Saida ta jira har motar Lubnah ta wuce kafin da ajiyar zuciya ta juya ta shiga asibitin. Yanzu har ta saba zuwa asibitin, duk kuwa da cewar ba wani cigaban azo a gani bane aka samu, amma ba laifi. Cikin natsuwa take takawa har ta karasa office din Dr Mahmud. Saida ta kwankwasa taji an mata alamar ta shigo kafin ta shiga office din idanunta kyam a kasa har saida ta zauna. Dagowa tayi da niyyar gaishe shi amma sai taga wata fuskar ta daban.
Da hanzari ta fara juyawa tana kallon office din dan taga ko mistake din shiga wani office din tayi, amma sai taga shi dindai ne, dan kuwa komai yana nan kamar yanda ta sanshi. "Ina kwana?" Ta furta a hankali tana kallon bakuwar fuskar data cikata da kallo.
"Ina kwana kema? Ramlah ko? Dan yace mun ke kadai yake da session dake yau." A hankali ta daga mashi kai tana wasa da yatsun hannun ta.
"Yana ina?" Ta tambaya tana dan kara kallon wajen kofa koda zataga shigowar Dr Mahmud.
"Yaje wata seminar ne, bazai samu damar zuwa asibiti ba yau. Ni sunana Dr Aliyu, ni zan zama therapist dinki a yau." Da har tana da niyyar mikewa, amma jin maganarshi yasa ta koma ta zauna tana tunanin yau ma wani sabon me san surutun Allah ya hadata dashi.
Duk tambayar daya mata, kamar yanda takewa Dr Mahmud shima haka ta mishi, babu amsa balle ya saka rai cewar zasu samu wani cigaba. Sai can ya danyi baya yana kallonta yana murmushi, "To yanzu Ramlah, me kikeso kiyi a rayuwarki? Kinga kamar ni inasan karance karance, dukda cewar aikin likitanci yanada cin lokaci, amma no matter how ina samun time nayi karatun novels da poems. Ke me kikeso ta wannan fannin?"
Saida tayi jim kamar bazata amsa shi ba can kuma ta dago tana kallonshi. A karo na farko Dr Aliyu yaga alamar rayuwa a idanta, da wani abu da zai iya kiran zagwad'in abu, wanda a turance ake cema enthusiasm. Da dan guntun murmushi kan fuskarta ta dago tana wasa da hannayenta, "Inasan hoto. Bawai a daukeni ba, Aa, ji na dauki mutane. Ba lallai sai mutane ba, komai na duniya. I love photography."
Murmushi yayi ganin ya samu hanya ta farko da zai samu har ya taimaketa. "To yanzu Ramlah kinasan hoto, in yanzu aka baki camera zakiyi?"
Da murmushi me gaggawa ta daga mashi kai, "Zanyi mana. Akwai abubuwa da yawa a rayuwa wanda bayan hoto dan adam sai ya manta dasu, abubuwan da suka faru da mutum musamman ma na farin ciki. I think photography is the greatest gift to mankind, my opinion though." Mamakin kanta ma take, rabon da tayi magana har ta manta, balle turanci, sai taji abun banbarakwai. Amma a lokuta da dama takan gaza yanda zatayi dan tayi magana mutane su fahimce ta. Dukda cewar batayi wani ilimi mai zurfi ba, amma kuma Allah yayi mata kaifin kwakwalwa.
Magana suke a hankali yana jan hankalinta tana kara bude baki tana mashi magana. Ya lura da wani murmushi dayake kwance kan labbanta, da alamar da gasken fa take san daukar hoto kuma har kasan ranta. Bayan sun gama ya daga waya ya kira number din driver da Lubnah ta bata akan idan ta gama ta kirashi kai tsaye kawai, dan ita tanada taron da zata halarta bai zama lallai ta iya daukar waya ba.
Lambar ce bata shiga ya dago ya kalleta, "To Ramlah lambar direban bata shiga, ya za'ayi kenan? Zaki gane gidan ne sai na kaiki?" Ya tambaya. Gani yayi tayi wani kasak'e kamar wacce aka jefa da kankara kafin ta girgiza mashi kai a hankali.
"Ko ka kira Lubnah?" Abunda zata iya furtawa kenan. Amma ita yanzu ko ranta akace zaa dauka in bata nuna gidansu Lubnah ba ai ta gwammace a daukeshi dan bata gane komai. Yaushe ma ta tsaida hankalin nata waje daya?
"Banda number dinta amma bari na kira Mahmud sai ya kirata." Hakan kuwa akayi. Suna nan zaune suna jiran Mahmud ya kira Lubnah sai gashi ya kirashi daga baya. "Tace zata aiko wani ya dauketa, Aliyu. Nagode sosai fah. Zaka iya magana yanzu akan halin da take ciki ko sai na dawo?"

YOU ARE READING
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...