BABI NA TARA

174 28 0
                                    

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*TSAKANINA DA MUTUWA...!*

©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals

*BABI NA TARA*

Tun da suka shiga cikin ƙungurmin dajin da ita bata dawo cikin hankali, hayyaci, nutsuwarta ba sai da ta kwana biyu ta yini sur tana layi, ba don komai ba kuwa sai sanadiyyar hodar iblis ɗin da suka shaƙa mata lokacin da suke ƙoƙarin tafiya da ita.

Hankalinta ya kai ƙololuwa gurin tashi ne lokacin da ta waiga hagu da dama gabas da yamma taga ba gida gaba ba gida baya, sai bukkoki guda uku a tsakiyar dokar jeji.

Su da aka kamo suna ɗaure a jikin wasu turke a wulaƙance kamar dabbobi, duk garjin ranar da ake ƙwallawa da ruwan sama mai tsananin ƙarfi haka yake ƙarewa a kansu.

Duk ta inda ta waiga sai taga matasa tsaye rirriƙe da manyan bindigu sunyi arresting ɗinsu, kamar masu jira a ce kule su ce cas! Ta ko wane ɓangare babu gurin gudu babu na ɓuya.

A can jikin wata ƙatuwar bishiya mai yalwar ganyayyaki kuma wani ƙasurgumin ƙaton matashi ne zaune akan wata kujerar roba, ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana girgizawa, waya ce kange a kunnensa yana magana yana ɓaɓɓaka wata irin mahaukaciyar dariya mare daɗin sauraro.

Ɓangaren da su Inna suke ɗaɗɗaure ya nuna da yatsarsa manuniya yana ci gaba da magana a wayar
   "E ga su nan! Mutane huɗu ne, maza biyu mata biyu, sunyi daidai da irin waɗanda kuke nema."

Sai kuma yayi shiru yana sauraren can ɓangaren, sannan ya ci gaba da cewa
   "A'a! Gaskiya za ku ƙara farashi akan na da, domin ka san in banda ba su da galihu tuntuni ƴan uwansu sunƙi kawo kuɗin fansa ni kuma na gaji da ajiyarsu kaima ka san bazan sayar maka da su ba. To in haka ne ba gara in aika su garin da ba a dawowa ba.?"

Bai jira cewar can ɓangaren ba ya katse wayar a fusace, a zuciye ya ɗauki ƴar ƙaramar bindigar da ke ajiye a kujerar gefensa ya saito inda su Inna ke ɗaɗɗaure ya sakarma da ɗaya a cikinsu harbi tau a ƙirji!

Luuuu matashin ya tafi zai zube ƙasa ɗaurin da aka yi mishi da igiya ya riƙe shi.

Tsananin tsoro da ɗimaucewa ga ƙarar harbi ga na mutuwar matashin nan a gabanta yasa Inna ta yanka wani ƙaƙƙarfan ihu sannan ta fashe da kuka, kafin kace me sai ga zawo tsuuuu ya kece mata daga inda take zaune.

   "Ke tsohuwa...! ke!! ke!!! Rufe min baki kafin yanzunnan kema in aika ki garin da ba a dawowa...!"
Ƙaƙƙarfar matashin ya daka mata wani ƙaƙƙarfar tsawa yana faɗin haka cike da fushi da hargowa.

Ɗif ta haɗiye kukan da take yi a tsorace tana zazzare idanu kamar ƙwai a ledar biredi, jikinta sai rawa yake yi kamar ana kaɗa mata ganga.

Idanunta akan matashin nan da tun yana ɗan motsi alamun fitar rai har ya daina. Runtse idanu tayi ƙam bakinta na marai-marai kamar tana cin ta-soyu, ita kuwa maimaita Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir raheem take yi a zuciyarta.

Bata ga isowarshi gurinta ba sai yatsun ƙafafunta da aka murje da ƙarfi yasa ta buɗe da baki a tsorace za ta sake yanka ihu sai tayi ido biyu da kan bindiga a saitin goshinta.

   "Kina buɗe ruɓaɓɓen bakinki da niyyar yin ihu ni kuma zan fasa ƙwaƙwalwarki."

Ɗaga kai ta yi da sauri-sauri kamar ƙadangaruwa.

Gaba ya matsa ya fara nuna ma yaranshi wasu daga cikin waɗanda suke ɗaɗɗaure yana musu bayani
   "Waɗannan ku ware su gefe ɗaya, Alhaji Yalli zai zo muyi cinikinsu. Ko a gurin iyayensu ba su da makoma shi yasa har yanzu ba'a waiwayesu ba."

Kusan gaba ɗaya waɗanda suke ɗaɗɗaure suka fara kuka suna salati da sallallami hankulansu a tashe, harba bindigar sama da yayi sau biyu yana rantsuwar duk shegen da ya sake tari sai dai uwarsa ta haifi wani yasa duk suka yi ɗif kamar an ɗauke wuta.

TSAKANINA DA MUTUWA...! Where stories live. Discover now