BABI NA GOMA SHA HUƊU

132 16 0
                                    

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*TSAKANINA DA MUTUWA...!*

©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals

*BABI NA GOMA SHA HUD'U*

Gefen kujerar da yake zaune ta ja ta zauna itama. Duk da cewa karfe bakwai ne na safe kadai, amma ta sha kwalliyarta kamar wata wadda zata je wajen wani biki. Gown ce a jikinta wadda ta bi jikinta ta lafe, ta kuma yi nasarar fitar mata da kirarta mai kyau da tsari wadda Allah Ya bata. Satar kallon wayar dake hannunshi tayi, anan ta fahimci chatting ma yake yi akan whatsapp, amma bata hango ko da waye yake yi ba. Koma dai waye yake chatting dashi taji ranta yana mata suya ganin yadda gabadaya hankalinshi ya karkata akan wayar har ma bai san lokacin data zauna a kusa dashi ba.
Plates ta jawo da gayya take hadasu waje daya suna bada sauti, hakan ya ankarar dashi da wanzuwarta a wajen. Da sauri ya kashe wayar ya jefata cikin aljihu yana dan murmushin yake, "ho...honey! Tun yaushe kike anan?!", ya watsa mata tambayar cikin in-ina da alamun rashin gaskiya.
Harara ta dan watsa mishi, "ina fa zaka sani tunda hankalinta kacokam yana kan waya! Wai kai da waye haka kake ta wani zabga fara'a kamar wanda aka yiwa kyauta da gidan aljanna?", itama ta watsa mishi tambayar cikin alamun tuhuma da rashin yarda.

Nan da nan ya fara sharce zufa, dama ance marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake. "Haba dai! Wata irin fara'a kuwa? Ai da manajan wajen aikinmu nake ne, kinsan fa akwai magana a kasa kan cewa za ayi mun karin matsayi, shi yasa kika ga fara'ar tawa ta wuce misali amma ba wani abu bane! Me aka dafa mana ne Mr. Chef?". Kokarin janye hankalinta yake yi amma wannan karon bata jin zata iya biyewa rainin hankalin daya saba yi mata.

Gabadaya ya bi ya canza mata kamar ba Khaleel dinta wanda ta sani ba. Da sai ya kai har wucewar karfe takwas a gida a ranakun aiki, da yamma kuma karfe biyar ya dawo. Amma yanzu wani lokacin karfe bakwai da rabi ma bata yi mishi a gidan, gashi kuma wasu ranakun sai ya kai har bayan magriba ko ma isha'i bai koma gida ba. Idan kuma ta tambayeshi yace mata aikine ya mishi yawa, wasu lokutan har rufe ido yake yi ya hau ta da fadan babu gaira. Abun tun baya damunta har ya dawo dai yana ci mata tuwo a kwarya.

Bata kara ce mishi komi ba ta fara zuba mishi dangin kayan data soya na kari. Maimakon ta sanya cokali su ci tare yadda ta saba, sai kawai ta zuba mishi idanu yana cin abincin tana kara nazartarshi a nutse. Da yana cin abincine bilhakki, kuma har yaci ya gama cikin yabonta da irin yadda ta kware a fannin girki take. Amma yanzu cin abincin yake yi kamar wanda ake tursasawa, ta ma kula gabadaya hankalinshi ba a wajenta yake ba. Ko rabin faranti bai yi ba ya ajiye abincin ya hau hada kan kayanshi zai wuce wajen aiki.
Ya juya yana kallonta, "babyna babu wani abu da zaki bukata ne? Saboda da yamma akwai wani muhimmin meeting da zamu yi da nake tunanin zai kaimu karfe taran dare".

Bata amsa mishi ba sai tashi da tayi cikin karya jiki da firirita, ta sanya hannuwanta biyu ta zagaya dasu wuyanshi, kamshin turaren arabian oud da yake matukar so ya kai mishi karo. Bakinsu take kokarin hadewa cikin sumba, ya wani zabura yayi baya da sauri kamar wanda ake shirin dosanawa wuta a jiki. Kame-kame ya fara yi mata, "ammm... kinga lokaci yana ta wucewa fa! Gashi sauri nake yi yau da wuri nake so in shiga wajen aiki!".

Abin ya bata haushi matuka gaya, har bata san lokacin data daga baki ta ambaci sunanshi da kakkausar murya ba, "Khaleel!".
Ya dakata daga kokarin fita daga falon da yake yi, ya juya yana kallonta da mamaki zane baro-baro akan fuskarshi, abinda bata taba yi ba tunda suke dashi. Ta kama kugu fuskarnan a hade kamar wadda aka aikawa da sakon mutuwa,

"Wai lafiyarka lau kuwa ko kuwa dai akwai abinda yake faruwa ne?".
Yace, "ban gane ba, me kike nufi ne?".
Tace, "kada ka mayar dani wadda bata san me take yi ba mana! Ko kuwa kana tunanin ban kula da canzawar da kayi bane? Ka daina zama a gida sosai, ka daina cin abincina Khaleel, yanzu kuma yar tabawar ma da nake maka ma guduna kake yi? Ko kana tunanin wai ban kula da cewa yanzu ko hada shimfida dani baka cika yi ba?!".

TSAKANINA DA MUTUWA...! Where stories live. Discover now