Mikewa yayi tsaye yana kallonta da yar dariya sannan yana kallon kofar, "To Ramlah, tunda nidai yanzu ba'a so na ga Dr Aliyu nan sai ki mishi magana shi." Ko kadan baiji haushi ba, in baccin ba dadin da yaji dan alami sun nuna da taimakon Dr Aliyu akan iya ceto rayuwar Ramlah, tunda har tafi sakin jiki dashi.
Dan dukawa tayi tana wasa da yatsunta tana murmushi irin na kayi hakuri, ta kusa minti sha biyar office din Dr Mahmud amma duk tambayar da zai mata bata ce mashi k'ala. karshe dai yace mata ko a kira mata Dr Aliyu, sai a lokacin ta daga kai ta mashi magana akan eh. Yanzun ma da murmushin jin kunya ta dago tana dan girgiza kanta.
"Allah ba haka bane ba." Ta furta a hankali, shi kuwa Dr Mahmud dariya yayi yana daukar wasu takardu kafin yayi hanyar kofa, jnda sabo ya saba da halin Ramlah yanzu. Tun ranar da suka fara therapy session da Dr Aliyu daga ranar kullum saidai ya kira mata shi, bata taba yarda tayi magana dashi.
"Na saba yanzu nikam, kila ma dai daga yanzu da kinzo zan maki kwatancen office dinshi ba sai kun rika tadani office dina ba." Da yar dariya Dr Aliyu ya dan bugi kafadarshi kafin ya karasa kujerar zamanshi ya zauna. Saida ya jira Dr Mahmud ya rufe kofar kafin ya dago yana kallonta.
"Ramlah, an tashi lafiya?" Abunda ya tambaya kenana ita kuma ta dago ido tana kallonshi tana murmushi a hankali. Dama labari take san bashi.
"Lafiya lau. Ina kwana?" Ta mayar mashi da martani. Shidai baisan dalili ba amma Ramlah tana burgeshi, kuma sosai ba kadan. Dukda cewar tarin damuwar da take ciki yak'i barinta ta kwantar da hankalinka amma daga ganinta sai ta burgeka kuma sai kaji kanasan taimaka mata da dukkan wani iko da Allah zai baka.
Murmushi yayi a hankali, "Ina kwana kuma? Saidai ina yini, dan yanzu babu dadewa sha biyu zatayi yan makaranta su tashi. Kinga yau juma'a ai." Dan kada kai tayi alamar ta tuna, amma a zahirin gaskia idan ba yanzu daya fadi ba ita bata ma gane ranakun mako, kawai dai rayuwa takeyi gata nan dai ita.
"To ina jinki, ya photography class din? Akwai dadi? Kinyi pictures?" Ya tambaya yana kureta da idanu, itama dagowa tayi da fara'arta alamar zatayi maganar abunda takeso.
"Sosai, inajin dadin zuwa class din. Na manta camera din a gida dana nuna maka."
"To yanzu akwai abunda kikeji dama ace kinada ikon maidawa baya ki dauki hotonanshi dan karki manta?" Shi wani lokacin har taka tsantsan yake wajen tambayar da zaiwa Ramlah, dan cikin minti daya tana iya chanzawa baki daya ta koma Ramlar ta tada.
Dan jim tayi da kamar bazata amsashi ba sai can kuma ta daga kai a hankali, "Hanan. Kullum na kalli camerata sai inji dama zan iya komawa baya dukkan rayuwar da mukayi da ita in dauka hoto. Dariyarta, murmushinta, yanda take bacci, rigmarta, kukanta, wasanta, komai nata." Sai kuma tayi shiru, dan tunawa da tayi da lokacin da Hanan tana raye ba karamin fama mata tabon dake zuciyarta yayi ba, wanda a kwanakin nan babu abunda batayi dan taga ta goge shi tayi rayuwa kamar kowa, kamar yanda Lubnah da Mama sukeso suga ta rayu.
Tunda take yau ce rana ta farko data taba yin magana akan rayuwarta ta baya, wanda hakan ba karamin dadi yama Dr Aliyu ba dan kuwa an samu cigaba sosai ma ba kadan ba. "Wacece Hanan din? Tana ina?" Hawayen dayaga sun zubo mata yasa yaji dama bai mata tambayar ba, amma kuma hakan ne kadai zai kara taimakonta.
Da kamar bazatayi magana ba sai can kuma ta fara, "Ta rash, diyata ce, shekararta biyar. Da inada iko dana koma rayuwarmu ta baya, komai nata nayi recording, har yanda ta koma da ciwonta yayi tsanani, yanayin yanda take kallona da zafi da radadin ciwo tana ceman Ammi. Har gawarta dana dauka, dan wataran sai naji kamar Hanan dita bata mutu ba, har muryarta inaji tana kiran sunana." Zuwa yanzu kuka take kamar ranta zai fita, watanni sun shude, amma Ramlah ta rasa yanda zatayi ta rage zafi da radad'in mutuwar Hanan a cikin zuciyarta.

YOU ARE READING
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...