*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA GOMA SHA SHIDA*
Baki da hanci buɗe ta ci gaba da kallonta, ta ɗora tafin hannunta na hagu ta tallabe haɓarta. Ta karkace kai gefe guda zuciyarta cike fal da mamakin ɗaure fuska da hura hancin da Luban take ta yi.
Hannu tasa ta yafito Alhaji Lukman ya matsa kusa da ita sosai, bakinta ta matsa kusa da kunnenshi ta ce
"Lukman? Kana ganin Luba da gwamammun ƙafafunta wai haushi ta ji don na kori wannan komaɗaɗɗiyar tsohuwar?"
Sai tayi ƙwafa ta ci gaba da cewa
"Ko da yake ƙyale ta. Kar ka ce mata komai, Ni warki ce dai-dai da ƙugun kowa. Yanzunnan zanyi mata wankin babban bargo in tashi hankalin kowa a gidannan..."Zazzaro ido yayi a tsorace yana kallonta, ya san halin Inna kamar yunwar cikinshi. Idan ta fara tsiya rufe ido take yi da wanda ya ji da wanda bai gani ba sai ta haɗa ta sille kowa. Ya ƙara tankwashe ƙafa yana niyyar fara rarrashinta da tausasan kalamai sai ga sallamar ƴaƴanshi sun dawo daga makaranta.
Abdulmalik ne a gaba, kyakkyawan saurayin yaro nutsattse ɗan shekara goma sha bakwai, ƙannensa ƴan biyu Ansar da Malika suna biye da shi a baya.
Ganin Inna da suka yi a zaune akan kushin ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa ƴan biyun suka nufi gurinta da gudu suna mata oyoyo da nufin faɗawa kanta.
Tsawan da uban ya daka musu yasa duk suka dakata suna tura baki
"Wani irin hankali ne wannan? baku ganin bata daɗe da dawowa daga asibiti ba?"
Ya ƙarashe cikin fushi yana zazzare musu idanu.Washe baki tayi ta kamo hannun Malika da Ansar ɗin ta zaunar da su a gefenta
"Kyale su Lukman ƙyale su, ai duk murnar gani na ce tasa haka ko mailaika?""Ni Inna ba fa Mailaika suna na ba. Malika ake cewa."
Yarinyar ta faɗa tana tura baki, zuciyarta cike da jin haushin yadda duk sadda Innan za ta kira sunanta sai ta ɓata mata suna."To rasai, rasa kunya ɓeran tanka, bazan ce Malikar ba Mailaika nayi niyyar cewa..."
"Inna barka da yamma. Ina yini.."
Abdul ya katse cece-kucen ya fara gaishe ta a nutse, fuskarsa yalwace da faffaɗan murmushi. Don sosai ya ji daɗin ganin Innan a gidansu.Da fara'a ta amsa shi, sai kuma aka fara musayar gaishe-gaishe a tsakaninsu cikin wasa da dariya.
Da wannan damar Alhaji Lukman yayi amfani ya tashi tsam daga gurin ya nufi ɓangaren da aka gina aka ƙawata musamman domin Innan. Sai da ya tabbatar da ko ina tsaf ne sannan ya ajiye mata jakar kayanta ya fice daga ɗakin.
A kicin ya samu Hajiya Luba tana ƙoƙarin haɗa abincin dare Lantana tana kama mata, fuska ba walwala yace ta biyo shi ɓangarensa.
Gabanta ne ya faɗi ganin yanayin fuskarsa, ko da ta je tas ya wanke ta yana faɗin idan bata shiga taitayinta ba wallahi zai mugun bata mamaki. Innan ne bata sani ba ko kuwa halinta ne bata sani ba? Kuma tun yaushe ya hana jaye-jayen mutane amma ba ta ji?
Ita dai haƙuri tai ta bashi kamar za ta kwanta ya tattaka gadon bayanta, hankalinta a tashe. Bata taɓa tsammanin ɗaure fuskar da tayi zai ɓata masa rai har haka.
Daƙyar ya sauko bayan ya ce lallai taje ta ba Inna haƙuri. Ko da ta je da yake Innan faɗa ne da ita ba riƙo ita har ta manta da abinda ya faru, cikin ƙanƙanin lokaci suka share komai suka ci gaba da harkokinsu cikin wasa da dariya.
*********
Wani irin mugun damƙa tayi mishi a kafaɗarsa na ɓangaren dama. Sai mutsu-mutsu yake yi, duk yadda ya so ya ƙwace allon kafaɗarsa ya kasa. Tsananin mamaki ne ya kama shi, hannu kamar ba na ƴa mace da aka santa da laushi ba? Da ya gaji da yunƙurin kwatar kanshi kawai sai ya tsaya ya zubawa sarautar Allah ido yana kallonta.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
TerrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari