*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA GOMA SHA TAKWAS*
Wani irin sassanyar tuƙi yake yi yana bin ƙira'ar Sudees dake tashi sannu a hankali ta cikin speekar motar, ko da ya shiga cikin asibitin ya daɗe a zaune cikin motar bai fito ba. Haka kawai yake jin wani nishaɗi da farinciki yana kwaranya a cikin zuciyarsa.
'Lallai cikin karatun alƙur'ani akwai farin ciki, nutsuwa, da walwala.'Ya ayyana hakan a ransa, kafin ya fito daga gida sam yanayinsa babu daɗi. Haka ya wayi garin yau jikinsa a sanyaye kuma ransa a ɓace.
Yayi ta hura hanci yana ciccin magani yana jira Safiyya ta taɓo shi ya sauke duk wani ɓacin ranshi a kanta. Amma da yake Allah yai mata gyaɗar dogo tun da ta kalli yanayinshi cikin kiyayewa da taka-tsantsan ta haɗa mishi ruwan wanka ta saaɓe zuwa ɓangarenta bata sake waiwayarshi ba.
Da yake duk monday da alhamis yana azumin taɗawwa'i shi yasa ba wani wahalar haɗa mishi abin karyawa. Haka yai ta laluben laifi ya maƙala mata amma bai samu ba.
Ko da ya shiga ɓangarenta da niyyar ya balbaleta da masifar bata tsaya ta fito mishi da kayan da zai saka ba bayan da can ba ita take zaɓa mishi ba, domin ko ta fito mishi dashi sai ya ce ba wannan kayan zai saka ba. Sai ya tarar da ita a banɗaki, da gangar taƙi fitowa tayi luf har sai da taji fitarsa, can kuma sai taji tashin motarsa ya fice daga gidan gaba ɗaya.
Tsawon lokaci yana zaune a cikin motar har sai da Suratur-rahman ɗin yake bi yakai ƙarshe, ya kashe radion motar, ya zare makullin ya riƙe a hannu sannan ya yunƙura da bismillah ya buɗe ƙofar motar ya fita waje.
Ringing ɗin wayarsa ne ya dakatar da shi daga yunƙurinsa na nufar cikin asibitin, ya cirota daga aljihun gaban rigarshi ta dakekiyar shadda ya duba.
Wani ƙayataccen murmushi ya sake ganin wacce take kiranshi, sabuwar budurwarshi ce Jazeela Baby.
Cikin satin da ya wuce suka hadu da ita, kyakkyawar yarinya ce da lokaci ɗaya tayi mugun matowa a kanshi. Shi ma ba zai yi karya ba zai iya cewa duk cikin yan matanshi bai samu wadda suka yi clicking a lokaci guda ba kamar ita.
Ɗaga wayar yayi ganin kiran yana daf da tsinkewa, nan ya jingina da motar yana sauraren daddadar muryarta dake cike da kissa mai hade da shagwaba wadda take amfani dashi don ta kara rikitashi kwarai da gaske.Daga gani babu tambaya, tun daga nesa idan ka hangoshi a kallon farko za a fahimci ya gama narkewa a cikin kogin soyayya, har wani lumshe idanu yake yi don tsananin daɗin tausasan kalaman da yake saurare daga bakinta.
Hankalinshi gaba ɗaya yana kanta, Idanunshi sun rufe ruf! ya manta da kowa da komai, kamar a ɗakinshi yake wayar. Babu abinda yake ji da saurare face ita kadai.
Allah kadai yasan lokacin da suka kwashe a haka suna waya kafin suyi sallama da kyar kamar ba zasu rabu ba, bayan yayi mata alkawarin zai tura mata manyan kudade wadanda zata je tayi sayayya dasu, saboda ya ce yana so da dare su fita shi da ita suje wajen cin abinci.
Bayan sun gama wayar ne ya maida ita cikin aljihu wata hadaddiyar bakar Benz g6 tana ta sheki da daukar idanu ta gangaro a hankali ta yi fakin gefen inda yake tsaye kusa da motarsa.
Da ganin motar sabuwa ce dal, abubuwan zamani irin wadannan basu dame shi ba sam, amma haka nan yabi motar da kallo har aka gama daidaita fakin ɗin motar.
Maimakon ya nufi ciki kamar yadda yayi niyya sai ya tsaya yaga wanene mamallakin wannan danƙareriyar motar?
Tsawon wasu daƙiƙu aka ɗauka ba'a buɗe motar ba, can kuma sai aka buɗe ƙofar ɓangaren direba, wata santaleliyar ƙafa fara sol mai ɗauke da dogayen yatsu kyawawa cikin wani haɗaɗɗen takalmi shi ya fara bayyana.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
Kinh dịA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari