BABI NA ASHIRIN DA BIYU

96 14 1
                                    

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*TSAKANINA DA MUTUWA...!*

©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals

*BABI NA ASHIRIN DA BIYU*

*******

   "Me kika aiko Ummanki ta faɗa min? ke ba ki da baki ne? Ke ga ki isasshiya mai cikakken iko da zaman kanta kin fi ƙarfin ki nemi izini a guri na da kanki sai dai ki aiko sa'arki ko?"
Ya watsa mata tambayoyin da muryarshi a cunkushe, fuskarsa na bayyana matsananciyar ɓacin rai, ko kaɗan babu walwala! Kamar bai taɓa sanin yadda ake wata aba wai ita dariya ba.

   'Ya rabbi ya rabbi ka kawo min ɗauki. Daman wanda aka tsana ko cikin ruwa ya faɗa sai a ce ya tada ƙura'
Ta faɗa a zuciyarta, idanunta suna ƙara ciccikowa da hawaye, da ta saci kallon yanayin fuskarsa sai ta ƙara daburcewa.

Ta ƙara sunkwui da kanta ƙasa, ƙirjinta na bugawa fat! fat!!. Zuciyarta cike da addu'o'i iri daban-daban, roƙon Allah take yasa ya barta tayi tafiyarnan! Don wallahi ta ci burin zuwa bikinnan ba kaɗan ba.

'Ta san idan ita ne ta nemi izini kamar ta tono wuƙar yanka kanta ne, don sai yayi mata wanki babban bargo ta fita tas kamar yadda yasha faruwa a mafiyawancin lokuta idan ta tambayi izininsa wajen yin wani abu da ya shafi al'amuran rayuwarta.

Shi yasa da bikin ya matso ta dinga naci tana roƙon Ummanta don Allah ita ta nemo mata izini a gurin Baban. Ta yi amfani da karin maganar nan ta bahaushe da yake faɗin tsakanin mace da miji sai Allah, a lokuta da dama idan Baban yayi yunƙurin zazzageta Umman ce take uwa tayi makarɓiya tana nuna mishi duk yadda yake damuwa da rashin aurennan fa ita Khadeejar ta fi su damuwa.

Idan ya taso ita ma Umman ta taso sai a sami sauƙin faɗan a kanta nan da nan zai shuri takalmansa ya fice a gidan yana ƙanƙanan maganganu. To ashe wannan karon bata nemi Umma ta nema mata izinin a sa'a ba...'

   "Ba da ke nake magana ba?!!"
Ya sake daka mata wani gigitaccen tsawar da yasa a tsorace ta matsa baya, duk ga tsammaninta haɗe da bugu zai kai mata.

   "Kin wani sunkuyar da kai kina mui-mui- mui da baki siffa da kamanni ta tantiran munafukai. Ke Khadeeja bari ma dai yau in faɗa miki wata magana, ki buɗe kunnenki ki ji ni da kyau!

Ki bar ganin ke kaɗai Allah ya bani a matsayin ƴa ta ɓangaren Ummanki, tunda dai kin ƙi jin maganata balle har kiyi abinda nake so tuni na daɗe da ajiye al'amarinki gefe ɗaya a cikin rayuwata. Ita uwar taki ta ci gaba da ɗaure miki kuna goga kafaɗu a tsakar gida.

Kuyi duk abinda kuke so a lokacin da kike so, kije duk inda kika ga dama, na sakar miki wannan damar. Ke baki isa ki saka min hawan jini ba, kinyi kaɗan wallahi.

Wani ɗan lokaci ƙanƙani nake jira ya cika idan baki karyo kin biyo layin da na daɗe ina nuna miki ba wallahi tallahi zan baki mamaki ke da uwarki, zan kore ki ki tattara inaki-inaki ki barmin gida na kije duk inda za ki.

Ki tafi can duniya ki ci gaba da yawon banzan da kike buri, bazan bari ki ci gaba da zubar min da mutunci a unguwa da cikin gari duk inda na shiga ana nuna ni da baki ana ga wacce ƴarsa ta ƙi aure shekaru arba'in tana zaune a gida.

Za ki ɓace min da gani ko sai na sheme ki? in karki in kar banza, sakarya, sha-sha-sha wacce har yau bata san Annabi ya faku ba."

Ai da gudu ta tashi ta fice daga ɗakin har tana tuntuɓe da dakalin ƙofarsa, ta san kaɗanne daga aikinsa ya sheme ta kamar yadda ya faɗa.

Domin yanzu ita kanta ko bai faɗa ba ta daɗe da sanin Baban ya daina sonta ya daina ƙaunarta a matsayinta na ƴar cikinsa. Ba tun yau ya fara faɗin zai kore ta ba, Shi yasa ko kaɗan kalmar zai kore ta bai ƙona mata zuciya fiye da ko wane lokaci ba.

TSAKANINA DA MUTUWA...! Where stories live. Discover now