"Ya kuwa nuna maki yaga sakon?" Ramlah ce ta juyo daga zaunen da take tana kallon Lubnah dake tuki hankali kwance. Yanzu suka gama waya da Zainab wacce sai masifa take mata akan wai bazatazo ba take nufi ko mi? Ita dai sai dariya take, dan batasan ta fada mata cewar gobe zata isa garin.
Dan juyowa tayi amma hankalinta yana kan titi, "Wai Rayyan? Ki barshi fa Ramlah, ni wallahi banma san yanda zanyi ba. Ga haushin kaina da nakeji dama bamu turo sakon ba. Kuma kinsan ko yau mun hadu da zan tafi office, muka gaisa lafiya lau kowa ya kama hanyar gabanshi." Wani dan guntun tsaki taja alamar haushin kantan takeji da gaske. Ita da tasan bama zai nuna mata yaga sakon ba ai da bata yarda an tura sakon ba.
Ramlah itama tsakin tayi, wayar Lubnah dake kan hannun kujera ta dauka dama tasan password dinta. Bude wayar tayi tayi searching number din Rayyan, Lubnah bata san abunda yake faruwa ba saida taji karan waya alamar wani take kira. Juyowa tayi taga wayarta ce hannunta, "Wa zaki kira, Ramlah?"
Har Ramlah zata bata amsa taga alamar an dauka, dama wayar a speaker take da hanzari tayi ma Lubnah alama da tayi shiru. "Assalamu Alaikum, Lubnah?" Muryar Rayyan taji, daga jin sautin waka dake fita a hankali kasan yana cikin mota.
"Na'am, ina yini? Ramlah ce. Tana tuki ne kuma muna cikin traffic sai tace na kiraka. Kana ina dan Allah?" Koda can asalinta ita bata saba boye abu cikin ranta ba, koma menene indai yazo mata cikin rai to babu makawa sai ta furta shi saidai ayi yanda za'ayi da ita. Saima da rayuwa tayi mata juyin waina kafin nan ta nemi duk wani confidence dinta da wani straightforwardness dinta ta rasa. Yanzu haka ma mamakin kanta takeyi, ashe dai mai hali bai chanza halinsa.
"Ina hanyar komawa gida, lafiya dai ko?" Ya tambaya yana kallon wayar, dan yanda yani Ramlah tayi magana sai ka rantse da Allah kace ba ita bace ba. Dukda kuwa dama ya lura kwana biyun nan ta saki ranta, dan wani lokacin idan yazo gaida mama daga dakinta yana jiyo dariyarsu da Lubnah.
"Akwai abunda zata nuna maka, yanzu dai muna hanyar zuwa shagon..." sai kuma tayi shiru, bata san shagon dinkin ba. "Ya sunan shagon ma?"
"Hudayya, shagon dinkin Hudayya." Jiki a mace Lubnah ta bata amsa, dan ita kanta nan cike take da mamaki, bata taba tunanin Ramlah tana da confidence din yin hakan ba.
"Yauwa, shagon Hudayya. In yana kusa ka biyo dan Allah." Saida yayi shiru kafin yace, "To shikenan, kila ma na riga ku isa wajen." Daga haka Ramlah ta mashi sallama ta juyo tana kallon Lubnah wacce tayi mutuwar tsaye.
"Kin gani ko? Yanzu dai wallahi indai har baki mashi magana ba ko Allah ya isa nai maki saita kamaki." Wata irin dariya suka fashe da ita a tare.
"Ni wallahi tsoro naji, ban taba tunanin zaki kirashi ba Ramlah, na bani." Har yanzu Lubnar dariya take, kuma manaki ne fal ranta. "To mi zance mashi? Za'ayi bikin kawata inaso muje tare? Ko so kike in gaya mashi san da nike mashi?"
Da hanzari Ramlah ta girgiza kanta, ita tasan a duk duniya yanzu babu wanda zata iyama irin abun nan sai Lubnah, dan ita da maza ma akan iya cewa haihata haihata. "Kai haba, karki gaya mashi. Amma me, dole ya fara sanki a Maiduguri Insha Allahu."
Daga haka sunata tsara yanda za'a tambayeshi zuwa biki har suka isa shagon kamar kau yanda yace haka suka ganshi jingine jikin motarshi yana latsa waya. Ramlah juyawa tayi taga jikin Lubnah har yayi sanyi. "Dan Allah ina confidence din naki? Karki bani kunya. Kawai be yourself, it's natural to ask mutum yazo maka biki ai. Ni da kikace inzo muje bakiji wani abu ba?"
Saida Lubnah tayi parking kafin takai ma Ramlah dukan wasa, "To ke namiji ce? Ko sanki nike?"
Ramlah fita tayi daga motar tana dariya wanda jin sautin dariyar nata ne ya dawo da hankalin Rayyan a kansu, dan bai lura da suna wajen ba saida ya jiyo sautin dariyarta. Tsayawa yayi kawai yana kallonta tana dariya kafin ya jiyo ta tana fadin, "In baki sona to ni ina sanki."
Daga haka Lubnah itama ta fito motar tana dariya, daidai idanunsu ya hadu dana Rayyan, zuciyarta har wani bugawa tayi tsabar kyaun da yayi mata. Saurin saita kanta tayi daga haka ya karaso inda suke. Saida suka gaisa kafin ya kalli shagon ya kallo Lubnah, "Dinki zaku karba?" Ya tambaya lokacin har sun fara takawa hanyar shagon.
"Eh, muje." Dan tsayawa yayi yana kallonta yana yar dariya, "Maza na shiga ne?" Dariya tayi tana daga mashi kai, "Yayar kawata ce me wajen, ko basu shiga sai ka shiga balle ma suna shiga." Ita dai Ramlah dan gaba kadan tayi dan ta bama Lubnah damar yin maganar daya kamata.
Da fara'a matar tazo ta tarbesu bayan sun zauna ta juya ta kalli Ramlah da sai kallon mannequins din dake da kaya jikinsu takeyi. "Wannan itace Ramlar? Baki samu damar kawota ba amma kamar yanda kikace size dinku daya nayi, amma gaskia zata gwada kayan dan muga in yayi ko sai an buda ko a rage."
Ramlah da hanzari ta juya ta kalli Lubnah, "A nan?" Girgiza mata kai Lubnah tayi, "Akwai fitting room, an zaki chanza." Bin bayan wanda akace ta kaita fitting room din tayi, ita kuma matar dama sauri take gida zata tafi mijinta na jiranta tama Lubnah sallama akan inma da wani abu ma'aikatanta zasuyi komai da komai.
Lubnah juyawa tayi ta kalli Rayyan, ganin in ta tsaya shawara da zuciyarta bai zama lallai tayi maganar ba. "Biki zamuje, kawata zatayi aure. Gobe zamu tafi." Tasan yanda ma tayi maganar yasha lallai da yanda ya kamata amma ita kanta batasan ya zatace mashi ba har ga Allah.
"Oh, yi hakuri dan Allah, naga message dinki bazan samu...." bai ida magana ba sukaga Ramlah ta fito cikin gown din dinner din da aka dinka mata. Wata tsinkewa zuciyarshi tayi. Har yanzu dan kwalin abayarta ne kanta amma sai ka rantse dama dan gown din aka yishi. Baisan lokacin daya juya ya kalli Lubnah ba, "In kikaje dani bikin kice ma kawarki wa? Dama ana zuwa biki da maza ne?" Dariya sukayi a tare, shi kanshi yasan ba abunda yayi niyyar furtawa ba kenan amma saidai a kasheshi shi kanshi baisan dalilinshi na chanza ra'ayi ba.
"Ana zuwa mana, zance mata ga abokaina kaida Ramlah, dama tanata so fa ganku ai." Magana Lubnah takeyi, kuma a ido ita yake kallo amma ta wuysihar idonshi Ramlah kawai yake kallo. Yanda take juyawa tana kara kallon kanta a madubi tana turbune baki wai ita wallahi sun matseta. Ma'aikaciyar sai kokarin nuna mata cewar matsewar ba wani bace, banbancinsu da Lubnah wajen hips ne kawai kuma shima ba wani cancan ba, zata iya sakawa a haka amma Ramlah sam batasan zance ba.
Takowa Ramlah tayi har inda suke zaune tana kare ma jikinta, "Lubnah dan Allah kalli fah, nidai kice masu su dan buda man kadan. Ni dama A shape suka man gown din."
Hankulansu gaba daya komawa sukayi kam Ramlah, da gaske ita bataso ba, bakinta har yanzu a turbune yake, "Ramlah nidai banga matsewar da rigar nan tayi ba tsakani da Allah." Juyawa Lubnah tayi tana kallon Rayyan, "Ko kaga matsewarta, Rayyan?"
Dama can a dardar yake kallonta bayaso daya daga cikinsu ta gane yana kallonta, amma tambayar nan ba karamin dadi ta mashi ba dan dan zai samu ya kalleta san ranshi. Juyawa yayi suka hada ido, "Dan Allah zakace kaima bakaga matsewar ba? Lubnah kalla fah!" A hankali tayi twirling dan su gani din. Shi tunanin ma da yakeyi wai dama haka take ko kuwa rigar ce?
"Nidai ban gani ba, amma idan ta matseta ku dan buda mata kadan mana." Yadda Ramlah ta dage dole ma'aikaciyar nan ta jiya taje ta maida kayanta kafin ta dauki wani awon nata dan kar a koma gidan jiya. Ramlah na dawowa ta zauna taga suna fira sama sama.
"Zaije din ko?" Tambayar da tayi kenan, saida ta furta hakan kafin ta tuna da karfi tayi maganar kuma babu makawa yama jita.
"Eh zanje kafin budurwar Dr Aliyu ta kaini kara wajenshi." Da dariya yayi maganar sai kuma ya juya yana kallon Lubnah, "Kin tambayi izinin shi ko, Lubnah? Kar yazo firar dare ace bata nan muga mutum Maiduguri." Tare shida Lubnah suka fara dariya.
"Innalillahi, wai sau nawa zan maimaita maku..." saurin katseta Lubnah tayi.
"Mun sani, ke ba sanki yake ba kema haka. Diyarshi kawai take sanki saiyasa kuke gaisawar mutunci, munsha jin wannan labarin Ramlah." Ai Lubnah bata ida rufe bakinta ba wayar Ramlah dake aje kan kujera ta fara ringing. Da hanzari Lubnah ta dauka tana wata irin dariya kafin ta haska ma Rayyan dan yaga wa yake kiranta, "Ka gani ko Rayyan? Anjima ma sai yazo, yanzu kuma da munyi magana ace mana ba haka ba." Dariya sukeyi a tare suna kallon yanda ta bata fuska.
"Anshi ki karbi call fin kar ta katse a fara mana kuka yanzu." Bakinta a turbune ta karbi wayar tayi hanyar fita shagon gaba daya.
"Kice mashi ina neman alfarma zan tafi dake, in kuma yanada lokaci yo yazo muje tare!" Da dan karfi Lubnah tayi maganar yanda zataji shi kuma Rayyan yanda ta bata ran tana turbune baki shi ya bashi dariya.
ESTÁS LEYENDO
MIJINA NE! ✅
RomanceAshe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana...