Ashirin Da Ukku

1.3K 196 11
                                    

Kafin tayi wani kwakwaran motsi taji muryarshi gefenta, "Yayi? Ko akwai abunda zanci kafin cookies din su gama?" Juyowa tayi amma tak'i yarda su hada ido, dan ita kam har ga Allah maganar ta tsaya mata a rai. So take ma ta gaya mashi magana amma ganin yanda yayi maganar kamar ma bai san me yace ba yasa ta fasa, dan kuwa idan ta maido maganar zai zamana kamar ta damu.

"Kamar dazu na aje pepper soup a cikin fridge, ka iya warming ko na maka?" Juyawa tayi ta nufi hanyar fridge dinma tun kafin ya bata amsa. Har ta saka cikin warmer kafin ta juyo tana kallonshi. "Yanzu kai gobe zakaje aiki amma har past 1 bakayi bacci ba? Kaje kaita musu layi wurin aikin ai."

Yar dariya yayi bayan ya koma ya zauna, yana sane sarai so take ta nuna baiyi wannan maganar ba, shi ma kuma bayaso a maido ta. Dan idan har aka maido ta zai iyayin maganar da sai daga baya zaizo yayi dana sani. "To ai nine ogan kowa, sai inyi bacci na yanda nikeso."

"Company dinka ne? Baku daukar ma'aikata?" Magana tayi da hanzari alamar abun yayi catching attention dinta. "Na Baba ne, amma ni nake managing branch din Abuja. Ma'aikata, aiki kikeso?" Yar dariya tayi kafin ta saka sauran cikin oven ta ciro mashi pepper soup dinshi ta aje ta janyo kujera ta zauna, "Ai baku neman photographers, ni kuma inba photography ba babu abunda na iya."

Ya lura yanda takejin yan magana yanzu ne daidai na ya mata tambayar daya dade yanasan yayi. Lubnah tace ta taba fara bata labarin iyayenta amma bata ida ba, kuma itama Lubnah bata fada mashi me tace ba, shi kuma yanaso yaji. "To baki da wasu takardu? Sai na duba maki wani aiki, ina iya chanza ma sakatariyata wuri in dauke ki."

Dariya ta fashe da ita tana mika mashi cokali hade da mishi nuna ya ci dan kar ya huce, "Ni? Takarda? Bama nan ba, in na zama sakatariyarka ai haushi zakai ta bani kullum muyita fada karshe a koreni aikin." Dariya yayi, amma bai bata amsa ba saida yaje ya dauko cokali itama ya mika mata.

"Muci, wannan ya mun yawa." Taso yin gardama amma ganin da gaske yake yasa ta amsa kafin ya cigaba, "Bazamuyi fada ma, ai Ramlah hakuri gareta sosai. Kedai in kinada su ki kawo kawai."

Girgiza kai tayi, bata bashi amsa ba sai data cinye abunda yake bakinta. "A'a, secondary school kawai nayi fa, shima da kyar. Wannan dan guntun turancin daka gani dace nayi mutanen nan sun sakani private school, inba haka ba babu abunda zan iya."

Dukda ko kafin ta fadi ya riga ya hango kunci tattare da maganganun da takeyi. Amma haka ya daure yayi yar dariya, "Wai mutanen nan, Ramlah iyayen naki?"

Murmushi Ramlah tayi, aje cokalin tayi kafin ta fara magana. "Basu ba, iyaye na basu da halin sakani ko ta gwamnati balle private, Rayyan." Har tayi shiru amma ganin yanda yake kallonta yasa ta cigaba, ranar ta fara bawa Lubnah labari Dr Aliyu ya kirata basu cigaba ba. Kuma ya taba fada mata cewar idan ta samu wanda taji zata iya bashi labarinta ta bashi, hakan zai hana abun damunta kamar yanda yakeyi a da. "Babana da Mamata yan Niger ne dukansu, a wani gari da ake cewa Dosso, ban taba zuwa ba suma kuma tun bayan aurensu suka baro garin." Yar dariya tayi, amma tayi hakan ne ba dan komai ba sai dan ta tsaida hawayenta daga zubowa.

"Sai daga baya Mama take fada man cewar gudowa sukayi aka daura masu aure a Jibia, karamar hukumar Katsina. Shi dai Baba dan gidan masu kudi ne, ita kuma Mama duk unguwar ma babu mai talaucin su. Babu yanda iyayenshi basuyi ba akan ya daina soyayya da ita amma ya ki wanda ganin za'a rabasu ta karfi da yaji yasa suka gudu suka bar kasar gaba daya. Waya sani? Kila haka Allah ya nufa, dama basu gudo ba kila da sun haifeni cikin jin dadi nayi rayuwa me dadi, su dadi soyayya." Tana dariya amma kuma hakan bai daina hawayenta zuba ba. Kallo daya ya mata ya gane cewar so take ta rage radadin da ciwon yake mata a zuciya.

"Ramlah..." A hankali ya fara kiran sunanta amma tayi saurin girgiza mashi kai tana me rufe fuskarta da tafin hannunta.

"Ka tsaya kaji, be my therapist for today, ban taba fadawa kowa ba. Will you?" Idanunta da har sun fara komawa jajaye ta dago tana kallonshi, a hankali ya daga mata kai amma a zuciyarshi wata kuna yakeji da bai taba jin irinta ba.

"Yan kudaden da Baba ya kwaso masu dasu suka nemi gida a nan jibia suka zauna. Ayanda Mama tace kullum sai suce zasuje Dosso amma sai su fasa saboda sunsan da sun koma rabasu za'ayi kuma iyayensu bazasu taba yafe masu ba. A hankali Baba ya fara shiga kasuwa yana samun abunda zai rufa masu asiri dashi. Har ya zamana ya fara dan tara kudi har ya chanza masu gida, a lokacin ne aka samu cikina. Zamansu cike yake da kwanciyar hankali da kaunar juna, dan a duniya ban taba ganin mutanen da suke san junansu kamar iyayena ba. Ban taba ganinsu sunyi fada ba, nasan suna samun sabani amma nidai ban taba gani ba. Wata irin soyayya ce wanda a da nake tunanin zan iya maimaita irinta amma yanzu na hakura.

"Mama nada ciki na wata tara wani ibtila'i ya afkawa Baba. Abokanan kasuwancinshi suka damfareshi gaba daya arzikin dayake juyawa ya kare. Suna cikin wannan halin kuncin ne da bakin ciki, yau su samu gobe babu har Allah ya hadashi da wani aljahi, wanda ya taimakeshi yace mashi dama yana neman me gadi idan zai iya toh, amma a Katsina yake zama. Shi kuma Baba bazai iya barin Mama ita kadai ba gashi haihuwa yau ko gobe. Ganin haka yasa Alhajin yace mashi akwai part din maigadi a gidan zai isheshi shida iyalinshi.

"Basu dade da komawa Katsina ba aka haifeni. Tunda Mama taje gidan Uwargidan Alhajin nan me suna Hajia Ramlah take matukar kaunarta. Komai ita take mata, dan harta zaman asibitin ma ita ta mata. Hakan yasa Baba ya saka man suna Ramlah. Ramlar Hajia. Ita kuma Hajia tana ceman me sunana. Bayan iyayena zan iya ce maka babu wanda ya taba mani san da Hajia take mani kuma har na koma ga Allah baza'a taba mani irin san nan ba." Zuwa yanzu kukanta yaci karfinta. A da ta dauka idan ta tashi bada labarinta abun zaizo mata da sauki. Zataji tamkar ta bude littafi ne tana karantowa ko kuma ace tana kallon film. Ashe abun ba haka yake ba, ji take tamkar duk kalma daya dake fitowa daga bakinta to yankar tsokar zuciyarta akeyi.

"Ba sai kin cigaba ba..." ai bata barshi ya ida ba ta girgiza kai. Zata iya cigaba, dukda cewar tasan bazata taba iya bashi dukkan labarin nata ba a yau, zuciyarta bata da wannan karfin.

"Nasan dai Baba shine Maigadin gidan Mama kuma ita take masu dukkan ayyukansu na gida wanda ta hakan ne suke taimakawa suci da kansu da sutura da sauran bukatun rayuwa, amma zan iya ce maka kusan kamar Hajia ita ta haifeni, Rayyan. In baccin yaran kishiyarta da har daki inada a cikin gidan amma kishiyarta ta tada bala'i dole Hajia tace na hakura. Kusan komai ita take man, gani da rigimar tsiya, jan fada, idan yaran suka jana suna ceman diyar me gadi ko yar aiki ban iya hakuri sai nayi masu dukan tsiya amma haka Hajia zatazo ta goyi bayana, wani lokacin har fada sukeyi da Alhaji, inaji har gori ake mata saboda danta daya namiji kuma tunda ya gama primary baya kasar ni ko ganinshi ban tabayi ba amma wani lokacin muna gaisawa idan ya kira Hajia. Koshi Ramlar Hajia yake ceman, ko Autar Hajia.

"Lokacin da Hajia tace a sakani makaranta kishiyarta wacce muke kira Umma ta dage ita akan baza'a rika biyan iyayena albashi ba sannan kuma Alhaji ya dauki dawainiyata. Hajia da kudinta ta dauka ta sakani makarantar da yaran gidan suke. In baccin inada tsiwa da nasha wahalarsu a makaranta, amma dukda haka babu wanda baisan ni yar wacece ba, ko kawa daya banda ita har na gama tunda makaranta ce ta yaran masu kudi ni kuma diyar me gadi ce.

"Lokacin na taba wani saurayi sunanshi Hafiz, Allah sarki..." Yar dariya ta kubce mata, wasu hawayen ta kara sharewa amma hakan bai hana wasu zuba ba. "Ina SS2 lokacin, kuma dama can ba wani sanshi nake ba, amma dayake Mama tasha fada man dana gama secondary zasu man aure dan sunasan su koma Dosso su naimi gafarar iyayensu yasa na yarda yaje yaga Baba. Da akaje ma Hajia da maganar ta fututtuke taita bala'i, ai inada kokari babu yanda za'ayi su man aure da wuri, makaranta zan cigaba sai na zama duk abunda nakeso na zama. Kuma yanda ta fara daukar nauyi na har karshe babu ruwansu da aurena ita zatayi komai sudai su zuba mana ido, dama shi Baba bayasan auren wuri, hakan yasa suka kwantar da hankalinsu.

"Ranar danaje firar dare wurin Hajia ta kirani ta rike hannayena, 'Kina sanshi Ramlah?' da hanzari na girgiza mata kai ina dariya. Dan wani lokacin nafi kusanci da ita fiye da Mamana. 'To babu komai kinji? Babu wanda zai maki aure yanzu. Karatu zakiyi ko? Gaki da kokari masha Allahu, sai kin zama wani abu insha Allahu kin gina ma su Baba gida me kyau ko?' rungume ta nayi ina dariya, dan duk wani burina babu wanda Hajia bata sani ba, dan nafi zama da ita na tsawon lokaci fiye da Mama. 'Har dake ma, Hajia. Ku uku zan saka cikin gidana muyi zamanmu. Shi Hafiz dama nasan baya man irin san da Baba yakewa Mama, bazanyi aure sai na samu wanda zaiman irin wannan san.' Hajia nata dariya tace, 'Duk wanda baiso kyakyawar diyata ba ai asara kanshi, rabu dasu kinji me sunana?"

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now