Kadan kadan Ramlah ta fara kuka, can kamar an bude famfo kawai ta fara kuka jikinta har wani jijjiga yake. Karshen tashin hankali ta kaishi, komai na duniyar ya tsaya mata cak, ga tsoro, ga fargaba ga kidimewa ta ma rasa shin menene gaskiar abunda take gani a gaban idonta? Rayyan magana yake mata amma sam ko saurarenshi batayi, kuka kawai take. Dakyar ya samu ya yasu sukaje kan roadside benches dinnan suka zauna ya jiyo yana fuskantar ta.
"Ramlah, lafiya? Meya faru? Wani abu kika gani ko kuwa?" Magana yake mata a hankali amma ta rufe fuskarta da hannayenta duka biyu banda kuka babu abunda takeyi. Shi gaba daya abun tsoro yake bashi.
"In bazaki iya magana ba to kiyita karanta Innalillahi, zaki samu natsuwa kinji?" Ya furta a hankali, tausayinta yakeji. Wannan wace irin rayuwa takeyi haka? Daga yau ta dawo daidai sai kuma gobe labari ya chanza? Wane irin murdadden alamari ne ya faru da rayuwarta hakan?
Da kamar ba zatayi ba, amma sanin girman alamarin daya fuskan tota yasa ta fara karanta Innalillahi tana share hawaye. A ranta tana karyata abunda idanunta suka gane mata, dan tasan babu yanda za'ayi hakan ta faru. Kila dai kawai tunani yau yazo mata haka nan. Tun tanayi cikin ranta har labbanta suka fara motsi, a hankali natsuwa ta fara dawo mata cikin jikinta amma maganar kwanciyar hali babu ita.
Dan juyowa tayi taga ya kureta da idanu yana kallonta, "Ina ne nan? Ina Lubnah?" Juyawa take a hankali, ga idanunta da sukayi jajir tsabar kukan datasha. Har yanzu sai sauke ajiyar zuciya takeyi. Kwata kwata ma taki yarda da zuciyarta ta ruwaito mata abunda ya faru lokaci kankani da suka wuce. Kila kawai tunani ne, dan bazata ce mafarki ba tunda ba'a mafarki mutum idonshi bude.
"Suna can hall din, muje na maida ki hotel dinku. Nasan kila sun gama sun watse wajen baki daya." Mikewa yayi yaga sai kalle kalle take, shi tsoronahi daya kar ta kara ballewa dan baisan kuma ta inda zai fara tarota ba. Jiki a sabule Ramlah ta mike tsaye ta kalleshi sai kuma kamar daga sama yaji ta rike hannunshi gam. Juyowa yayi ya kalli hannunta dake rike da nashi ga kuma sai juye juye takeyi.
"Rayyan tsoro nakeji, fatalwa nagani." Shar shar sai hawayenta suka dawo. Bata san tuna abunda ta gani, gaba daya ma ta kauda tunanin a ranta amma kuma tsoro da fargabar abun har yanzu basu bar zuciyarta ba. Baiso ya mata magana yanzu dayaga ta gama tsoro, hannunshi ya riko nata in a way that ko zata ruga ma bazata iya guduwa ba kafin a hankali suka fara tafiya.
"Babu abunda zai sameki kinji? Ina tare dake, most importantly, koda ke kadai ce Allah yana tare dake, Ramlah." Daga mashi kai kawai tayi. Karshe ma runtse ido tayi dan gani take a kowane kofa zata iya kara ganin abunda ta gani. Baice mata komai ba a haka hannayensu rike dana juna ya jata har suka isa hall dinnan. Kamar kuwa yanda yayi hasashe babu kowa sai kwararan mutane da alama anyi yan mintuna da tashi amma kuma abokan amarya da ango har yanzu basu gama watsewa ba.
Janta yayi hanyar motarshi ya juyo ya kalleta, "Ki shiga ki zauna, bari naje na dauko maki jikkarki kinji?" Har ta daga mashi kai zata zauna kawai ta jiyo sautin dariyarta. A kidime ta waiga inda take jiyo sautin taga shidin daine. Ga angon nan daga gefenshi suna hira yana dariya, ga wata mata mai ciki suna takawa a hankali da alamu rakasu zaiyi wajen motarsu.
Mutuwar tsaye kawai tayi, yanayin yanda yake tafiya take bi da ido, yanayin yadda dariyarshi takeyi ma fuskarshi, yanda yake ma hannu idan yana ma mutum bayanin abu. Komai nashi iri daya ne sak, bai chanza ba, kuma Ramlah tana da tabbacin koda kuwa itama mutuwar tayi ta dawo bazata taba mantawa da siffofinshi ba. Wani irin kuka ta fashe dashi tana nunashi da yatsa.
"Rayyan wallahi shine, Abban Hanan ne gashi can tsaye. Rayyan baisan Hanan ta rasu ba, bari naje na fada mashi." Zumbur tayi zata je wurin da suke tsaye, rigota Rayyan yayi gam daidai lokacin da Lubnah ta karaso wajensu hankalinta duk ya gama tashi. Gani tayi Ramlah sai kiciniyar kwacewa takeyi yana kokarin tsaidata waje daya.
"Rayyan lafiya? Wai meya sameta?" Ta tambaya idanunta suna kawo ruwa. Gani take kamar tabin hankali ke neman kama Ramlah, wani irin kunci takejin yana dabaibaye ilahirin ruhinta.
Da hanzari Ramlah ta juyo tana kallonta, "Ki fadi mashi ya barni naje, Lubnah. Abban Hanan ne, baisan Hanan dinmu ta rasu ba, Dan Allah ku kyaleni naje ma fadi na rokeku." Kuka takeyi kamar ta fito da zuciyarta ta huta tsabam dacin da takeji cikinta. Tsoro takeyi amma kuma burinta bai wuce taje ta fada mashi Hanan dinsu ta rasu ba. Duk duniya babu abunda Hanan takeso tamkar Abbanta, tunda ya rasu kuwa bata magana biyu bata kira sunanshi a na ukkun ba.
Lubnah kallon inda Ramlah takeyi tayi sai taga ashe su Yassar ne basu tafi ba, "Ramlah wa kike magana a kai? Can wajen babu Abban Hanan, Yassar ne abokin mijin Zainab da matarshi Nuratu. Sai kuma mijin Zainab din da kanshi..." kuka ne ya kwace ma Lubnah dan ita duk a tunaninta fatalwa Ramlah ta fara gani.
Karshe dai Ramlah hakura tayi da kiciniyar kwacewa ganin har sun shiga mota. Kuka takeyi kamar yau su biyun suka rasu, "Dan Allah na rokeki Lubnah kice ya barni naje na fada mashi, Hanan ta rasu, Abban Hanan baisan Hanan ta rasu ba, Lubnah!" Wani irin karfi ne yazo mata, fizgewa tayi ta ruga da gudu amma ko kafin taje wajen sun fita da gudu daga hall din. Faduwa tayi dabas a kasa tana fashewa da wani irin gunjin kuka. Gashi nan, har yanda yake tuki, yanda yake juyawa yana magana, wallahi shine.
Hade kai kawai tayi da guiwa tana rigzar kukanta, "Wallahi shine, wallahi Abban Hanan ne." Har can kasan zuciyarta takejin wani daci yana taso mata. Zuciyarta cike take fal da kunci da bakin ciki. Komai daya taba faruwa a rayuwarta sabo ya dawo mata fal.
Rayyan da Lubnah ne suka karaso inda take, "Kamata muje mota tun kafin attention din mutane ya dawo kanta, Lubnah." Hakan kuwa akayi. Saida suka tabbatar ta zauna an kulle kofa kuma Lubnah ta zauna gefenta kafin Rayyan yayi locking duka kofofin ya tada motar suka fita daga hall din baki daya.
Har suka isa babu abunda Ramlah takeyi banda kuka, sai tayi kukan ta jiyo tace ma Lubnah wallahi shine, komai nashi yana nan bai chanza ba, wallahi ita tasan Abban Hanan ne. Dakyar Lubnah ta samu ta yarda suka haura daki dan saida tace mata gobe zasuje a tambayeshi idan shi dinne. Har daki Rayyan ya biyosu da jakkunansu. Kan gado ta makure ta hade kai da guiwa babu abunda takeyi banda dizgar kuka.
Zainab ne ta shigo itama hankalinta a tashe tana tambayar Lubnah ko lafiya? Fita sukayi su biyun suka koma dakin Zainab dan ta bata labarin abinda ake ciki. Rayyan takawa yayi ya zauna kan bedside drawer yana kallon yadda ta kulle idanu rip babu abunda take sai kuka, jikinta kuwa babu inda baya amsawa.
"Ramlah," ya kira sunanta a hankali. Da kamar bazata dago ba sai kuma ta dago tana kallonshi, wasu sababbin hawaye suna kwanciya male male kan fuskarta.
"Rayyan wallahi shine, Abban Hanan ne. Kaki barina naje na fada mashi Hanan ta rasu, baisan ta rasu ba, Rayyan." Dan me bazasu yarda da ita ba? Ita kanta tasan faruwar hakan abu ne mai wahala amma kuma koda mutuwa tayi ta dawo fuskarshi ba abuce wadda zata manta ta ba.
Ruwa ya mika mata, bata mashi musu ba ta karba tasha kafin ya aje cup din gefenshi. "Ramlah, ke da kabki kika fada mana cewar Abban Hanan ya rasu, ko ba haka ba?"
Dan shiru tayi kafin a hankali ta daga mashi kai, "Ya rasu, amma wallahi Rayyan shine. I can bet on my life cewar Abban Hanan ne wancan mutumin, kuma daka barni naje da ka yarda dani."
"Ba hanaki yanayi ba dan banaso kije ki ganshi, Ramlah, sai dan hakan shine abunda ya kamata nayi. Ba'a mutuwa a dawo, ko kin taba ganin wanda ya rasu kuma ya dawo?" Kamar karamar yarinya haka tana share hawayenta wasu na kara zubuwa tana kuma girgiza mashi kai. "To kin gani, kila idanunki ne ke nuna maki siffofin Abban Hanan amma bashi bane ba tunda kin tabbatar man da cewar ya rasu, Ramlah."
Juyowa tayi gaba daya tana fuskantar shi, wasu hawayen ke bin kuncinta amma ta sharesu, babu abunda takeyi sai ajiyar zuciya, idanunta kuwa sunyi jajir kamar yau akayi mata rasuwar. "Bai zama lallai ka yarda dani ba, amma wallahi Rayyan shine. Yanda yake tafiya, yanda yake dariya, maganarshi, har yanda yake tuki, komai nashi yana nan bai chanza ba. Dan me zaku cemun bashi bane ba?! Nasan ba'a mutuwa a dawo, amma inada tabbacin Abban Hanan ne wallahi!"
Wani kukan ta kara fashewa dashi, Rayyan ya bude baki zaiyi magana ta riga shi, "Fita! Dan Allah karka kara cewa komai, kawai ka fita ka bani wuri." Yanda tace din haka yayi, saidai kafin ya tafi hotel dinshi saida ya kira Lubnah akan taje ta kula da ita kar wani abun ya faru.

VOCÊ ESTÁ LENDO
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...