

Da hanzari ta kallo Lubnah tana murmushi, "Eh, inaso!" Abunda ta furta kenan sai lokacin kuma ta lura cewar to ai bada ruwa ake siyowa ba, hannu ta daga ma Lubnah da hanzari. "Aa, abunda nake nufi inasan photography bawai muje a siya yanzu ba..."

Dariya kawai Lubnah ta fara, "Dan Allah Rayyan ka kaimu na siya mata."

"Lubnah! Allah da gaske karki siya!" Ita data san abunda Dr Aliyu zaiyi kenan da bata fada mashi tanasan daukar hoto ba. Ita ta dauka kawai a matsayin labari sukayi abun.

Juyowa Lubnah tayi tana kallonta, "Tunda na hadu dake ban taba ganin liveliness a idonki ba sai yau, kuma akan photography, Ramlah. Yau za'a sayi camera insha Allahu. Sannan kuma idan nasanh wanda yake masterclass na photography cikin photographers din garin nan zanyi enrolling dinki kije ki koya sosai, shikenan?"

Ramlah idanunta raurau sukayi suna neman zubda hawaye, "Bansan ya zan gode maki ba, Lubnah."

Da murmushi Lubnah ta gyada mata kai, "Ki daina damuwar nan, ki zama mutum tamkar kowa, kiyi farin ciki, Ramlah, shikenan kin biyani."

"Zan daure, Insha Allahu. Nagode." Daga haka suka wuce, tana jin Lubnah na bawa Rayyan labarin wajen aikinsu suna tattaunawa. Idan ka gansu suna magana zaka dauka abokai ne ba wai wanda iyayensu ke san hadasu aure ba. Tunda suke tare ma basu taba maganar dalilin na iyayensu ba. Yanzu kuma tunda Ramlah tazo gidan maganarsu tafi yawa a kanta.

Kamar yanda Lubnah tace, haka sukaje shagon siyar da kayan wuta wanda a nan sunada tabbacin samun camera. Saida ta kira waya taji wacce tafi kyau kuma wacce ta kamata ta siyawa Ramlah tukunna ta siya suka wuce studio din George Okoro, inda nan aka tabbatar mata tabbas ya fara registration din masterclass din da zai fara next week.

Saida suka gama magana da komai da komai, wanda a karo na farko Lubnah taji sunan cikakken sunan Ramlah, wato Ramlah Kamal Ibrahim shima dan tana cike mata form ne. Anzo biyan kudin registration Rayyan yace shi zai biya, dakyar Lubnah ta bari ya biya kafin suka koma mota suka karsa gida.

Da gudu Lubnah ta shiga gida dan ta shaidawa Mama yau dai an samu abunda Ramlah takeso, koda Ramlah ta fito mota jira tayi saida ya fito kafin ta ciro gilas dinshi ta mika mashi. "Nagode sosai. Sannan registration dinma, nagode."

Kin karbar gilas din yayi, "Shi glass din kyauta na baki, duk ranar da kikayi kuka kuma zaki shiga cikin mutane sai ki saka. Amma kudin registration, ki hadasu da wancan bashi ne, wataran zance ki biyani." Batasan ya akayi ba, saidai ganin kanta tayi ta dan buga kafa daya kasa tana me pouting (miye pouting da hausa?) labbanta daidai da ya sakar mata wani kayataccen murmushi.

MIJINA NE! ✅ Onde histórias criam vida. Descubra agora