*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA GOMA SHA BIYU*
Wannan maganar ba karamin tayar da hankalin Malam tayi ba. Kwarai ya shiga cikin damuwa ba kadan ba. Ba tare da ɓata lokaci ba ya fara bincike akan matsalar Ɗan malam da ire-iren matsalar, don ya san ta inda ya kamata ya ɓullowa al'amarin.
Da farko yayi iyaka bakin kokarinshi a cikin sanin da yake da shi don ganin ya kamo bakin zaren amma, hakan ya faskara, duk iya sanin da yake da shi a ɓangaren magungunan musulunci da na gargajiya ya gwada shiru kake ji, tsawon lokaci ba'a dace ba. Duk da matsananciyar addu'ar da suke yi shi da Ɗan Malam amma har lokacin Allah bai kawo musu iyakar wahalar ba.
Sai kuma ya fara binciken magunguna gurin sauran nagartattun Malaman da ya sani da sauran masu bada magunguna, da kuma ɓangaren manyan likitoci. Tsawon lokaci nan ma shiru ba wani ci gaba, abu daya da wasu manyan malamai suka samu nasarar ganowa kuma aka sanar da shi shi ne, mummunan sihiri ne a jikin Dan Malam.
Wanda karyewarshi ba ƙaramin jan aiki bane sai abinda hali yayi ko kuma wani ikon Allah, tunda babu abinda ya gagari mahaliccin sammai da ƙassai. Domin mugun tsafi ne aka yi da bakaken kafuran aljannu gurin aikata shi.
Da jin wannan bayanin hankalin Malam da Ɗan Malam ya ƙara ɗugunzuma fiye da baya, yayi kuka sosai. Wane irin bala'i ne wannan ace bazai iya sauke nauyin buƙatarshi a jikin matarshi ta sunnah ba sai matan banza waɗanda ba halaliyarshi ba? Me yayi a rayuwarshi me ya tare ma wani a rayuwar duniya da za a haɗa shi da bala'i irin wannan?
Kusufa-kusufa na Nigeria da kewayenta sun zaga amma babu wani ci gaba sai godiyar Allah. Amma a wasu lokutan bin matan nashi ya kan ɗan yi sauki, idan kuma ya motsa abin ba a magana.
Bayan Malam ya sake nema mishi auren wata yarinya Mansurah, ita kam ko watanni hudu bata rufa ba ta kara gaba. A takaice dai a cikin shekaru hudu sai da ya auri mata biyar kowacce tana karawa bujenta iska.
Hasina yarinyar da aka fara aura masa ta yi matuƙar kokarin zama da shi a hakan saboda tsananin son da take mishi. Duk tsayin wannan lokacin tana tare dashi. Sai a cikin kwanakin ne bayan matarshi ta karshe ta gama mishi dibar albarka da rashin mutunci, ya fita ya dawo ya tarar gaba dayansu basa nan sun tafi gidajensu.
Sai wasikar Hasina ya tarar a ɗakinshi tana mai bashi hakurin tafiyar da tayi, haƙurinta ya kai ƙarshe. Don Allah ya taimaka ya yanke mata ƙaddararrun igiyoyin aurenshi da suka zarge ta ƙafa da hannu.
Bai ja abin da tsayi ba don kuwa yasan da cuta a cikin zamansu. Tunda har ta iya daga baki tace ya sauwake mata, tura ta kai bango kenan. Ya rubuta mata takarda ya kai mata gidansu da abin arziki raga-raga, suka rabu cikin mutunci da girmama juna.
Ita kuma Safiyya da yake kamar mayya take duk tsiyar da suke kwasa sai ta tafi gida kafin ya aika mata da takarda sai ta dawo, mugun sonshi take yi. Ta kuma faɗa mishi kar ya kuskura ya ce zai sake ta don wallahi ko ya sake ta dole ya zauna da ita. Mugun son shi take yi kamar za ta haɗiye ranta don shi.
*****
Yau kam da fara'a sosai ta dawo gida kamar ba ta a cikin wata damuwa. Tana dakinta tana cire arabian gown din dake jikinta, Ummanta ta shiga dakin da kular abinci a hannunta.
Itama sai ta saki murmushi ganin irin fara'ar dake kwance akan fuskar Khadeejan.
"Ya aka yi ne Khadin Mama? Tun da kika dawo naga bakinki har kunne, ta samu ne? A ƙyanƙyasa min mana ni ma in taya ki farin ciki".Murmushi ta ƙara saki, ta karɓi kular hannun uwar ta ajiye can gefe ɗaya, ta riƙe hannayenta duk biyun. Bakinta har kunne ta fara magana cike da karaɗin murna da matsanancin farin ciki
"Ke dai Ummah ki bari kawai, ai dole in faɗa miki wannan kyakkyawar labarin don ki tayani murna. Wallahi kamar daga sama yau nake jin cewa an min transfer zuwa bangaren yan sakandare, shi ne abin yayi min dadi sosai don na jima ina neman wannan damar ban samu ba sai yanzu!"
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari