Sha Biyar

1.7K 234 32
                                        

Ita dai bazata ce bikin yana mata dadi ba ko akasin sa. Gata nan dai ne kawai, amma abunda take da tabbacin shi shine da ace ba a matsayin photographer tazo bikin nan ba babu abunsa zai hana ta koma daki ta kwanta har sai Lubnah ta dawo. Ba kasafai hayaniyar mutane take burgeta ba. Yanzu haka kallon yanda mutane suke ta hidima wasu na rawa wasu na cin abinci takeyi. Ganin indai ta tsaya wajen babu ahunda zai hana kanta ya fara ciwo yasa ta taka taje inda Sumayyah da Idris suke tsaya.

"Sumayyah zan dan fita insha iska, mutanen nan nema suke su saka mani ciwon kai. Dan Allah ku kula sosai kiyi aikin daya kamata, Idris." Ta fada tana murmushi.

"Insha Allahu, Hajia." Har yanzu abun bai daina bata dariya ba in suka kirata Hajia, sai taji abun wani banbarakwai. "Nasha fada maku sunana Ramlah, in baccin zuwana garin nan ban taba koda leka jirgi ba, balle wai jirgin har na Hajji. Ko rika ceman Aunty Ramlah in baku iya kirana Ramlah kai tsaye." Murmushi kawai sukayi a tare har ta bace da ganinsu suna mamakin mutum irinta. Dan da zasu biye mata babu abunda zai hana Ramlah treating kanta kamar su.

Fita tayi daga wajen hall din, dinner akeyi kuma yau rigar nan ta saka. Amma yau duk yadda taso Lubnah tsaye tayi saida aka mata kwalliya me yawa, kuma janbaki ma me kala aka saka mata. Jin yanda iska ke kadawa cikin jin dadi a waje yasa ta saki dan murmushi kafin ta karasa kan bencin data gani dan gefe da hall din. Zama tayi sai ga kiran Dr Aliyu ya shigo, sai lokacin ta tuna taga missed call dinshi amma shaf ita mantawa ma tayi da ta kirashi back.

"Assalamu Alaikum, ina yini?" Ta furta a hankali tana murmushi.

"Gaskia bazan amsa ba, ni ai fushi ma nake dake in banda Hafsah data takura mani sai na kiraki." Magana yake amma murmushin da take jiyowa yasha banban da kalaman da yake furtawa.

"Dan Allah kayi hakuri, Dr. kasan Allah hidimar biki ce tamun yawa, inata so na kiraka sai kuma wani abu ya shige man kai. Ina Hafsar?" Ta fadada murmushinta. Gara ma kenan data fito, dan tasan da tana cikin hall dincan tasan da bazata ji ringing din wayar ba.

"Oh ta Hafsah ma kike yanzu kenan?" Ya tambaya da alamu yaji haushin abun amma da hanzari ta fara dariya tana girgiza kai kamar tana gabanshi.

"Dan Allah kayi hakuri. To me kakeso ince? Ya kake? Ya gida ya aiki?" Ya tambaya tana murmushi, daidai lokacin taji alamun wani ya zauna kan bencin da take, juyawar da zatayi taga Rayyan ya kura mata idanu ga hannuwanshi ya harde saman kirji kallonta kawai yakeyi.

"Lafiya lau. Kinje biki kin manta dani..." bai ida magana ba ta jiyo muryar Hafsah carai tana ihu, "Abba nidai ka bani Ammita! Cewa fa kayi ni zaka kira ma ita!" Dariya Ramlah ta fashe da ita a ranta tana fadin 'Hafsah rigima.'

"To ga diyata nan tana magana, bata mu gaisa anjima idan na koma gida sai na kiraka mu gaisa, yanzu muna wajen event." Babu abunda takeso face kodai ta gama wayar ko kuma Rayyan ya dauke idanunshi kanta. Wani kallo kallon tuhuma yake mata duk ta rasa sukunin ta.

"Ammi! Nayi kewarki!" Muryar Hafsah taji tana magana da wani faffadan murmushi alamar taji dadi har cikin ranta.

"Hafsah am, nayi kewarki nima. Yaya diyar Ammi take? Bakiwa Abba da Hajia Mama rigima ko?" Ta tambaya.

"Eh Ammi. Abba yace kinje biki, yaushe zaki dawo? Inaso inzo in ganki, Ammi."

"Nan da kwana biyu zamu dawo, Hafsah kinji? Dana dawo zance Abba ya kawo mani ke...." Yar fira sukayi a hankali kafin Ramlah tace mana zata kira suyi waya sosai gobe, tana kashewa ta juyo tana kallon Rayyan. "Ina yini?"

Girgiza kai yayi a hankali, har yanzu idanunshi kyam saman fuskarta. "Ni ki daina gaidani. Anya ma baki girmeni ba kullum kita wani ce mani ina yini?"

"Dan Allah daina, a tunaninka shekarata nawa? Duka duka I'm 23 fah. Ka girme ni mana." Ta fada tana dan murmushi.

Murmushi yayi a hankali kafin ya dauke idanunshi daga kanta, dan ya lura kallonta bawai zai haifa wani abu me dadi bane ba. "Shekarunki daga da kanwata, sunanta Maryam."

"Dan Allah? Allah sarki, kuna kama?" Ita idan taga mutum yana da kan'i ko wa abun har burgeta yake, sai taita tunani to ya sukeji kanada abokin fira da fada? Dan ita koda ta tashi saidai ta fita waje taja fada in yan rigimar takeji.

Wayarshi ya janyo daga aljihu ya budo hotonsu da sukayi da Maryam lokacin bikinta shekara ukku da suka wuce. Nuna mata yayi aikam ta fara murmushi, "Jibarku dan Allah kamar yan biyu, amma dai daga gani ta fika kyau nesa ma ba kusa ba. Tayi aure ne?"

"Ki jiki fah, yarinyar da akabi aka shafe da powder da janbaki za'ace ta fini kyau. Eh, three years ago tayi aure, tana zaune Germany da mijinta yanzu yaranta biyu yan biyu ne amma."

Murmushi tayi tana kara kallon hoton, yanda Rayyan ya rikota sai murmushi sukeyi. "Allah sarki, Allah ya raya mata su." Sai kuma yaji ta bashi tausayi amma da hanzari ta maze tamkar babu abunda ya faru.

"Idan mun koma gida zan tayaki fadawa Mama."

Juyowa tayi ta kalleshi dan bata gane abunda yake nufi ba, "Me zaka fada mata?"

"Dr Aliyu mana, ga diyarku nan ai yaci ku taimaka ma yarinyar nan ku daina bata wahalar neman Amminta." Wata itin dariya ta fashe da ita, ita ba kasafai ma ta cika gane gatse ba a rayuwarta, "Innalillahi! Ni abubuwan nan naku fa dariya suke bani. Ko ba diyarmu ba? Dan Allah daina ma kar kayi sab'o." Kallonta kawai yake tana dariya tana girgiza kai alamar lallai ma. "Ni yanzu nida aure ai saidai a aljanna." Baikai ga bata amsa ba ta jiyo Sumayyah na kiranta.

"Aunty Ramlah, Aunty Lubnah tace kizo zakuyi pictures!" Daga bakin hall din ta tsaya tana magana, juyawa Ramlah tayi kafin ta amsata da toh tana mikewa tsaye.

"Kai tunda kazo amma yi maka picture kuwa? Muje a mana dukanmu da Lubnah." Bai mata gardama ba haka ya mike suka shiga hall din a tare. Dukansu saida akayi pictures din dasu. Koda akazo za'a masu ita da Lubnah kankame ta tayi sunata dariya aka dauka. Anzo anama Rayyan shi kadai da dariyarta tace "Bari in bata maka picture!" A haka ta shiga aka masu hoton a tare.

Daga nan aka cigaba da event Rayyan ya samu waje ya zauna amma duk inda tayi idanunshi na kanta, shi kanshi abun har tsoro yake bashi. Haka daren jiya kaf dakyar ya samu ya saita kanshi ya daina tunaninta yayi bacci. Yau kuwa ganinta da yayi tana waya da Dr Aliyu ba karamin bata mashi rai yayi ba amma haka ya daure ya nuna kamar babu wani abun a ranshi.

Ramlah ce ta karbi camerar daga hannun Idris tana ma Amarya da Ango da friends dinsu picture. Bayan an gama na abokai har ma ana maganar tashi Zainab tace, "Dan Allah Lubnah ki mana, ga friend din Sadiq yazo shida matarshi kuma so suke su tafi." Idanun Ramlah yana kan camera tace "Kai haba, ku tsaya kawai na maku." Da murmushinta ta saita camera tana ji suna raha ana wasa dariya, dagowar da zatayi dan ganin idan sun shirya ta dauka batasan lokacin da numfashi ya tsaya cak ba cikin jikinta.

Jikinta babu inda baya rawa har wani kakkarwar sanyi ta farayi idanunta na neman kafewa. "Shine...wallahi shine..." abunda take furtawa kenan tana baya baya tangal tangal kamar zata fadi. Lubnah wacce hankalinta ya dawo kansu da hanzari ta karasa inda take ta rungumota tana hanyar fita da ita daga hall din bayan ta fadama Idris ya cigaba da daukar hoton.

Dakyar Lubnah ta janyota suka fito hall din, sai nunawa take tana kiran "Shine...wallahi shine..." numfashinta kuwa dakyar take janyoshi.

"Ramlah wanene? Wa kike magana a kai?!" Ai Lubnah bata ida magana ba kawai Ramlah ta fizge jikinta daga nata ta falla da gudu. "Na shiga ukku!" Juyawar da zatayi taga Rayyan har ya bita, zata bi bayansu saiga wata kawarsu tana tambayar lafiya? Kawai sai ta maze, "Tana da ciwo ne amma Rayyan ma ya tafi ya maida ta hotel, ba damuwa." Dan dole ta koma cikin hall dan tasan idan tabi bayan su Rayyan dole hankalin mutane ya dawo kansu.

Ramlah gudu kawai take tana wani irin numfashi na wanda hankalinshi yakai kololuwar tashi. "Shine... wallahi shine..." abunda take iya furtawa kenan. Rayyan ganin idan ya tsaya sai a rasa yanda zaa kamota. Dakyar ya samu ya sha gabanta sai haki yakeyi, ita kuwa cikin kidima take nuna hanyar data biyo, "Shine, wallahi shine..." karshen figewa da tashin hankali ta shigeta babu ma abunda take ganewa, ko ganin gabanta batayi sai duhu.

"Ramlah, ki natsu! Meya faru?" Magana yake mata a hankali amma nema take ma ta kubce mata ta kara rugawa. Yasan hanya dayace zaisa ta dan natsu hankalinta kila ya dawo jikinta. A hankali ya rungumo ta jikinshi yana karanta 'Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun' danshi duk tunaninshi ma aljanu suka shafeta.

MIJINA NE! ✅ Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu