"Ya Rayyan dan Allah kazo, wai so kake inta rokanka kana man wulakanci?" Dariya ya kara fashewa da ta, ya rasa dalilin dayasa ta raina shi har haka. Dan daure fuska yayi kamar tana gabanshi yana kara gyara zaman wayarshi kan kuncin shi.
"Wai Maryam raina ni kikayi ko mi? Ba ke aure dadi ba? Tunda kikayi aure yaushe rabonki da gida? Har kika haifi yan biyu bakizo ba, to me zakizo yi yanzu? Gulma ko mi?" Abun dadi yake mashi idan yana tsokanarta, gashi magana daya daga Rayyan sai ta gunzuga mata bakin ciki.
"Kaifa kasan ba haka bane ba, Ya Rayyan. Nazo kafin na haifi twins mana, kai Ya Rayyan. Nidai dan Allah kace zakazo." Langabe murya take kamar zatayi kuka, wanda kuma sanin kanta ne koda kuwa Rayyan din zaizo sai ya gama ja mata rai har taji dama tayi kukan.
"Wai yanzu me kike nufi? Kawai sai inzo Lagos dan zakizo Maryam? San da nike maki baikai nan ba gaskia." Dariya ya fashe da ita jin yanda ta wani bata rai.
"Yaushe rabon da in ganka? A tattara kusan shekara ukku kenan fa Ya Rayyan. Rai ake mawa, kar kazo ka mutu ko in mutu muzo dayanmu yana dana sani."
"Zaki fara yan maganganun naki ko? Ba mun hadu wancan zuwan da kikayi ba bayan biki? Ko bai isa ba?" Duk duniya babu abunda ya tsana kamar Maryam ta mishi maganar mutuwa, ita kadai ce kanwarshi wadda suke uwa daya, shi kanshi baisan adadin san da yake mata ba.
"A airport ko? Lokacin kaje Switzerland, ko ka manta? Ranar daka dawo ni kuma zan tafi muka hadu airport, ko minti talatin bamuyi ba kowa yanaso ya wuce. Kai kaje gida ka huta ni kuma kar nayi missing flight dina. Dan Allah, Ya Rayyan kazo, dan Allah."
"Naji zanzo, yaushe zaki taho? Ni banma taba tunani zakizo ba tunda naga Germany ta fiye maki Nigeria, miji yafi yan uwa da iyaye." Dariya ya kara fashewa da ita jin yanda ta wani marairaice.
"Munyi magana da Abdallah yace cikin next month, ban sayi ticket ba tukunna. Dana siya zan fada maka. Koma dai kai zaka daukoni daga airport din?" Ta tambaya tana janshi da dariya.
"Zanfa zane yarinya, ni sa'an wasanki ne? Ko direbanki na zama ban sani ba?" Da dariya itama ta maida mashi.
"Yarinya fa yanzu ta girma, tana da mijin da zai rama mata in aka zalince ta. Naji ance kana Abuja, koma ta nan zan sauka?"
"Bafa a gidana nake zama ba, Abba ya dage dole na zauna gidansu Lubnah. Ki sauka ta Lagos din kawai yafi, nima ranar da zakizo zan koma gidan." Duk wacewar dak'ik'a daya sai hayaniyar wajen ta kara yawa, a hankali ya sulale ya fara fita daga cikin mutanen yanaso ya koma dakinshi na hotel ko bacci yayi ya fiye mashi wannan hayaniyar.
"Wai har yanzu dai Abba yana kan maganarshi, Allah dai ya zaba maka mafi alkhairi, inga dan yayana yayi aure, zanyi wulakanci bikin ka. Kana inane haka?" Dariya yayi yana kada kai irin yarinyar nan baki da hankali.
"Wallahi munzo Maiduguri wani biki ne, kinga ko..." dama kidan ganga kura sukeyi, shi ko kallon inda matan suke ma bayayi balle yaga halin da suke ciki. Juyawar da zaiyi kawai idanshi ya hango mashi Ramlah. Rausayawa take sai wata irin dariya da bai taba gani a fuskarta ba. Lubnah take kallo suna rawa tare, da alamun yanda take bin dukkan wani taku na Lubnah zakasan so take ta koyi rawar. Data dan goce sai ta fashe da dariya ta cigaba da rawar. "Hasbinallahu wa ni'imal wakeel..." abunda ya furta kenan da hankali. Yasan tabbas matan Maiduguri idan suna wannan rawar ba karamin daukar hankali suke ba, amma duk cikin matan nan da suka kware da rawar, babu wacce ta burgeshi face Ramlah. Yar rausayar da suke, juyawar da suke suna wani watsa hannu ga abun turaren wuta. Innalillahi.
Dariyar mugunta Maryam ta fashe da ita, "Ya akai, Ya Rayyan? Gamo kayi ko mi?"
"Maryam, idan mace tana rawa haka take ko kuwa kai kake ganin kyanta?" Yasan Maryam kila har duniya ta nad'e saita rika janshi da wannan abun amma kuma bazai iya daurewa ba sai ya tambayeta.
"Shikenan, halan rawar ganga kura sukeyi? Naji kidan." Dan daga nata kai yayi kamar yana gabanta, "Wacece tayi kyan da kake tunanin ko haka take? Ka santa?"
"Sunanta Ramlah..." sai kuma yaji karma Maryam ta bata mashi lokaci, "Ke sai anjima. Kuma kika jani kan maganar man zan zane yarinya."
Dariya ta fashe da ita, "Yarinya dai tana da mijin da zai rama mata." Kashe wayar yayi kawai ya kyaleta. Gaba daya hannayenshi ya nade saman kirji yana kallonta. Yasan koda ya daukota ba karamin kyau tayi ba, baisan ko hada ranar da take sauka bane sararin samaniya yayi wasu kaloli masu ban sha'awa. Sannan ga kidan dake tashi, ga yanayin shigarta kawai ma, ga murmushin da take wanda da tayi kuskure wajen rawar zakaga ta fashe da dariya. Shidai tunda yake bai taba ganin abunda ya burgeshi ba kamar Ramlah yau.
Baisan ya akayi ba, shidai yasan idanunshi kanta kamar an karkato da ita kawai ta juyo tana kallonshi. Wani irin kayataccen murmushi ta zuba mashi tana dago mashi hannu alamar taga wanda ta sani. "Ko zakayi rawar?!" Da farko bai gane mai take nufi ba, ga hayaniyar mutane gata kidan dake tashi. Labbanta ya koma yana kallo, "Ko zakayi rawar?" Ta kara furtawa tana nuna mazan dakeyi daga gefe.
Girgiza mata kai yayi, "Maza basa rawa ai." Dama idanunta kyam kan labbanshi, kallo daya tayi ta gane abunda yake nufi.
"Su wadannan ba maza bane?" Mikama matar dake gefenta abun turaren wutar tayi tama dora hannayenta saman kugu. Akwai tazara sosai a tsakaninsu, amma magana suke kai ka dauka gata gashi. Duk wanda ya lura da abunda sukeyi babu abunda zai hana yayi tunani sunyi shekara da shekaru suna soyayya.
Dan langabar dakai yayi yana yar dariya, "Mata maza ne, baki gani ba?" Da hannu ya nunasu yanda suke rawa dan wasu cikinsu yanda suke karya kugu yafi na matan karyuwa.
Dariya tayi ta girgiza kai alamar Allah ya shiryeka. "Yan daudu ake cewa, su kuma wadannan bakaga kayan maza bane da hula saman kansu? Indai zaka shigo ka shigo, in baka iya bane sai na koya maka."
Kara gyara tsayuwarshi yayi yana kara jingina kanshi jikin mota, "Naga bobrisky karshen daudu. Indai zaki koya man to zanyi." Hayaniyar mutanen kara yawa tayi, dan wasu bakin ma sai yanzu suke zuwa. Ganin gane abunda take fada zaiyi wuya yasa kawai Rayyan ya zaro wayarshi dake cikin aljihu ya kirata.
Dago wayar tayi ta kalleshi kafin da murmushi ta dauki kiran, "Da gaske zakayi rawar?" Abunda ta fara furta mashi kenan, shi kuwa Rayyan yana kallon dukkan yanayin dake kan fuskarta.
"Indai zaki koya man. Amma mutane sunyi yawa a nan wurin, ni ba na mata bane ba." Kamar wasa yaga tana takowa, zuciyarshi har wani tsayawa tayi ganin yadda wani murmushi yayi mazauni saman labbanta ga tafiyar da takeyi cikin lafayarta, shidai yau ranshi kawai yai saura a jikinshi.
Har saida tazo inda yake tukunna ta ciro wayar daga kuncinta, "To sai anjima, Rayyan." Ta furta tana kallon wayar kafin ta kashe call din, wata irin dariya yayi wacce baisan yanda akayi ta fito ba. Ya rasa gane muryarta wacce tafi dadi? A waya ko a fili. "Nima ban iya sosai ba, Lubnah yanzu ta koya man, kuma suna can ana kaman siyan baki ne koma menene ohon masu."
"Wai ohon masu, Allah ya shiryaki, Ramlah. Eh inaso, amma saidai kawai in kalleki kinayi dan nikam bazanyi ba."
Turbune baki tayi tana harararshi ta wasa, "In rawar kakeson gani ga wadanda aka haifa cikinta nan." Juyawar da zatayi sai taga daya daga cikin matan dake zubawa baki abinci zata wuce da plate din snacks sai drinks a hannunta. Da hanzari tace, "Dan Allah ko zaki dauko wani?" Babu gardama matar da murmushi ta mika mata ta juya dan ta dauko wani.
"Haka kawai Babbar mata sai ki aiketa, Ramlah?" Da mamaki yake kallonta yana dariya.
"Ai ba aikenta nayi ba, harda dan Allah ta. Yunwa nakeji, ina zanci abinci?" Juye juye ta farayi, ganin duk fadin gidan babu inda zataci abincin yasa Rayyan ya karbi plate daya daga wajenta.
"Muje inda babu mutane, babu ma me kallonki. Mazan can kamar zasu cinye ki danya." Dariya ta fashe da ita tana fara tafiya, jerawa sukayi a tare.
"Ka san ko? Da ace da ne, yanda kayi maganar nan da yanzu saidai ka ganni tsaye gabansu ina tambayarsu dalilin kallona, amma yanzu na shiryu." Dariya yayi kafin ya girgiza kai, ashe dai tana magana, ashe kuma tayi rashin ji?
Mota suka karasa ya bude mata ta shiga kafin ya shiga shima. AC kawai ya kunna masu gashi glass din tinted ne babu yanda za'ayi na waje na gansu. A tare sukaci abincin, saida suka gama ta juyo tana kallonshi, "Na bata kwalliyata ko?" Babu madubi balle taga kanta, kuma kamar an hanata sauke glass din ta duba.
Tissue ya zaro yace "Tsaya, kin dan bata janbakin ki." Cak ta tsaya tana kallonshi har ya gama goge mata inda janbakin ya bata kafin ga kalleta da wani kyakyawan murmushi. "To yanzu yayi. Kinyi kyau kamar kece amaryar."
YOU ARE READING
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...