*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA SHIDA*
"Ɗan malam! Ɗan malam!! Ɗan Malam!!!".
Sautin amsa kuwwar muryoyin mutane mabambanta da suke ƙwalla kiran sunanshi haɗe da kururuwar murna da farin cikin ganin irin nasarar da yake samu shi ne abinda yake ƙara mishi ƙarfi da karsashi, ƙara zillewa da ƙwallon yake yi yana ta yayyanke abokan karawarsu duk da yadda suke ta kai mishi duka a dabarance kuwa. Bai saurara ba sai da ya samu nasarar jefa ƙwallo na uku a raga duk da saura minti ɗaya kacal ya rage a tashi wasan.
Nan take kuwa filin ya sake kaurewa da ihun murna da sowar kiran sunanshi don tsananin farin cikin nasarar da ya samo musu.
Ƴan club ɗinshi da suke buga ƙwallon tare ihu suka saka sannan da gudun tsiya duk suka nufi inda yake suka rungumeshi suna juye-juye da shi a tsakiyar filin suna rera mishi baitin kirarin da suka saba.
Wasu kuma suka zube a ƙasa suka yi sujjada suna godiya ga Allah kan wannan nasara da suka samu bayan sun riga sun cire rai da samun nasarar, sun san samun nasarar ba komai bane face iko na Ubangijin sammai da ƙassai.
Waɗanda ba musulmai ba kuma suka yi can-cak suka ɗaga shi sama suka ɗora a saman kafaɗunsu suna zagaye da shi a tsakiyar filin haɗe da waƙe-waƙe irin nasu na ƴan ƙwallo. Shi kuwa ya hau dagawa mutane hannu wadanda suke kara kwarzaba shi.
Abokan karawarsu da sauran tawagar tafiyarsu kuwa kallo ɗaya za ayi musu a fahimci tsantsar baƙin cikinsu da takaicin rashin nasarar da suka yi, domin abin ya zame musu kamar ta leƙo ta koma ne. Sai da suka ci biyu ba ko ɗaya, amma tunda aka canza wani sulluɓaɓɓen ɗan wasa aka maye gurbinsa da Ɗan Malam lokaci ɗaya wasan ya canza.
Wani irin mugun kallo suke jefa ma Ɗan Malam suna cin alwashi a zukatansu, duk da tun kafin suzo sun samu labarin irin nasararsa da ƙwarewarsa amma sun sha alwashin ko ana ha-maza-ha-mata sai sunci nasara, shi yasa ko da suka ga a zagayen farko babu Ɗan malam wani irin dariya suka yi na farin ciki haɗe da karkaɗa kai. Da wannan dalilin yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka zura musu ƙwallo biyu a raga su kuma daƙyar suka zura ɗaya.
Sun gama sakankancewa da cika bakin su ke da nasara sai ga shi komai ya zama tarihi cikin ƙanƙanin lokaci. Suna ji suna gani kofin da suka sha alwashin tafiya da shi aka danƙawa su Ɗan Malam. Da wannan takaicin suka bar filin wasan bayan sun sha alwashin dawowa nan gaba ba da daɗewa ba.
*
Ya cire rigar jikinsa kenan aka kai mishi wata wawuyar runguma ta baya haɗe da fara sakar mishi wasu zafafan sumba a duk inda laɓɓanta suka sauka, tana yi tana goga mishi tudun ƙirjinta a gadon bayanshi. Runtse idanu yayi cike da shauƙi yana amsar irin saƙonnin da take aika mishi da shi.
Duk da cewa bai juya ya ga ko wacece ba, ƙamshin turarenta ya gama bayyana mishi wacece ita.
"Karishma..!"
Ya kira sunanta a hankali daga can ƙasan zuciyarshi zuwa saman laɓɓanshi."Uhmmm my champion! Congratulation Albasa na!", ta faɗa cikin karaɗin murna da zazzaƙar muryarta, tana ci gaba da kai mishi sumba ta ko wane ɓangare a bayansa.
Gorar ruwan faro mai sanyi da yake ajiye kusa da inda yake tsaye ya ɗauka ya kafa a baki, bai sauke ba sai da ya shanye tas sannan yayi cilli da gorar.
Yana haramar juyo wa ya mayar mata da martanin rungumar da tayi masa ya ji a tsiyace an janye ta daga bayansa, ƙarar saukar marin da ya biyo bayan janye Karishmar a jikinsa shi ya saka shi sakin wani ƙayataccen murmushi.
Cike da ƙasaita ya juyo yana kallonsu, murmushin da yake yi har lokacin bai bar kan fuskarsa ba. Ya kalli Haly da take tsaye ta riƙe ƙugu da hannu biyu tana girgiza jiki cike da masifa da mahaukacin kishi, sai huci take fuskarta na bayyana wani irin fushi da bala'in da ke cinta.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari