*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareedah Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA ƊAYA*
Wani ƙayataccen murmushi ne ya suɓuce a kyakkyawar fuskarsa lokacin da yaji yana ta magana ta yi shiru, sai saukar numfashinta a hankali da yake ji yana bugun dodon kunnensa, bisa ga dukkan alamu ta yi barci kamar yadda ta saba a mafiyawancin lokuta idan hirarsu tayi tsawo. Lumshe idanu yayi yana saurarenta, har lokacin murmushin da yake yi bai bar fuskarsa ba. Tunanin Da ma a ce a daidai wannan lokacin tana kwance akan faffaɗan ƙirjinsa tana barci ne ya saka shi ƙara faɗaɗa murmushinsa. A hankali yadda bazai tashe ta ba ya cigaba da magana
"Yau ma barcin kika yi Haneeta? Ga shi ni kuma ban gaji da sauraren lallausar muryarki ba. Amma ya zanyi? Dole zan ƙyale ki kiyi barci don bana so in tashe ki ki kamu da ciwon kai saboda rashin samun wadataccen barci. Ina miki fatan samun barci mai daɗi cike da kyawawan mafarkaina. Kin ji ko Haneeta? Nima ina jiran zuwanki a mafarki, ina roƙon alfarma don Allah yau cikin barcina kizo min a mabanbancin yanayi... I love you.!" Yaja sumba a hankali ya sakar mata iskar a cikin kunnenta. Ƙit ya katse wayar yana sosa ƙeyarshi, wayar ya ɗora a ƙirjinsa har lokacin bai buɗe idanunsa ba. Zuciyarsa cike fal da matsananciyar soyayya da tunanin Haneepha. Tsananin son da yake mata yasa ya cire 'pha' na ƙarshen sunanta yana kiranta Haneeta, bai taɓa cire ran ita ɗin za ta zama tasa ba.Da wannan tunanin wani nannauyan barci yayi awon gaba da shi ba tare da yayi addu'ar barci ba.
*2:48am*
"Bashir...! Bashir...!!"
A hankali yaji ana ɗan bubbuga gefen kafaɗunsa ana kiran sunanshi. Sannu-sannu yake buɗe idanunsa da suke cike da barci har ya buɗe su gaba ɗaya ya zuba a cikin nata da suke fari fat babu ko ɗigon baƙi a ciki. A tsorace ya kauda idanunsa daga cikin nata, ya yunƙura zai miƙe zaune sai yaji kamar an ɗaɗɗaure shi a kan gadon da yake kwance. Da sauri ya fara waige gefe da gefe na cikin ɗakin sai yaga ai ba a ɗakinshi yake ba, a tsakiyar dokar daji yake kwance akan gadonshi."Me kake nema ne Bashir? Ko baka gane ni masoyiyar taka Haneepha ba?" Tayi maganar da wani irin murya mai rawa cike da amo mai tsoratarwa.
Tun daga ƙasa ya fara kallonta har ya dire a kyakkyawar fuskarta da in banda fararen idanunta da babu ko ɗigon baƙi a cikinsu babu abinda ya canza a kamannin fuskarta. Tana sanye da doguwar riga fara kar da ya sauka mata har ƙasa ya rufe ƙafafunta. Ya buɗe baki da niyyar yin addu'a sai yaji kamar an saka ƙugiya an naɗe harshensa.
Ta haske shi da murmushi da jajayen haƙoranta. Sai kuma ta fara matsawa daf da shi tana cewa
"Na zo inyi maka sallama ne... sai wata rana masoyi Bashir..."
Yana ji yana gani tayi amfani da dogon ƙumbanta mai shegen kaifi da tsini na yatsarta manuniya ta yanke jijiyar hannunsa na dama, nan take jini ya fara tsiyaya. Murmushin da babu ko kyan gani ta ƙara sakar masa
"Karka damu masoyina... Wannan ita ce soyayya ta gaskiya a waje na. Ina maka albishir TSAKANINA DA MUTUWA akwai amintaka mai ƙarfi, tayi min alƙawarin baza ta wahalar dakai lokacin wucewa barzahu ba." Tasa hannu da ƙarfin tsiya ta fincike agarar ƙafarsa ta hagu jini ya ɓalle sannan ta ɓace ɓat kamar anyi ruwa an ɗauke.Duk iya kici-kicin da yake yi ya kasa ko da ƙwaƙƙwaran motsi balle har ya iya buɗe baki ya ƙwalla ihu don a kawo mishi ɗauki. Yana ji yana ya fara galabaita da ganin hazo-hazo saboda yadda jini ke fita daga gurare biyu da ta yiwa illa. Lumshe idanu yayi yana ayyana kalmar shahada a zuciyarsa, don ya san tasa ta ƙare!!!
******
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un! Wayyo ni! Wayyo rayuwata!! Na shiga uku na lalace.!!! Wayyo Allah na..." Haj Altine take fada cikin karajin kuka da kururuwa tana buga kanta da bango kamar taɓaɓɓiya. Takai gwauro takai mari ta ɗora hannu bibbiyu akai ta sake yanka ihu ta cigaba da sambatun da in a cikin nutsuwa da hayyacinta take baza tayi ba.
"Haba mutuwa! Wallahi bakiyi min adalci ba. Mai yasa baki daukeni ni tsohuwa kin tafi dani ba za ki daukar min ɗa ɗaya tilo da Allah Ya bani? Shi kaɗai ke gare ni mutuwa me yasa?!..". Ta sake rushewa da wani ƙaƙƙarfar kuka ta zube a ƙasa tana gurnani kamar za ta tashi aljanu.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari