*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA GOMA SHA UKU*
Bai ce da Hajiya Laura komai ba, sai kallonta yake yana wasu tunane-tunane a zuciyarsa. Yana kallo har ta tattara kuɗaɗen gaba ɗaya, ta ciro ɗankwalin kanta ta zuba a cike ta naɗe ta rungume tsaf kamar ta ɗauki jinjiri! Ta ɗan saci kallonsa sai taga shi ma ita yake kallo, jikinta na rawa ta fice daga falon baƙin ta nufi cikin gidan.
"Hajiya ya tafi ne?"
Aira ta tambaye ta hankalinta yana kan wayarta da take dannawa, sam bata lura da abinda uwar ta rungumo ba."A'a ina zuwa!"
Cikin ɗakinta ta shiga kai tsaye tayi ma kuɗin ɓuya mai nisa, sannan ta dawo cikin falon ta nemi guri ta zauna kusa da Aira tana sauke ajiyar zuciya, fuskarta na bayyana matsananciyar farin ciki ta fara magana."Ki je ki shirya a gurguje, yana jiranki a sitting room. Da alamun wannan karon buƙatarmu za ta biya Aira. Da maganar aurenki yazo da zafi-zafi abinda muka daɗe muna jira har mun fara fidda tsammani. Ki shirya kije yana jiranki."
Galala ta bi uwar da kallo baki buɗe, sai kuma ta yamutsa fuska, da mamaki ta sake tambayarta
"Aure dai Hajiya?""E ƙwarai kuwa! ke ma kina mamaki ko? Ni kaina haka nake ta mamaki wallahi, ban gasgata maganarsa ba sai da ya waro wasu maƙudan kuɗaɗe ya bani a matsayin kuɗin gaisuwa da na na gani ina so..."
"Taɓɗijan! Ai kuwa tun wuri ki mayar masa da kuɗinsa, don wallahi bazan aure shi ba..."
"Kul! kul!! kul!!! Karki kuskura ki ƙarasa Sameera."
Ta kwaɓe ta cikin tsawa da ɗaga murya sannan ta kira ainahin sunanta abinda ta daɗe bata yi ba. Lokaci ɗaya ta murtuke fuska kitif ta koma Boss ɗinnan da ƴaƴanta basu isa su kawo mata cikas ko misƙala zarratin akan abinda ta gindaya musu ba."Kin sanni kin san hali na, ba na ɗaukan wargi ko ƙanƙani. Balle akan kuɗi babu abinda bazan iya yi ba, kuɗi su ne abinda ba su da na biyu a rayuwata. Don haka ko za ki mutu sai kin auri Alhaji Safiyanu, ai aure ma kamar anyi an gama don a gaggauce yake son komai. Babu wata shegiyar ƴa da ta isa ta musawa abinda nake so. Tun tale-tale akan wannan turbar nake tafiya, akanta na ɗora duk ƴan'uwanki daga kanki bazan canza alƙibla ba. Wuce maza ki shirya ki same shi a falon baƙi kafin in saɓa miki."
Ta ƙarasa maganar da tsawa muryarta cike da ɓacin rai da hargowa.Tsam ta miƙe ta nufi cikin ɗakinta don ta shirya, bakinta a gaba tana gungunin magana ƙasa-ƙasa.
"Taɓ! ai wallahi sai dai kiyi, bazan taɓa auren wanda ba na so ba. Ɗan malam nake so kuma shi zan aura. Bari inje in samu tsohon banzan can shi ma in ci mishi mutunci. Idan ke baki ji maganata ba shi idan ya ce ya fasa ai dole ki haƙura ki bani wanda nake so."A gaggauce ta gama shiryawa cikin wata doguwar riga da ya kamata tsam ya fidda duk wani shape na jikinta. Ta yi kwalliya sama-sama wanda ya ƙara tona asirin kyawun fuskarta dukda ita ɗin mai kyau ce.
Uwar ce ta kafa ta tsare tayi tsaye a kanta sai da ta gama shiryawa ba tare da ɓata dogon lokaci ba, hatta rigar da za ta saka uwar ce ta zaɓa mata. Ta bulbula mata turarukan humra masu sanyin ƙamshi kaloli daban-daban, ta raka ta har ƙofar falon baƙin ta tabbatar ta shiga sannan ta juya cikin gidan tana mamakin Aira a zuciyarta.
'Can baya ita ce mai yawan nacin Alhaji Safiyanu ya turo ayi maganar aure, har gurin malaman da suke mata aiki ta mimmiƙa sunanshi amma shiru kake ji ya ƙi motsawa.
Sai dai yazo susha soyayyarsu, tsawon lokaci babu maganar aure. Idan bata manta ba an ɗauki kusan shekaru uku kenan Aira tana tare da Alhaji Safiyanu, don ma wani lokacin yana daɗewa bai waiwaye ta ba.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari